Yaƙin daya afku a wannan shekara tsakanin Uznu'Ururu da kuma jama'un doron ƙasa ta bakwai, ya haɗa harda sauran ƙasashe da dama.
Wasu suna goyon bayan Ururu, wasu kuma al'ummar ƙasa ta bakwai.
A ɗaya daga cikin ƙauyukan dake ƙasa ta uku shashin arewa, wadda akewa laƙabi da Kanyú, da dama daga jama'ar wannan gari sun ziyarci wannan yaƙi daya wakana, kuma akai sa'a da dama sun dawo gida bayan kammala yaƙin.
To amma duk da haka duk fuskar wanda ka kalla acikin wannan gari zaka babu annuri kwata-kwata a tattare da ita, duk da cewa da dama daga cikin su iyalunsu sun dawo!
Ba wani abu bane ba kuwa ya janwo hakan ba, ill abinda ya faru da wannan jarumai bayan dawowar su daga wannan yaƙi.
Wannan kuwa ba wani abu bane illa cewa, kwanaki kaɗan waɗannan mutane da su ka dawo suka fara mutuwa, ba tare da wani cikakken dalili ba, hasalima da dama babu wani ciwo na zahiri a jikinsu.
Kafin kace meye wannan sama rabin waɗanda suka dawo sun isa lahira!
Hakan yasa tun da aka fara sallar jana'iza da binne gawarwaki bayan isha ba'a dainaba sai zuwa kusan ketowar alfijir.
Ana cikin wannan hali wani Mai shela acikin wannan gari, haye kan wani doki samfurin Kilí ya fara zagayawa kwararo-kwararo yana cewa,''saƙo daga sarki!
"Sarki ya aiko ni, ya ce a gaya muku, ku daina taɓa jikin waɗanda suka dawo daga yaƙi da fatarku, domin akwai matuƙar yiwuwar cewa duk abinda yake kashesu za'a iya ɗaukansa ta hanyar taɓi.''
A wannan gari, acikin waɗannan fuskoki masu cike da juyayi da baƙin cikin rabuwa da masoyansu akwai wani yaro wankan tarwaɗa dogo mai cike da kamala, yana ɗaure da jan ƙyalle a saman kansa wanda ya zagayo ta gaban goshinsa.
Duk da fuskarsa na nuna yarinta amma kallo ɗaya zakai masa, ka gano cewa a tattare dashi akwai kwarjini.
Ɗauke yake da wata mace, wadda yake riƙe da ita cikin yanayi na tsananin kula da kaffa kaffa.
Tafe yake yana sassarfa cikin keta mutane, idanunsa a sama yana hange-hange tamkar wanda ke neman wani abu daya rasa wanda kuma in bai samu ba rayuwar sa zata iya tagayyara.
Duba ɗaya tak inkai masa ka san cewa yana cikin damuwa, daga gani wannan mara lafiya dake bayansa wata ce ta kusa dashi.
Tuni duhu ya fara yi sanda ya isa wata ƴar runfa dake kudu maso gabashin ƙauyen, inda ya tadda wani ɗan tsoho aciki.
Ya ɗan duƙa kaɗan yai sallama, sannan a wata murya mai cike da kwarjini ya fara bayani da sauri-sauri, ''Barka da yamma baba mai magani.
"Baba ta na kawo, ina fatan ko zaka iya taimakon ta.
"Kaga ko rauni ɗaya babu a jikinta, tana numfashi, kuma bugawar zuciyarta dai-dai yake amma bisa mamaki taƙi farkawa ta buɗe ido.
"Na zagaye dukkanin wajen wani mai magani a wannan ƙauye amma babu wanda ya iya yi mata wani abu.
"Yanzu kaine na ƙarshe daka rage, dan ALLAH ka taimake ni, ita kaɗai ce ta rage min.''
Nan da nan wannan ɗan tsoho mai yawan farin gashi a fuska da kai, ya ɗauko ƴar fitila aci bal bal ya kunna saboda duhun da gari fari yi, sannan ya ɗan duƙa ya fito waje ta cikin ƴar ƙofar shagon inda ya nufi wannan saurayi.
Yana zuwa baiyi wata-wata ba, ya dubi matar wadda ke bayan saurayin ya miƙa hannu ya buɗe idanunta.
Nan take a fili jikinsa ya mutu, saboda da kyar ya iya ɗago kai ya dubi saurayin cikin yanayin tausayi gami da cewa, ''ɗan saurayi ya sunanka."
Saurayin ya amsa cikin ladabi, ''Suna na Armad Djinn."
Tsohon yaci gaba da cewa, ''Armad haƙiƙa yau na duba marasa lafiya da dama, kuma mafi yawa duk ragowar wannan mummunan yaƙi ne.
"To amma kusan da yawan waɗanda na gani haka suke.
"Ba ciwo ba rauni, ba buguwa, amma basu san inda hankalinsu yake ba!"
Yana cikin magana Ya ɗanyi shiru kamar yana tunani, kafin daga bisani ya isa ga wannan mata ya duƙa, ya ƙara buɗe idonta, sannan kuma bakin ta.
Ya ɗakko wata ƴar fitila ya haska kunnenta. Sannan yai wani dogon numfashi gami da duban Armad, ya ce, ''Armad kake ko?" Wannan saurayi ya kyaɗa kai.
Tsohon yaci gaba da cewa, "Gaskiya kayi haƙuri Armad, babu abinda zan iya, irin wannan cuta a littafi kaɗai na taɓa ganinta.
"Abinda kawai nasani shi ne tana da alaƙa da Ururu.
"Kuma dai a iya sani na, mutun ɗaya na sani da zai iya yin wani abu akai a duk faɗin doron wannan ƙasa ta uku!"
Yana faɗar haka ya nemi waje ya zauna kusa da Armad, sannan yaci gaba da cewa, "to amma wannan mutum dana sani bani da cikakkiyar masaniya ko zai iya ko bazai iya ba, sannan ko zai iya sai yaga dama, kuma baya taɓa taimako a banza.
"Sannan kuma tunkararsa abu ne mai matuƙar hatsari, tunda shi mutun ne wanda ba'asanshi akan taimakon mutane."
Tun kafin wannan tsoho ya gama rufe baki, Armad ya zabura cikin zafin nama ya miƙe gami da cewa, ''ko ina ne kuma ko wanene, ka gaya min zan tunkare shi indai akwai yiwuwar mahaifiyata ta iya samun sauƙi ta hanyarsa!"
Tsohon yai shiru yana kallon Armad fuska cike da jimami.
Kafin daga bisani ya girgiza kai gami da cewa, "sunansa sarkin duba Abul Babara!
"Kuma ina kyautata zaton kasan inda zaka sameshi?"
Da jin haka Armad ya miƙe zumbur gami da yin godiya ga wannan tsoho. Kan kace meye wannan tuni Armad yayi sallama da wannan mutun ya kuma doshi inda sarkin duba yake.
Har ya kusa ƙulewa yajiyo muryar wannan tsohon yana masa magana, "ka kula, ba komai ya gayama zaka yarda!!"
Armad bai iya bashi amsa ba saboda sauri da yake, sai kawai ɗago masa hannu da yayi.
Wannan saurayi daya kira kansa da suna Armad Djinn, yaro ne ɗan kimanin shekaru sha bakwai, ƙafa huɗu a tsaye.
Wani abu guda shi ne, wannan yaro yana da kyawun fuska sosai, ta yadda a ganinka dashi na farko, zaka iya kuskuren cewa wannan yaro ba mutun bane, ɗaya ne kurum daga cikin manyan ƴaƴan aljanu!
Duk da rigar jikinsa nada ɗan faɗi amma murɗaɗɗɗen ginin jikinsa saida ya bayyana duk da haka.
Yana sanye da kayan da yafi so wato, farar riga ƴar shara zuwa ƙugu mara faɗi sosai. sai kuma baƙin wando wanda bashi da faɗi zuwa idan sahu.
Sannan kuma kamar kullum yana tare da, wani jan ƙyalle da yake ɗaure kai dashi.
Zuwa wajen Abul babara dan neman magani abu ne wanda aka daɗe matuƙa da hanashi daga fadar sarkin Hán-na-ɗaya, wanda shike mulkin ɗaya daga cikin mafiya girman ɓangarori biyu a doron ƙasa ta uku.
Kusan kowa yasan Abul'Babara a wannan ɓangaren na ƙasashen ƙasa, musamman saboda irin halayensa, da kuma yadda sarki Hán wanda akafi sani da Hán-na-ɗaya yasa aka koreshi daga cikin gari.
Saboda hakan ba abin mamaki bane Armad yasan wajen da aka kora wannan ɗan duba.
Kai tsaye ya nufi wajen. Babu abinda yake sai sassarfa cikin kula kada yayi abinda zai cutarda mahaifiyar tasa.
Tuni dare yayi tsakiya Armad yana tafiya, amma har wannan lokaci Armad yana tafe bai tsaya ba.
Iska tana kaɗawa daɗan ƙarfi, sannan kuma gari ya fara yin shiru. Amman Armad babu ko alamun tsoro a tattare dashi kawai burinsa ya ƙara nutsawa zuwa ga bakin gaɓa wajen da yake sa ran zai tadda AbulBabara.
Kan kace meye wannan, Armad na tafe har yayi awannin yana abu ɗaya, kuma bai haɗu da wani mahaluƙi ba, saboda dama ko idan ka cire makokin dake faruwa acikin garin, wannan wajen ba wajen ziyartar mutane bane.
Can wajen tsakiyar dare, Armad ya fara hangen bangon Arewa, nan take yasan cewa lallai ya kusa bakin gaɓa.
Koda ya kusa sai yaɗan fara rage tafiya yana dudduba muhallinsa, dama da hauni ko zaiga alamun wannan ɗan duba, amma ina babu wani alamu, sai kawai yaci gaba da tafiya.
Bayan wani lokaci saiya fara hangen wata ƴar bukka daga ɗan nesa, nan take kuwa ya durfafeta babu ko jira.
Yana isa yaga abin mamaki, inda yayi arba da cewa wannan bukka ba'a sama take ba ba kuma a ƙasa take ba.
Wato dai wannan bukka akan iska take.
Armad ya kasance mara tsoro, domin babu ɗar ko kuma faɗuwar gaba a tattare dashi, duk da hatsarin dake tattare da wannan wajen, gashi kuma babu kowa sai shi kaɗai, sannan kuma ga bukka a kan iska.
Abinda kawai zaka iya gani a idonsa shi ne tsananin buƙatar mahaifiyar sa ta samu lafiya.
Koma wacce hanyace komai wahalarta bai dameshi ba.
Da ganin wannan bukka akan iska, maimakon yaji tsoro sai kawai ya fara jin farin ciki a ransa, na cewa yasan akwai yiwuwar samun AbulBabara a wajen, saboda nan take ya fara kwala masa kira, ''AbulBabara...AbulBabara... kana ina, kana ji na!"
Haka yaci gaba da kwala kira har saida ya fara ɗebe haso daga samun wani a wannan wajen, saboda haka har ya fara lissafawa acikin zuciyar sa wacce hanya zaibi ya faɗa cikin wannan bukka ya ganewa idonsa maiye aciki.
Sai kuma ya tuna da mahaifyar tasa dake bayansa saboda haka bazai iya tsalle, ya kuma san bazai iya barinta ba a wannan waje ita kaɗai, saboda haka nan take ya ajiye wannan shawara.
Ya na cikin wannan tunani sai kawai yaji wata kakkausar murya a kunnensa na hagu, ''Ɗan samari, ka tashe ni daga barci. Da fatan abinda ke tafe dakai na ƙaruwa ne?''
Cikin zafin nama da mamaki Armad ya juya ɓangaren da yaji maganar. Saiko yai Arba da wani ɗan gajeren mutum mai dogon gemu.
A wannan lokaci Armad bai san lokacin da yai baya ba da saurin tsiya, kafin daga bisani ya dawo hayyacinsa, ya kuma fara nazartar lamarinda ke faruwa.
Armad bai taɓa ganin AbulBabara ba, fuska da fuska, dalilin kuwa shi ne mahaifiyarsa ta hana.
Saboda haka cikin zafin nama ya manta da cewa wannan mutum kawai bayyana yayi babu ko masaniyar daga ina, yana dubansa abinda kawai ya faɗo masa a rai ita ce tambaya ɗaya, ''Baba, dan ALLAH ko... ko kaga wani mutum a wajejen nan da ake kira da AbulBabara?''
Mutumin najin abinda Armad ya furta wani ɗan ƙaramin murmushi yazo gefen bakinsa ya tsaya, amma baice komai ba, sai kawai ƙurawa Armad ido da yayi kamar wanda yake kallon wani mutun daya daɗe bai gani ba, kafin daga bisani ya mayarda kallonsa kan matar dake bayan Armad a sume.
Tsahon lokaci yana kallonta har sai da Armad ya fara jin ba daɗi, kafin daga bisani yai kyaran murya gami da cewa,
''hmmm, wato har yanzu akan samu jaruman yara marasa tsoro a wannan zamani!
"Kwana nawa kenan?" Idan da Armad ya lura sosai, zai fuskanci cewa akwai yanayi na tausayi daya gilma ta idon wannan ɗan duba mai suna AbulBabara a lokacin da yai masa wannan tambaya.
Amma abinda kawai ke gaban Armad shi ne ya za'ai mahaifiyarsa ta samu lafiya, saboda haka cikin sauri ya bayyana masa dukkan labarin yadda yake ta bilayin nema mata magani amma babu nasara.
Bayan ya gama jawabinsa kaf AbulBabara yai ajiyar zuciya gami da cewa, ''toh, ƴan samari, zan iya taimakon ka amma fa idan ka ƴarda da sharuɗa na!''
Armad najin haka ya bada amsa cikin sauri, ''ko meye indai zata sami lafiya zanyi.
"Faɗi sharaɗin ka naji.'' Yana magana yana hangowa acikin ransa cewa babu wani abu, ko menene wanda za'a tamabaya, da zaiƙi yi koda kuwa zai iya halaka a garin yinsa, indai mahaifiyar tasa zata samu sauƙi.
Saboda haka baiyi wata wata ba ya bada wancan amsa.
AbulBabara ya ƙara kawo irin wannnan murmushi na ɗazu gefen bakinsa gami da tambaya, "Kayi alƙawari?"
Armad ya kyaɗa kai, alamun eh.
"To shikenan, amma fa ka sani ba'a saɓamin alƙawari!
"Indai aka ƙulla alƙawari dani to shike nan." Armad ya ƙara kyaɗa kai cikin sauri, lamarinda yasa murmushin AbulBabara ya canja a lokaci guda, inda yaci gaba da bayani ba tare da kallon Armad ba, ''Sharuɗa na guda biyu ne;
"Na farko ina so ka gayamin cikakken sunanka na gaskiya."
Yana gama faɗar haka ya tafa hannunsa biyu, inda wata kujera mai faɗi ta bayyana a wajen, ya kuma umarci Armad daya kwantar da mahifiyar tasa akai.
Dukkanin abubuwan nan basa girgiza Armad ko kaɗan, duk da kuwa bawai ruwan dare bane a wannan zamani ba, to amma da yake idan akwai abu ɗaya da Armad ya banbanta dashi daga sauran yara shi ne karatu.
Mahaifiyarsa wadda ita kaɗai ta rage masa, ta matsa masa matuƙa ta fanni karatu, tun baya so har ya zamo ya haƙura babu yadda zaiyi.
Daga cikin irin littafan daya karanta, da dama sun nuna cewa irin waɗannan abubuwa su na faruwa a zahiri, kawai al'amari ne na Izza kawai.
Saboda haka, baiyi wata-wata ya kwantar da babar tasa akan kujerar.
Sai dai kuma duk da a fuskarsa babu mamaki ko tsoro, amma kuma daga sanda AbulBabara yai masa wannan tambaya, gaba ɗaya yanayin sa ya canja.
Duk da kuwa cewa ga mafi yawan mutane, wannan tambaya zata zama tambaya mafi sauƙin amsawa a garesu amma banda Armad.
Armad bai taɓa tunanin AbulBabara zai kawo irin wannan abu a matsayin sharaɗinsa ba, saboda haka ya sameshi ba'a cikin shiri ba.
Armad yana da wani kaka mai Narba'ata, wadda tunda ya cika shekara goma yake zuwa gurinsa dan koyar dabarun yaƙi da Izza, badan komai ba saboda mahaifiyarsa duk da kuwa ta kasance daga cikin manyan jaruman doron ƙasa ta uku, amma taƙi koya masa komai, bisa dalilin cewa saiya gama littattafan data sa masa.
Amma duk da haka wannan kaka nasa ya karɓi ragamar koya masa dabarun yaƙi da Izza, amma abisa dalilin cewa lallai bazai taɓa faɗawa wani sunansa cikakke na gaskiya ba.
To da shikenan matsalar data ke gaban Armad a wannan lokaci, to da da sauƙi, amma ina, hatta a ranar da mahaifiyarsa zata fita wannan yaƙin, wasiyya ɗaya data bar masa shi ne, kada ya ringa gayawa mutanen da bai yadda dasu ba cikakken sunan sa.
Hasalima kanta tafi sai da su biyun suka yanke shawara akan cewa daga wannan lokaci zai ringa amfani da Armad Djinn, maimakon cikakken sunan nasa wato Armad Wilbafos!
To duk tunanin waɗannan abubuwa sune suka sa Armad yai kasaƙe yana ta tunani mai ya kamata yayi.
Shi kansa yasan AbulBabara ba abin yarda bane, Kuma duk da cewar bai san dalilin da yasa babar tasa da kakan basa son ya faɗi sunan nasa ba, amman yana ji a ransa cewa, idan zai gayawa kowa a duniya to bai kamata ya gayawa AbulBabara ba.
To amma kuma duk da haka ya ƙara tambayar kansa shin wanne zaɓi yake dashi.
Yana cikin kai komo da zuciyarsa ne, ya ji muryar AbulBabara a kunnensa ''Ɗan saurayi ina jiran amsarka, domin sharaɗi na na gaba yana da alaƙa da amsar da zaka bayar."
Armad bai ce komai ba, illa kawai ƙurawa mahaifiyarsa ido yayi, wadda kallo ɗaya zakai mata kasan tana rai a hannun ALLAH, sannan kuma ya tuno da wasiyyar data bar masa akan faɗar sunan nasa, da kuma matakin da kakansa ya sa masa kafin ya fara horar dashi, nan take ya kara rikicewa ya kuma rasa mai yafi dacewa yayi a wannan hali daya tsinci kansa.
To amma yana cikin wannan yanayi ne wata dabara ta faɗo masa, wadda ba wani abu bane illa cewa a iya tunaninsa babu tayadda za'ai Abul-Babara yasan sunan nasa na gaskiya, saboda mai zai hana ya jefi tsuntsu biyu da tsakuwa ɗaya!!
Saboda haka nan take ya ɗago kai ya dubi AbulBabara inda ya buɗe baki ya ce, "Suna na Armad Dji....."
Kan ya ƙarasa rufe baki, AbulBabara ya ɗaga masa hannu gami da ƙura masa kaifafan idanunsa, sannan ya tambayi Armad cikin ɓacin rai, "Armad Djinn ko Armad Wilbafos?"

Comments
Post a Comment