Skip to main content

Babi na Sha ɗaya : Dordor

Dordor!! Wannan suna ne wanda jama'ar wannan zamani suka laƙabawa waɗansu halittu, waɗanda ba mutane bane, hasalima a zahiri fatalwowi ne. Sai dai kuma amma su na da irin sura ta mutane sak, in banda waɗansu banbance-banbance da suka raba.

Girmansu ya haura na mafi yawancin mutane misali, tsaka-tsakinsu sune waɗanda girmansu yakai kimanin girman ƙarti biyu na mutane a haɗe.

Kalar fatar jikinsu zata iya ɗaukar kowacce irin kala, kama daga kan baƙi, fari, ja, kore, shuɗi kai dama dukkan sauran launuka.

To ɗaya dai daga cikin irin waɗannan fatalwowi ne, ya nufo Armad ta baya, da tsananin muguwar niyya taya halaka shi. Kuma shi ne wanda Hasanu ya gano yana tahowa tunda farko, kuma shi ne dai wanda Zahra/Nostalgiya ta gani, lamarinda yasa take ta ƙoƙarin janyo Armad waje.

A dai-dai lokacin da Armad ya waiwaya, sukai ido biyu da wannan fatalwa, mai suna Dordor, kamanninta suka shiga kwakwalwarsa. Nan take yasan cewa lallai a kowanne lokaci, mutuwa zata iyai masa sallama idan baiyi wani abu ba.

Wannan Dordor dai daya Shuɗi ne gabaki ɗayansa; tun daga kan dogon gashin kansa wanda ke taɓo har tafin ƙafarsa, harya zuwa tafin ƙafar tasa komai shuɗi ne.

Idan ka cire launin fatar jikinsu, wani banbanci da waɗannan fatalwowi suke dashi, idan ka haɗasu da mutane shi ne, adadin kawunan kowanne ɗaya a cikinsu.

Duk da kasancewar yawanci waɗanda jama'a suke arba dasu, adadin kayikansu bai wuce ɗaya zuwa biyu ba, to amma akan gamu da masu kai uku a lokuta ƙalilan. Misali wannan shuɗin dake biye da Armad kansa ɗaya ne kurum, wanda hakan yasa yayi kama da ɗan-adam sosai, idan banda mahaukacin dogon gashin kansa da kuma shuɗiyar fatar jikinsa!

Amma a zahiri da yawa daga cikin mutane sun san akan iya samun Dordor masu kai ɗai-ɗai har guda bakwai.

Abin mamakin shi ne, watanni shidan ƙarshen kowacce shekara duk wata ƙasa dama duk wasu matafiya dake da burin yin tafiya akan Bangwayen ruwa guda biyu sai sun yi rijista, a wajen ma'abota Ururu, domin tafiya akan wannan ruwan.

Hakan zaisa abasu shedar kariya daga waɗannan halittu masu laƙabin Dordor, wanda ta hakane kaɗai ake iya yin tafiya akan wannan bangwayen ruwa cikin kwanciyar hankali.

A cikin littafin ''Halittun farko a duniya,'' da B. Zinariya ya wallafa, ya rawaito cewa, A farkon lokaci, al'ummar fulani mazauna yamma, sun yanke shawarar yin hijira zuwa gabas.

Amma bisa ƙaddara akan hanyarsu ta tafiya, sun gamu da halittu masu firgici da dama, sai dai kuma mafi muni aciki, su ne waɗansu halittu da suka kira da suna Dódo.

Karawar waɗannan fulani da waɗannan halittu shi ne ya zamo mafi munin abu da fulanin suka taɓa fuskanta.

Domin abisa alƙaluma kafin su isa inda zasu je, sai da sama da biyu cikin uku, na jama'arsu suka salwanta.

Bayan shekaru masu yawa, suka isa gabas. Amma sai suka ɗauki wata sabuwar al'ada ta rashin magana tsahon kimanin wata ɗaya, domin jimanta waɗanda suka rasa rayuwarsu a yayin wannan hijira.

Bayan shekaru masu tsaho, zafin rashin da suka fuskanta yaɗan fara raguwa, ma'abota kwarewa ta fannin magana da salo wajen bada hikaya acikinsu, sai suka fara rubuta labarai domin fito da jarumtar mutanen nasu da suka fafata da waɗannan halittu, masu suna Dódo.

A saboda haka kafin jimawa sunan Dódo ya bazu a sassa da yawa na duniya. Harma ya zamanto abin bawa yara firgici da tsoro;

''Wato idan yaro yayi abu sai kaji ance ya bari ko kuma a haɗa shi da Dodo."
***
To wannan dai shi ne abinda yazo acikin wancan littafi.

To da yake a gaba kaɗan acikin littafin anyi bayani akan su waɗannan halittu masu suna 'Dódo' da kuma siffofin su, waɗanda idan ka duba za kaga sunyi kama sosai dana waɗannan halittu da a wannan zamani, jama'a sukewa laƙabi da Dordor, to da dama daga cikin mutane su na tunani cewa akwai yiwuwar waɗannan halittun iri ɗaya ne ko kuma ƴan'uwan juna ne da waɗancan da suka fafata da fulanin a wancan zamani.

***
Armad ya kalli idanun wannan budurwa ya kuma kalli irin yanayin yadda take ta ƙoƙarin kuɓutar dashi.

Tuni har makarin fuskarta ya faɗi, amma duk da hasken dake tashi daga fuskarta ta bai hana ganin kwalla dake haɗowa acikin idanun nata ba.

Armad bayan yayi ajiyar zuciya ya ɗaga ido ya ƙara kallonta, suka haɗa ido.

Baice komai ba, ita ma kuma bata bashi amsa da komai ba, amma bayan wannan kallo guda ɗaya tak da sukai wa juna, Armad ya yanke shawarar cewa lallai bai kamata ya bari wannan budurwa ta halaka a wajen nan ba.

Koba komai yana da buƙata ya tambaye ta yaji baki da baki, mai yasa yake jin cewa kamar ya taɓa ganinta, harma yana ganin waɗansu mu'amaloli da suka gudana a tsakaninsu. Waɗanda suke matuƙar kama da zahiri, amma kuma shi yasan a iya tunaninsa basu faru ba.

To a dai-dai wannan lokaci tuni wannan shuɗin Dordor ya ɗaga hannunsa ya kuma kawowa Armad wafta.

Wanda kuma a lokacin ne su Hasanu suka ƙaraso dab dasu.

Idanunsu acike da rashin sanin yadda zasuyi, suka tsaya cirko-cirko akan Zahra.

Kasancewar su na da cikakkiyar masaniyar cewa taɓa wanda Dordor ya taɓa tamkar taɓa Dordor ɗinne da kanka, wanda kuma hakan tamkar cakawa kanka wuƙa ne. Domin duk wanda ya taɓa Dordor, a take gaba ɗayan ruwan jikinsa ke ƙonewa!

Saboda yana daga cikin sanannen ilmi a wannan zamani cewa ba'a taɓa Dordor da fata, saboda haka basu da damar taɓa wannan budurwa, a dai-dai wannan lokaci da take riƙe da Armad shi kuma Armad ɗin bai rage saura ɗan taƙi ba, tsakaninsa da shuɗin hannun wannan Dordor ɗin nan ba.

To a wannan lokaci da kusan kowa acikinsu ya ɗebe haso a sannan ne abinda ko a mafarki basu taɓa kawowa zai faru ba ya faru ba.

Wannan Dordor yana gab da taɓa Armad, a yayinda Armad ya fizge hannunsa daga hannun Zahra, ya guma zare takobinsa, sannan yana lilo akan iska ya juya ya kai sara ga hannun wannan Dordor da sauran ƙiris ya kama wuyansa.

Koda ganin abinda ya faru, sai jikin Zahra ya fara karkarwa, ba tare da ta sani ba ma ta yunƙura da ƙarfin tsiya tare da miƙewa da niyyar riƙo Armad.

Amma a dai-dai lokacin da take gab da faɗawa cikin ramin ne, su Hasanu da Kiru suka isa gareta, a inda Kiru yakai hannu ya riƙo ta, sannan kuma kafin kace meye wannan ya dawo da ita baya kuma a lokaci ɗaya duk su ukun suka yi tsalle sukai baya da sauri.

Cikin daƙiƙa ɗaya tuni sun bada kimanin taku biyar tsakaninsu da Armad.

To a sannan ne suka tsaya, sannan baki a buɗe cike da mamaki suka ƙurawa Armad ido.

A baya basu samu lokacin mamaki ba, amma yanzu da suka ga sun ceto ƙanwar tasu wadda keta ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da su biyun sukai mata, sai suka ɗan nutsu. A inda hatta Kiru da dakakkiyar zuciyarsa, saida ya sarawa Armad da irin jarumtar daya nuna wajan fuskantar wannan Dordor, gaba da gaba.

Idanun Kiru suka ƙara kaɗawa da marmarin yaƙi babu abinda yake faɗa a zuciyarsa sai, ''kash! badan mutuwarsa tazo da wuri ba, ai daya taimaka wajan fiƙe takobi ta, domin ko badan komai ba ina son fafatawa da marasa tsoro irinsa.''

Shi kuwa Hasanu wanda ke riƙe da hannun hagun Zahra ƙam-ƙam magana yake aciki, ''hanzari ya kamata nayi na koma gida, na tabbatar da abinda nake kokwanto!''

Da yake tunda aka fara wannan fafatawar baice uffan ba, sai kawai nazari da kuma bibiyar abubuwa da yakeyi.

Daga gefe kuma acikin abinda bai wuce daƙiƙa biyar ba, har Armad da wannan shuɗin Dordor, sunyi musayar sama da sara ashirin, a fafatawarsu a saman wannan rami.

Duk da tsananin kyau kamar na ƴaƴan sarakunan manyan fararen aljanun farko, da kuma girman kai da ƙasaita da mulki irin ma'aboa maɗaukakiyar Izza, da Zahra take dashi, amma hakan baisa ta buɗe baki ba, idanunta cike da kwalla ta dubi Armad,kamar wani wadda take so ta bawa wanda zai mutu cikin ƴan daƙiƙu wasiya, amma ina takasa cewa komai.

Nan take Kiru ya riƙe baki, yana mamaki; shi dai yasan irin buwaya da ƙanwarsa take dashi a fannin kyau da sarautaa dukkan faɗin ƙasa bakwai. Hasalima kusan ta kori sama da ƴaƴan manyan sarakuna goma, masu neman aurenta. Kuma tunda yake bai taɓa ganin ta nuna wani yanayi irin wannan ga wani ɗa namiji ba, komai kyansa, komai buwayarsa, kuma komai mulkinsa.

Ballantana Armad, wanda yasan cewa koda ma wani ɗan babban sarkin ne, to yasan cewa bazai taɓa kama ƙafar manyan ƴaƴan sarakunan da suke neman auren ƙanwar tasa ba.

Hasalima da dama zasu iya bayarda duk abinda suka mallaka, domin kawai rana ɗaya, sau ɗaya tak, ta riƙe hannunsu. Amma basu samu ba.

Yana gama wannan tunanin, kawai abu ɗaya ya yanke acikin zuciyarsa, cewa LALLAI WANI ABU YA TAƁA AFKUWA TSAKANINSU; BANDA GAYA MANA DA TAYI TA CETO SHI DAGA CIKIN WANNAN GARI, LALLAI AKWAI WANI ABU, WANDA BAMU SANI BA!

Can bayan wani lokaci kalmar kawai data fita daga bakinta ita ce, ''Ar...mad...''

A dai-dai wannan lokaci ne wannan Dordor ya buɗe bakinsa ya fesowa su Hasanu wani ruwa baƙi-ƙirin a dunƙule kamar ƙawanya daga bakinsa.

Wanda kan kace meye wannan, tuni ya bayyana a gaban su Zahra, inda ya fara buɗewa yana ƙara girma tamkar wanda yake so ya haɗiye su gaba ɗaya. Kan kace meye wannan tuni wannan baƙin ruwa ya canja daga kimanin kamu ɗaya zuwa kimanin  ɗaya.

Bayanin yadda abubuwan suka faru zai ɗauki lokaci, amma yanayin yadda komai ya faru a zahiri baifi ƙiftawar ido da bismillah ba.

Lallai duk wani mutum a wannan zamani yasan me wannan baƙin ruwa yake ƙunshe dashi, lallai yasan cewa ko mai za'ai kuma ko a bakin ransa to bai kamata ya bari wannan ruwa ya taɓa shi ba.

Armad duk da bai taɓa arba da Dordor ba, amma yasan haka daga ilmin da yayi a rayuwarsa, su kuma waɗannan mutane uku dake wajen dukkansu ƴaƴan sarakuna ne, saboda haka sun san sarai mai hakan yake nufi.

Armad bai san mai yasa ba, amma kawai yaji a ransa cewa bai kamata ya bari wannan budurwa ta halaka a wajen. Sannan kuma ya san cewa idan ya bari ta halakan, to lallai baya jin zai samu wanda zai iya bashi amsar abubuwan da yake so ya tambayeta.

Kan kowa ya farga tuni Armad ya ɗaga takobinsa sama, ya numfasa a wani yanayi mai cike da yanke shawara, sannan ya saukarda saran takobin tasa da ƙarfin gaske gami da ambatar, ''Wilbafosiyan-Siwod-Dans!!''

Rufe bakinsa keda wuya wani haske ya fara feshi daga jikin takobin tasa, nan take komai ya tsaya cak; kama daga kan wannan baƙin ruwa dake gab da haɗiye su Zahran da kuma wannan Dordor dake biye da Armad zuwa ga dukkan ƙasar data rududduge.

Wannan haske nan take cikin ƙiftawar ido yai matuƙar ƙaruwa ta yadda ya kashewa kowa ido, ko tafin hannu ba'a iya gani.

Bayan kimanin daƙiƙa biyu hasken ya fara raguwa, kafin daga bisani ya ɗauke gaba ɗaya.

Su Hasanu na tsaye inda suke, idonsu a gaba na ƙoƙarin karanta maiya faru.

Abinda kuwa sukai arba dashi shi ne, babu alamun wannan baƙin ruwa, babu alamun shuɗin Dordor ɗin, sannan kuma bisa mamaki dukkan ƙasar da suke kai wadda da duk ta rududduge kuma su na gab da ruftawa ta dawo ta haɗe tamkar wani abu bai taɓa faruwa da ita ba.

Dukkanin wannan abin mamakai ne da ban al'ajabi a garesu musamman ganin ƙasar da da ta riga ta rududduge ta kuma zaizaye, amma yanzu kuma ta dawo ta haɗe tamkar babu abinda ya taɓa samunta.

To amma wani abu guda ɗaya daya fi ɗugunzuma hankalinsu sama da komai shi ne rashin ganin Armad ko sama ko ƙasa!

Bayan ganin wannan fasaha da Armad yai amfani da ita, Hasanu ya ƙara samun nutsuwa kan abinda yake kokwanto, lamarinda ya ƙara sawa yaji akwai buƙatar ya koma da Armad garinsu maimakon kashe shi, duk da kuwa Armad ɗin yaji sirrin su, SIRRIN DAZAI IYA RIKITA DUNIYA BAKI ƊAYA.

Shi kuwa Kiru, marmarin yaƙi ne kawai ya ci gaba da kaɗawa a idonsa, yana jin cewa lallai Armad ya isa su kara dashi.

Ita kuwa wannan budurwa kana ganinta zaka san tana cikin jimami da ɓacin rai, saboda badan hannun Hasanu dake riƙe da ita ba, da tuni ta faɗi ƙas!!
***
Wai me Hasanu yake kokwanto akan Armad, harda yasa ya fara ƙoƙarin fasa kashe shi?

Anya kuwa babu wani abu daya faru tsakanin Armad da Nostalgiya, wanda bamu sani ba, wanda kuma shima bai sani ba, wanda kuma ga dukkan alamu ita kaɗai ta sani?

Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...