Skip to main content

Gabatarwa

K​imanin ƙarfe sha biyu na rana, akan wani tsauni dake kan doron ƙasa ta biyu, waɗansu mutane guda uku, ke ta tafka gudu a tsakankanin wasu bishiyun giginya acikin wani daji mai yawan duhuwa.

Biyu daga cikinsu sanye suke da jan sulke, sannan kuma haye suke kan ingarman dawakai fasalin danda, ɗaya kuma wanda shi ne na tsakiyarsu yana sanye da sulke ruwan ƙasa akan ingarma fasalin dandan-akwal.

Kana ganinsu kasan akwai gajiya da raunika a tattare dasu, amma kuma a lokaci guda haɗe da wannan gajiya akwai dagiya da kafiya irin ta mutanen farko, wadda tasa ko kaɗan wannan gajiyawa bata sa sun rage azabar gudun da suke ba.

Can bayan wasu ƴan daƙiƙu, na ɓangaren daman ya buɗe bakinsa wanda kana gani zaka tabbatarwa kanka cewa ruwa ya daɗe bai shiga ciki ba, saboda tsananin bushewar da yayi, ya ce, "shugaba, suna gab da cimmana, mai ya kamata muyi?"

Yana faɗar wannan magana yana juya kansa bayansu, kamar wanda yake karanta wani abu a bayan nasu, duk da kuwa babu abinda ake gani a bayan nasu sai zallar duhu. Wanda idan ka kula sosai zaka ga abin mamaki ne, saboda duk da ranar dake tsakiyar sama, bata iya haskaka wajen. Hasalima kamar ƙara masa duhu take.

Duk da kasancewar dukkanin fuskokin waɗannan sadaukai uku a rufe suke, amma dai-dai wajen idonsu a buɗe yake kana iya ganin idonsu tar-tar, ta cikin wata ƴar tsaga da akai domin gani.

 Mutun biyun dake gefe idanunsu a buɗe suke, sai kuma na tsakiyar tasu, wanda duk da azabar gudun da suke amma idonsa duk biyun a rufe suke!

Acikin idanun na ɓangaren damar akwai wani abun mamaki, wanda ba wani abu bane, illa cewa babu baƙin ido kwata-kwata acikin idon, sannan kuma a dai-dai wajensa an maye gurbinsa da alamun hoton takobi launin baƙi.

Ko kuma zaka iya cewa tunda ita ma takobin launin baƙa ce, baƙin cikin idon nasa ne ya juye izuwa zanen wannan takobi.
To koma dai meye acikin tsakiyar idonsa maimakon baƙin ido, babu komai sai baƙar takobi.

Na tsakiyar tasu wanda shi wannan na ɓangaren dama ya  kira da shugaba, idonsa a rufe yake saboda haka babu damar ganin menene aciki.

Amma na gefen hagun idanunsa a buɗe suke, kuma zaka iya cewa sunfi kama dana mutane, idan aka kwatanta dana ɓangaren daman, duk da kuwa cewa suma idan ka kula zaka ga akwai wani haske da suke fitarwa a duk sanda ya ratsa ta cikin duhu, kamar yadda na mage suke yi da dadaddare.

Wannan jarumi na tsakiya shiru kawai yai baice komai ba, har tsahon kusan daƙiƙa talatin, bayanda daga bisani yayi magana cikin wata murya mai cike da wata Izza irin ta sarakunan farko, "na yanke shawara!

"Wannan Izzar zanyi amfani da ita!
"Ina da buƙatar tsahon lokaci kimanin zuwa sanda rana zata faɗi kafin na gama!

"Yanzu tambayar ita ce.. zaku iya kare kogon can daga Ururu shida, har zuwa wannan lokaci?" Yana mai nuna wani kogon dutse da bashi da nisa daga inda suke, sannan kuma a lokaci guda yana kallon wanda yai masa tambayar.
"Zamuyi iya ƙoƙarin mu shugaba!" Ita ce kawai amsar da suka bashi a tare.

Ba jimawa suka ƙaraso wajen wannan kogo daya nuna, inda ba tare da ɓata lokaci ya shige ciki kai tsaye, su kuma waɗannan mutun biyu dake gefensa suka tsaya abakin wannan kogo.

Kallo ɗaya tak zakaiwa yanayin tsaiwar da sukai, kasan cewa babu wanda a cikinsu yake da niyyar ɗaga ƙafa daga bakin wannan kogo indai yana da ragowar numfashi.

Ba daɗewa waɗansu mutane su ma su uku, suka bayyana a bakin wannan kogo kamar an cillosu daga sama.
Kana jin irin iskar dake tashi daga jikinsu kasan akwai sarauta acikinta, sarauta da Izza irin na sarakunan farko.

Kallon farko zakai tunanin malamai ne sanye da baƙaƙen kaya, amma idan ka lura sosai zaka gane cewa kayan jikin nasu bawai baƙaƙe bane, amma akwai wani abu a jikin fuskarsu wanda ke zuƙe haske dukkanin abinda ya kusance shi, kamar yadda suna bayyana a wajen, gaba ɗaya ko'ina ya fara yin duhu, duk da kuwa rana tana tsaka.

Idan ka matsa kusa dasu zaka fuskanci cewa lallai da gaske akwai wannan abu a jikin fuskarsu wanda ke zuƙe haske kowanne iri ne, ba wani abu bane illa idanunsu, wanda suka kasance baƙi-ƙirin, babu alamar fari ko kaɗan acikinsu.
Ajikin fuskar kowannen su akwai irin waɗannan baƙaƙen idanu guda biyu, wanda idan ka haɗa zaka ga akwai guda shida kenan a tare dasu.

Kallon ɗaya kacal zakai koda kuwa daga nesa ne, ka gane cewa waɗannan idanu na musamman ne; gaba ɗaya farin cikin idon ya juye ya koma baƙi wuluk, tayadda idan ka kalli idon ba abinda zaka gani sai baƙi. Irin baƙinnan mai sawa kaji kamar za'a zuƙe ka ciki idan ka kalla, saboda tsananin duhu.

Duk da cewa dukkanin cikin idon baƙi ne, amma idan ka lura sosai zaka fuskanci cewa tsakiyar idon yafi ko'ina baƙi, hasalima banbancin baƙin dake tsakanin biyun kamar banbancin sama da ƙasa ne.
Saboda wannan tsakiyar idanu har baƙar kala suke amayarwa idan ka lura sosai.

Saboda haka nema abu ne mai sauƙi mutun yai kuskuren cewa cewa tsakiyar idon ne kaɗai baƙi.
Wannan irin idon shi akewa laƙabi da URÚRÚ!!

Babu ko magana ɗaya data faru a tsakanin ɓangare biyun banda kallon gaba kawai sama da daƙiƙa sittin.
Kafin daga bisani na tsakiyar ma'abota wannan baƙaƙen idanu da akewa laƙabi da Ururun ya dubi na ɓarin damansa, wanda kana ganinsa zaka ga alamun ƙarancin shekaru a jikinsa, ya ce, "Uznu, ka lura sosai, zaka koyi abubuwa da dama, kasan bazan dauwama a gefenka ba ko!"

Sannan ya juyar da kansa ya dubi waɗannan mutun biyu dake tsaye a bakin wannan kogo zare da takubban jan ƙarfe, cikin izgili ya ce, "shekara goma kenan kuna gudu, sai yau kuka ga dama kuka tsaya!! Hah!

"Bana buƙatar naji dalilin tsayawarku, dan bashi da wani muhimmanci, abu ɗaya dana sani shi ne da tsayawarku anan, da kasancewar cewa lallai yau zaku ziyarci lahira, kaf abubuwa ne wanda haka sarki Dumaƙisu Kuyurussa'ayi ya ambata zasu faru!"

Wannan ita ce magana ta ƙarshe data faru tsakanin waɗannan ɓangaro ri guda biyu, kafin daga bisani azababben faɗa ya kaure a tsakaninsu. wannan faɗa ya shafe dogon lokaci yana afkuwa, kuma babun wanda yasan adadin tsahon wannan lokaci sai waɗanda ke wajen!
Wannan abu ya faru ne a shekara ta 1469 bayan Amri!

Saboda tsananin azabar wannan faɗa daya afku a wannan shekara har bayan shekara ɗari biyar baya, babu wata halitta data ƙara iya rayuwa a wannan dajin, wanda ada ke daga cikin dazuka mafiya girma a dukkan ƙasa ta biyu.

Babu ko kiyashi daya rage bayan wannan faɗa wanda zai iya bada labarin yadda faɗan ya kasance, sai mutun ɗaya, wannan ma'aboci Ururu da aka kira da suna Uznu.

Kuma shima bayanda aka gama faɗan, ya isa doron ƙasa ta farko domin ya kaiwa sarki Dumaƙisu Kuyurussa'ayi bayanin abinda ya faru, baice komai ba, banda cewa sun isar da aikin da aka basu.

Sai dai kuma daga baya, bayan ya dawo hayyacinsa ya bayyanawa sarki Dul'Ururu, shugaba bisa doron ƙasa ta biyu cewa wannan mutun daya shiga cikin kogon nan kafin a fara fafatawar ya bar wata takobi bayan mutuwarsa, wadda keda ban mamaki!

Ya bayyana cewa a ɓangarenta guda akwai rubutu wanda bai iya karantawa.
Kuma koda sarki Dul'Ururu ya tambayi ko mai yasa bai ɗakkota ba, sai ya bayyana masa cewa yayi ƙoƙarin hakan, amma yana kusantar ta, ta juye izuwa wani ɗan ƙaramin littafi wanda baifi girman hannu ba, kuma ta ɓace ɓat.

Ya neme ta tsahon kwanaki, badan komai ba sai dan kallo ɗaya yai mata yaji ta shiga ransa, amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya tafi!

Ya dai bayyana cewa tunda wannan al'amari ya faru, Uznu ya shiga halwa ta neman Izza, tsahon shekaru masu yawa har saida aka manta dashi!

Shekara bayan shekara, sama da shekaru ɗari biyar da sha ɗaya sun wuce, da dama daga cikin mutane da suka rayu a wancan zamani sun daɗe da mutuwa, kai hatta jikokinsu basa nan.

Wannan mutun da ake kira da Uznu'Ururu ya ƙara bayyana, inda ya jagoranci yaƙi zuwa doron ƙasa ta bakwai akan wasu masu adawa da salon mulki na shugaba Dumaƙisu Kuyurussa'ayi, shugaba bisa doron ƙasa ta farko.

Yaƙin da ya ɗauki watanni ana fafata shi, kafin daga bisani nasara ta faɗa ɓangaren Ururu!

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...