MAGAJIN WILBAFOS na A M IBRAHIM
Armad na tsaye yana cikin yanayin tunanin maiya kamata yayi har tsahon kimanin daƙiƙu biyu zuwa uku.
Kafin daga bisani ya ƙara jin irin wannan ƙaraji da yaji a baya, lamarinda yasa ba shiri ya waiwaya ɓangaren da ihun ya taso.
Inda idanuwansa sukai arba da wani ƙatoton miciji kore, wanda a tsaye kaɗai yakai tsayin Armad wato taku huɗu, a kwance kuwa yakai kamu sittin da ɗoriya.
Idanun micijin suma koraye ne kaf, kuma a buɗe suke tar-tar, domin tun daga nesa Armad ya hangesu suna bada sheƙin kore.
Sai dai kuma wani babban abin mamaki shi ne kana ganin wannan miciji zaka fuskanci cewa ba'a cikin hayyacinsa yake ba, domin gumi kawai yake sannan yana cikin halin gudu mai tsanani tamkar wanda yaga mutuwa ido da ido.
Armad na tsaye baima gama karantar abinda ke faruwa ya ƙara hango wata koriyar ƙura ta turnuƙe a can bayan wannan miciji, kafin kuma daga bisani ya fuskanci cewa ashe wata tawagar korayen namun dawa ce, irinsu su zaki da damisa da kuma manya-manyan kuraye, dukkaninsu koraye, sai dai kuma bisa mamaki dukkaninsu suma gudun suke kamar ransu zai fita.
Yana cikin haka sai kawai yaji wannan wannan shaho dake manne a jikin takobinsa ya fara karkarwa kamar wanda ke cikin farfaɗiya.
Ba shiri Armad ya juyo da niyyar ganin meke faruwa, inda yai arba da wannan shaho acikin wani yanayi na firgici kamar irin wanda yaga wancan miciji na ciki.
Ba shiri Armad yaga wannan shaho ya fizge bakinsa daga jikin takobin, inda cikin tsananin sauri da zafin nama ya fara kaɗa manyan fuka-fukansa, tare da kuma yin sama da juyawa ya doshi gabas.
Nan take Armad ya tabbatarwa da kansa cewa lallai akwai wani abin tsoratarwa da yake saka waɗannan manyan halittu wannan gudu. Saboda haka nan take shima Armad, a irin girman rashin tsoronsa, ya yanke shawarar maiya kamata yai.
Wanda ba komai bane illa ya tsaya yaga abinda yasa suke gudun kafin shima yasan maiya kamata yayi.
Ko cikakkun daƙiƙu bakwai ba'ai ba, wannan halittu dake ta gudun fanfalaƙi suka zo suka wuce inda Armad yake tsaye, ko kallonsa babu wanda yai acikin su, lamarinda ya ƙara bashi mamaki sosai. Domin a sannan ne ya tabbatar lallai ko menene yasa waɗannan namun dawa gudu, ba ƙaramin abin firgici da tashin hankali bane, kuma koma menene ba abu bane da Armad ya kamata yai gangancin tara ba, saboda nan take Armad ya fara tunanin yanke sabuwar shawarar shima ya kamata ya ranta a na kare, in yaso daga baya yaga mene ne!
Har Armad ya juya zai bi bayan waɗannan halittu, kawai sai yaji ƙarar gudun ruwa, lamarinda yasa ala dole ya juyo da niyyar ganin mai ya kawo ruwa wajen.
Tun kafin ya ƙarasa juyawa idanunsa suka fara karkarwa, fuskarsa cike da mamaki, gashin jikinsa ya mimmiƙe, sannan kuma a lokaci guda gumi ya fara keto masa.
Duk ba wani abu bane ya janyo haka ba illa abinda idanun Armad suka gane masa da kuma abinda zuciyarsa take ɗarsa masa.
Wannan abu ba wani abu bane illa wata ƙatotuwar igiyar ruwa wadda girmanta yafi gaban misali, sannan kuma launinta baƙi ne, baƙi ƙirin. Kuma wannan shi ne karon fari da Armad yaga wani abu ba kore ba, tun bayan shigowarsa wannan koriyar duniya.
Armad ne tsaye cak, kamar an riƙe masa agara, ya kasa ko motsi. Babu abinda yake mamaki sai launin wannan ruwa.
Kasancewar tunda yake bai taɓa gani ruwa mai launin baƙi, baƙi-ƙirin irin wannan ba!
Sannan kuma wani abin mamaki ruwan ya tokare sararin samaniya, ta inda baka iya gano ƙarshensa duk yadda ka ɗaga kai.
Nan take Armad ya juya cikin tsananin sauri da niyyar da fara gudun-tsira da rai, inda ya ɗaga ƙafarsa ta dama gami da yin tsalle da niyyar fara gudu.
To amma rashin sani yafi dare duhu, juyawarsa keda wuya sai kawai bisa mamaki yaji wani abu mai santsi yana ƙoƙarin haɗiye shi, abu na gaba sai kawai yaga ganinsa ya fara yin dishi-dishi, kafin daga bisani ya fara jinsa akan iska wani mugun jiri yana ɗaukansa, inda ba zato ba tsammani sai kawai tsintar kansa yayi a sume.
Bayan adadin wani lokaci da Armad bai iya tantancewa ba, sai kawai farkawa yayi ya kuma tsinci kansa acikin wani ɗaki.
Ya na buɗe ido jikinsa ya fara bashi cewa lallai akwai wani kuskure daya aikata, duk da kuwa cewa bashi cikakkiyar masaniyar menene, amma yana da yaƙinin cewa lallai yayi kuskure a wani waje!
To babban abinda Armad bai sani ba shi ne, duk wani abu da zakai a wannan duniya yana da sakamako, kama daga kan motsi, numfashi, magana da dai sauransu. Kuma shi ne babban amfanin wannan takarda mai ƙunshe da bayanai da ɗalasimai da wancan mutun mai suna HanDiyúza ya bashi.
Daga inda da Armad yake tsaye acikin wannan koriyar duniya zuwa cikin wannan ɗaki tafiya ce ta sama da shekara goma akan ingarman doki, wadda gabaki ɗaya Armad yayi ta ba tare da ya sani ba.
Sai dai babban abin tambayar shi ne, a ina ya bayyana, kuma ina ne cikin wannan ɗaki.
Ɗaki ne mara girma sosai, kuma samansa a buɗe yake hanhai, sannan yana da bangwaye guda huɗu; gabas da yamma, kudu da arewa.
Babban abin mamakin shi ne, kowanne bango launinsa daban ne; bangon arewa shuɗi ne na kudu kuma kore ne sai kuma na gabas da yamma waɗanda farare ne.
Babu ƙofa ko taga acikin wannan ɗaki.
A tsakiyar ɗakin akwai wata ƴar ƙaramar shirwa ta zinare.
Wannan shirwa ta kasance an gina ta akan wani gadan aba'i wanda sai mutum yabi takansa sannan zai iya kaiwa gareta.
Bayan tsahon lokaci Armad na tsaye yana mamakin bayyanarsa a wannan waje, sai kawai ya yanke shawara ya gwada zuwa wajen wannan shirwa ya duba ko zai tadda wani abu.
Yana isa matattakalar gadon aba'in nan ya tsaya, ya fara dube-dube yana tunanin maiya kamata yayi, amma bisa mamaki kan ya yanke wata shawara yaga bakin wannan shirwa ya fara buɗewa da kansa ba tare ya taɓa komai ba.
Kan kace meye wannan ya buɗe hanhai.
Wanda sai a dai-dai lokacin ne Armad ya kula da hasken da takardar dake aljihunsa take yi. Inda nan take ya zira hannu ya fito da ita.
Nan take ya fara karantawa, tunda daman karatu da rubutu a wajensa ba matsala ba ne, musamman yanayin yadda mahaifiyarsa ta matsa masa tun yana yaro akan karance-karancen abubuwa da dama, wanda har a wannan lokaci Armad bai san amfanin da dama daga cikinsu ba, ko kaɗan.
Ba komai ake bayani acikin wannan takarda ba sai umarni da ƙaidojin yadda za'a fita daga cikin wannan duniya, wanda ganin hakan ne yasa Armad ya fara fuskantar abinda ya faru dashi a baya acikin wancan koriyar duniya daya bayyana. Sai dai kuma Armad bashi da lokacin tsayawa tunani a lokacin.
Nan take cikin sauri ya karanta wasu ɗalasimai daga cikin takardar sannan ya tofa acikin bakin shirwar nan data buɗe. Sannan ba tare da ɓata lokaci ba ya dawo tsakiyar wannan ɗaki, wato kusan daidai inda ya fara bayana a karan fari kenan.
Daga nan ya dubi kudu, inda kai tsaye yayi taku biyar, idonsa a buɗe, kafin daga bisani ya rufe ido ya ƙara wasu taku biyar ɗin.
Sannan ya tsaya cak yana duban wannan bango, kamar wanda ke tsammanin wani abu ya afku.
Yana tsaye a haka ba jimawa sai wannan bango ya fara ƙara kamar ana buɗe ƙofa, kuma kafin a jima, gaba ɗayan bangon ya fara girigiza, inda daga bisani ya karkace ɓari ɗaya ya bada hanya kamar an buɗe ƙofa.
Yana ganin haka, ya ɗanyi tunani kaɗan, kafin daga bisani ya faɗa cikin ƙofar.
Shigarsa keda wuya wani haske ya kashe masa ido tsahon daƙiƙu, inda bayan ya washe ya tsinci kansa a wani fili na daban.
Babu alamun rayuwa a wajen ko ɗaya, ko'ina ka kalla babu abinda yake tashi sai yanayin kaɗaici.
Daga can nesa ɓangaren gabas akwai wasu manya-manyan tsaunuka guda biyu, wanda baya iya hango ƙarshensu daga inda yake.
A tsakiyarsu kuma abin mamaki wani ƙasaitaccen gari ne, amma babban abin mamakin shi ne tun daga inda yake yana iya hangen yana ta rufe garin ruf, tayadda daga yawan yanar kaɗai zaka iya ƙiyasta cewa anyi shekara sama da dubu babu wanda ya shiga wannan gari.
Bisa mamaki sai Armad yaji tsananin son ya shiga cikin wannan garin duk da bai san mai yasa ba, kuma yana da cikakkiyar masaniyar cewa kafin yai wani abu akwai abinda ya kamata ya karanta acikin wannan takarda. Amma kuma duk da haka yana ji tamkar rayuwarsa ta ta'allaƙa da shiga cikin wannan gari.
Saboda haka bai san lokacin da ya ɗaga ƙafa da niyyar isa gun waɗannan tsaunika ba, da niyyar ya ɗan leƙa ciki kawai yaga meye aciki.
Haka kuwa akai, cikin rashin tsoro, Armad ya nufi ƙofar garin, inda yana zuwa yasa hannunsa ya fara cire ƙoƙarin cire yanar data lulluɓe ƙofar.
Haka kuwa akai, ba jimawa ya gama cire ta, lamarinda yasa ƙofar garin ta bayyana a sarari yadda yake iya ganinta.
Sai dai kuma wani abu daya bawa Armad mamaki shi ne, ba kamar yadda yayi tunani ba da fari, ƙofar garin a buɗe take maimakon a rufe. Domin yana ɗan tura ta kaɗan ta tafi ta fara biɗe kanta hanhai.
Lamarinda saida yasa Armad ya ɗan jada baya kaɗan, kafin daga bisani ya yanke shawara ya kuma shiga cikin wannan gari.
Shigarsa keda wuya, takunsa na farko ya tsaya cak a inda yake,abu na gaba kuwa daya gani saida yasa nan take duk da ɗimbin rashin tsoro na Armad saida jikinsa ya fara karkarwa. Kuma kan kace meye wannan tuni ya fara ƙoƙarin jada baya cikin sauri da niyyar ficewa daga cikin garin kasancewar tuni ya daɗe da yin nadamar saka ƙafa aciki, da kuma tabbatar da cewa yayi kuskure!
Sai dai kuma amma ina a dai-dai wannan lokaci ne yaji ƙasar wajen da yake tsaye ta haɗiye shi zuwa idan sahu.
Ala dole haka ya tsaya cak a inda yake, bashi da ko niyyar juyawa baya, ya kuma ƙurawa abinda ke gabansa ido, abisa dole.
Ba komai Armad yake gani ba illa wasu mutane manya-manya mutane samfurin adawa. Kowannensu cikin kayan yaƙi irin na al'ummar farko, sannan kuma a jere suke a layi; kowanne layi yakai mutun casa'in zuwa ɗari, sannan kuma akwai layika kusan guda goma a jere.
Babban abin tsoron daya firgita Armad shi ne babu alamun canji na tsufa ko kuma gajiya ko kaɗan a jikin waɗannan mutane, wato dai kamar fitowarsu kenan zasu fita yaƙi, kawai motsi ne da basa yi. Domin idan badan wata kakkaurar yana data rufesu ba to da babu ta yadda Armad zai iya gane cewa wannan mutane sunyi shekaru aru-aru a tsaye basu motsa ba.
Sannan kuma babban abin mamakin shi ne dukkansu idanunsu a buɗe yake, kuma acike da tsananin tsana da baƙin ciki. Sun kasance acikin yanayi na ɗaga kai suna kallon sama kamar wanda suke kallon abokin gaba a kan ƙasar dake samansu.
Irin tsananin faɗuwar gaban da Armad yake fuskanta idan ya kalli waɗannan mutane irin wadda bai taɓa ji bace.
Sai dai kuma duk wannan ba shi ne abinda ya razana Armad ba, kuma yasa yake ƙoƙarin ficewa daga cikin duniyar ba.
Wannan abu kuwa ba wani abu bane illa wata murya da Armad yake ji a kunnensa, wadda tafi kama da muryar manya-manyan sarakunan aljanu ma'abota Izza maɗaukakiya, irin Izzar nan wadda ita kaɗai zata sa kaji dole saika durƙusa akan gwiwowinka ka kai gaisuwa idan kai arba da ita.
Abinda kuwa da wannnan murya take cewa shi ne;
"NI BAYAJIDDA ƊAN ALMA'ATA ƊAN DJINN ƊAN ODUDUWA ƊAN IKENGA DA HÁRÚNU ƊAN MASARAYÚLÚ, INA MAI RANTSUWA DA MAHALICCIN SARKI WILBERIYA, BAZAN TAƁA DENA YAƘAR KUBA, KU MA'ABOTA BAƘAƘEN IDANUWA (URÚRU).
"KODA KUNYI AMFANI DA WANNNAN LA'ANANNIYAR IZZAR DA KUKA GADA ACIKIN WAƊANNAN BAƘAƘEN IDANUWA NAKU, KUN HANANI TAKA DORON ƘASA, TO NI KUMA ZAN YAƘE KU A TSAYE A INDA NAKE.
"IDAN MA KUMA KUKA YI AMFANI DA WANNAN TSINANNIYAR IZZA DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KU KA HANANI MOTSI, TO NI KUMA ZANYI AMFANI DA BAKI NA NA YAƘE KU.
"KAI KODA KUNYI AMFANI DA WANNNAN KORARRIYAR IZZAR DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KUN HANANI MAGANA, TO NI KUMA ZANYI AMFANI DA ZUCIYA TA NACI GABA DA YAƘARKU.
"KAI KODA KUNYI AMFANI DA BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KUN KASHE RUHI NA, BAZAN DAINA YAƘARKU BA, BAYAN NA MUTU!!!" Bayanda muryar tazo nan a zancenta saita ɗanyu shiru, kafin daga ƙarshe ta rufe da jimla guda ɗaya!
"URURUUUUUU, DUK MASIFAR DA AL'UMMA KE CIKI KU NE SANADI!!!"
A dai-dai lokacin da Armad ya gama jin waɗannan maganganu wanda yake jinsu suna tasowa daga can cikin garin nan, tuni ya faɗi ƙasa akan gwiwowinsa, jini ne kawai yake feshi daga idanunsa da bakinsa da hancinsa.
Hankalinsa kuwa tuni ya gushe. Sai dai kuma abu na ƙarshe da Armad yai tunani a ransa kafin ya ƙarasa suma shi ne, "wannan ba wani abu bane illa kawai muryar wannan mutun mai suna BAYAJIDDA, wadda take neman halaka ni, kawai saboda na saurare ta!
"To mai zai faru idan da shi wannan mutumin na ainihin ne ya tsaya a gabana!!" Armad ya ciji yatsa gami da girgiza kai, sannna ya rufe da cewa;
"Lallai bani da ƙarfin Izza, lallai ya kamata na ƙara zage dantse, dan idan ba haka ba babu inda zanje acikin duniyar da mutane irinsu BAYAJIDDA suka rayu!!!"
Waɗannan sune kalaman da Armad yake ta faɗa acikin zuciyarsa a yayinda ya suma a bakin ƙofar wannnan gari mai ban al'ajabi!!!
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved

Hmm gaskiya
ReplyDeleteDuk musifun nan URURU ne suke haddasa su