Skip to main content

Babi na uku : Wasu-wasi (part1)

Idan mai karatu bai mantaba, a Babi na biyu mun tsaya a inda Armad Wilbafos ya zare takobinsa, wadda tsawa da walƙiya suke rawa akan farin ƙarfenta, ya kuma yiwo kan wannan mutun mai matakin Izza ɗari, wanda ya bayyana acikin wannan duniya, ya kuma bayyanawa Armad cewa indai yana so ya wuce, to sai yaci galaba akansa. To daga nan zamu ci gaba!

***
A shekarar dubu ɗaya da ɗari takwas da arba'in da bakwai 1847 bayan Amri, akan doron ƙasa ta uku ɓangaren arewa. Acikin wani fili mai matsakaicin girma, wanda ya kasance a kewaye da busassun itatuwan bishiyar giginya, wasu mutane guda biyu, saurayi da dattijo suna tsaye suna fuskantar juna a wani salo mai kama dana malami da ɗalibi.

Wannan saurayi na sanye da farar ƴar shara mara girma sosai kuma iya ƙugu, sannan yana sanye da baƙin wando zuwa tsakiyar ƙaurinsa, idan ka kalli fuskarsa zaka ga jan ƙyalle a ɗaure a gaban goshinsa, wanda iska take ta kaɗawa.

Duk da cewa akwai ragowar duhun dare a lokacin, amma idan ka lura sosai zaka gano cewa wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos!

Wannan dattijo kuma dake tsaye a gabansa ba wani bane illa kakansa wanda akewa laƙabi da farfesa-Zaikid.

Kallo ɗaya zakai kasan cewa horo ake bawa Armad.

Wannan dattijo ya buɗe baki gami kyaran murya yana mai cewa, "abun alfahari ne ga sauran al'umma su zamanto sunkai matakin bautar da aljanunsu domin su ringa amfani da fasahar su, amma kai a wajenka ba wani kayan gabas bane!

"Saboda kai ɗan zuriyar Wilbafos ne, kuma tsarin rayuwarka ya banbanta da sauran, saboda haka kada ka saki jiki wai dan ka haura wancan mataki!

"Yanzu abu na gaba dake gabanka shi ne kwarewa akan wannan tafarki naka na 'Aradu, tsawa da kuma walƙiya'.

"Kai sani cewa na kira ka wannan waje ne a wannan rana saboda abu ɗaya kawai; domin na fara koyar dakai waɗansu manyan fasahai guda biyu!

"Ɗaya daga ciki zaka iya koya a yanzu, amma amfani da ita sai sanda Izzarka takai mataki na ɗari, ta biyun kuma ita ce wadda zaka iya amfani da ita nan take!"

Yana zuwa nan a zancansa wata iska mai ɗauke da sanyin asuba ta busa, lamarinda yasa babbar rigar dake jikinsa ruwan ƙasa, ta kaɗa sama wanda hakan ya bayyanar da wata doguwar takobi sanye acikin kufe rataye acikin babbar rigar tasa.

Farfesa Zaikid ya ƙara ɗaga kai ya dubi Armad gami da tambayar sa, "mai kake gani a  tunaninka tsakanin iska da tsawa wacce tafi wata gudu?"

Armad najin wannan tambaya ya cika da mamaki, domin shi a iya saninsa babu abinda yakai iska sauri, saboda baya ganin akwai wani abin tambaya ma akai, saboda haka nan take ya bada amsa da cewa, "farfesa, iska tafi sauri ni a gani na."

(Yawanci indai suna wajen horo, Armad yafi so ya kira kakan nasa da farfesa.)

Farfesa Zaikid najin haka yai murmushi, gami da cewa, "amsarka ba dai-dai take ba!

"Indai zance kake na sauri, tsawa tafi. Kuma sannan tafi daɗin sarrafawa ga bil'adama dama aljanu.

"Kai a tunaninka, daƙiƙa nawa tsawa take ɗauka ta iso tun daga sararin samaniya zuwa doron ƙasa! Bai kai ko rabin daƙiƙa ba!"

Armad najin haka ya cika da mamaki, inda daga bisani kawai ya gyaɗa kai, amma duk da haka fuskarsa cike take da kokwanto.

Lamarinda yasa kakan nasa ya dubeshi yai murmushi, gami da cewa, "a yanzu ba lalle kai amanna ba, amma a hankali zaka fuskanci abinda nake nufi.

"Nasan cewa kasan wata fasaha ta saran takobi, wadda masu amfani da aljanun da suke sarrafa iska suke amfani da ita, wadda sukewa laƙabi da 'gayawa jini na wuce'?"

Armad ya ce, "eh nasani farfesa, ita ce wadda take amfani da tsananin sauri wajen saran mutun tayadda har sai ta wuce sannan jini yake fitowa.

Hakan nema yasa baka taɓa ganin jini a jikin takobin kwararrun da suke amfani da aljanu masu sarrafa iska."

Bayani akan ire-iren fasahai abu ne wanda kakan nasa ya daɗe da koya masa, shi yasa Armad baisha wahalar bada wannan amsa ba.

Kakan naji ya kyaɗa kai alamun amincewa da abinda Armad ya faɗa, sannan kuma ya ɗora da cewa, "Armad kasan cewa akwai fasahar saran takobi wadda tasha gaban 'gayawa jini na wuce'?"

Armad najin haka ya gwale ido cikin al'ajabi da mamaki, "farfesa wadda tasha gaban 'gayawa jini na wuce' fa!

"Zaiyiwu kuma?" Mamaki ya bayyana ƙarara a fuskar Armad.

Murmushi kawai farfesa Zaikid yayi, gami da zira hannu cikin rigarsa ya fito da wannan takobin, sannan ba tare da ɓata lokaci ba yaja daga ya fara horar da jikansa Armad akan waɗannan fasahai(fasahohi) guda biyu!

***
Acikin wannan duniya kuwa da Armad ya tsinci kansa, a dai-dai wannan lokaci yana riƙe da takobi tsirara yayi kan wannan mutun da niyyar afka masa, sai dai kuma a dai-dai lokaci ne, shima wannan mutun ya ɗaga tasa takobin sama, wadda tuni ƙarfen takobin wanda na jan ƙarfe ne ya kama da wuta tamkar wanda ake sawa ziga-zigi.

Kallo ɗaya zakai masa kasan cewa babu alamun zai ragawa Armad ko kaɗan acikin wannan fafatawa.

Kan Armad ya ƙaraso takobin dattijon ta gama tashi sama, inda nan take, ta dai-dai ɓangaren da Armad yake nufowa wannan mutun ya ɗaga takobin ya sari iska da ita.

A dai-dai lokacin da saran takobin tasa ya sauka babu wani canji daya faru ko kaɗan, kai kace ma babu abinda ya afku, amma daƙiƙu biyu kacal bayan ya sauke takobin tasa ƙasa gaba ki ɗayan ilahirin iskar dake kewayen wajen ta fara ɗaukar wani azababben zafi irin na musamman.

A kimanin daƙiƙa ta huɗu bayan saran iskar da wannan mutun yai, wannan iska takai ƙololuwar ɗaukan zafi, lamarinda saida yasa Armad Wilbafos cin birki daga afkawa wannan mutun, badan komai ba saboda duk wani taku daya ƙara a wajen kusantar wannan dattijo, ji yake zafin wannan iska yana ƙara ninninkawa tamkar wanda aka sa acikin wuta.

Sai dai kuma da ace a iya nan wannan ibtila'i da yake fuskanta ya tsaya toda da sauƙi, amma ina! A kimanin daƙiƙa ta shida bayan saran iskar, gabaki ɗayan ilahirin iskar dake tsakanin Armad da wannan mutun ta kama da wuta, wadda ta fara ci tamkar wadda ake zubawa fetir.

Kan kace meye wannan tuni wanan wuta ta fara dunƙulewa a waje ɗaya.

Inda a kimanin daƙiƙa ta goma bayan wannan saran iska, wannan wuta ta ƙarasa dunƙulewa zuwa wani ƙatoton dunƙulen wuta murje akan iska, inda ta bada wata sifa mai kama da ƙatoton al'amudin wuta irin wanda mutanen farko suke azaba dashi!

Baki a buɗe cike da mamaki, Armad ya ƙurawa wannan dunƙule ido, amma kafin ya samu damar yin wani abu tuni wannan dunƙule ya fara motsi, inda kan kace meye wannan ya fara mirginawa yana nufoshi da gudun gaske.

A dai-dai kimanin daƙiƙa ta goma sha ɗaya bayan saran wannan iska, wannan wuta ta ƙaraso dai-dai wajen da Armad yake tsaye riƙe da takobinsa tana neman haɗiye shi.

Nan take zuciyar Armad ta fara bugawa tana bayyana masa alamun tsananin firgici, lamarinda yasa yaji a jikinsa cewa lallai indai ya bari wannan wuta ta taɓa shi, tofa lallai kwanansa ya ƙare a ban ƙasa.

A dai-dai lokacin da wannan wuta ta fara taɓa jikin Armad a lokacin ne ya buɗe baki ya kira ɗaya daga cikin ɗalasiman da ya koya a wajen kakansa farfesa Zaikid, wanda ake cewa "ƘABAN'SHISU!"

Yana furta wannan ɗalasimi ya ɓace ɓata daga inda yake, inda ya bayyana a can gefe cikin yanayi na galabaita.

Ita kuma wannan wutar taci gaba da tafiya cikin sauri, inda taje ta haɗu da ɗaya daga cikin manya-manyan bishiyun nan masu kama dana kuka.

Suna haɗuwa nan take wannan bishiya ta juye izuwa toka, kuma duk da cewa girman wutar ita ma ya ragu, amma bai ƙare ba domin saida taci gaba da tafiya ta ƙara samun wata bishiyar irinta, wadda itama ta koma toka.

A haka a haka saida nan take bishiya biyar suka dagargaje izuwa toka, kafin wannan wuta ta ƙare.

Armad wanda yasha dakyar yana gefe yana kallon abinda ke faruwa, ajiyar zuciya kawai yai ya kuma tabbatar da cewa, kiran wannan ɗalasimi da yayi ita ce shawarar data dace a wannan lokaci duk da kuwa hatsarin dake tattare da ɗalasimin.

Armad yana da cikakkiyar masaniyar sau ɗaya kacal zai iya amfani da wannan ɗalasimi mai suna, 'ƙaban'shísu' a shekara.

Shi dai wannan ɗalasimi, kakan nasa ne ya koya masa shi saboda tsaro, domin yayi amfani dashi a irin yanayi mai matuƙar hatsari domin ya kuɓucewa halaka.

Domin shi wannan ɗalasimi idan mutun ya kware ashi, yana da damar ɗauke mutun daga duk inda yake ya kaishi wani wajen daban, ta haka kenan mutun zai iya guduwa daga hatsari komai girmansa, kuma Armad yana da yaƙinin cewa ko daga cikin wannan waje yake son tafiya, wannan ɗalasimi zai iya ɗauke shi.

Sai dai kuma shi Armad ɗin yana da cikakkiyar masaniyar sharaɗin da ake buƙata kafin hakan ya faru, wanda shi ne sai kasan wajen da kake so kaje sosai da sosai acikin ranka, wanda kuma zaka aiyana a yayinda kake ambatar ɗalasimin.

To matsalar ita ce duk inda Armad ya sani a wannan lokaci  doron ƙasa ta uku ne, wanda kuma shi bashi da niyyar komawa can. Hasalima tunda jimawa yayi rantsuwa acikin ransa cewa komai wuya komai daɗi, komai duhu komai tsanani komai wahala saiya nemo wannan mutun da ake cewa Tirifil-fakta, koma wane ne, kuma koma a ina yake!!

Armad na cikin wannan yanayi ne, wannan dattijo ya ƙara ɗaga takobinsa wadda har a lokacin bata daina ci da wuta ba, ya kuma kara sarar iska da ita.

Armad yayi tunanin cewa dama zai iya ƙara turo masa da wannan irin harin na farko, kuma tuni ya ƙudure a ransa abinda zai aiwatar idan hakan ta faru.

Amma kuma bisa mamaki wannan takobi na dukan iska, maimakon dunƙulen wuta irin na baya, kawai sai wata koriyar wuta ta fara fita daga tsinin takobin, lamarinda yasa fuskar Armad ta ƙara canjawa.

Ba'a haura daƙiƙa biyar ba wannan wuta ta gama ficewa gaba ɗaya, a lokacinda wannan mutun wanda har a lakacin idanunsa suna kafe akan Armad. A wani yanayi mai nuna cewa bazai ɗauke su daga kan Armad ɗinba har yaga ya daina numfashi.

A kimanin daƙiƙa ta uku  bayan ficewar wutar, wani zazzafan gumi ya fara ɗisa daga jikin jan kyallen dake ɗaure a gaban goshin Armad. Ba komai bane ya janyo haka ba illa ganin da yayi wutar ta fara lankwashewa tana buɗewa.

Abu kamar wasa akan idonsa, cikin daƙiƙu uku masu zuwa wannan koriyar wuta ta canja siffa zuwa zagaye, inda ta bada fasalin ƙawanya.

Da farko girman ƙawanyar baifi kimanin taku ɗaya ba, amma kan kace meye wannan ta fara buɗewa tana ƙara girma, cikin kowacce daƙiƙa tana ƙara buɗewa da kimanin girman taku uku, sannan kuma Armad ya lura cewa ta fara motsi tana kusanto shi a lokaci guda.

Duk da cewa ba sauri take sosai, amma firgicin da zuciyarsa take gaya masa a lokacin, sun ninninka wanda ya ji ɗazu a lokacinda yai arba da wannan wutar ta farko.

To da ace ma a iya haka abin ya tsaya, toda da sauƙi. Amma ina, a dai-dai wannan lokaci ne ya fuskanci cewa duk inda wannan ƙawanyar ta gifta akwai wani abu mai kama da toka da yake murmushewa ta bayanta.

Saboda haka nan take wasu tunane-tunane akan abinda yake gani suka kwaranyo masa a zuciya.

Kusan zaka iya cewa yasan abinda yake faruwa, amma yaƙi yadda saboda tuni gumi ya gama jiƙa masa riga, badan komai ba sai dan cewa, yasan lallai in abinda yake tunani ne, to al'amari yakai ƙololuwar lalacewa.

Saboda haka nan take ya durƙusa cikin zafin nama, ya ɗebi ƙasa a tafin sa, sannan cikin sauri ya miƙe ya watsata cikin wannan ƙawanyar koriyar wuta da take gabato shi.

Wannan ƙasa ta tafi cikin sauri, tana zuwa ta shige cikin wannan ƙawanya, kuma ta fice ta baya.

Amma bisa mamaki bawai ƙasa ce ta fita ba, a'a toka ce kawai. Nan take Armad ya tabbatarwa da kansa abinda yake tunani.

Wato cewa wannan abu mai kama da toka daya gani tun da farko, ba wani abu bane illa Iskar datai rashin sa'a ta gifta ta cikin wannan ƙawanya, lamarinda yasa nan take ƙonewa izuwa toka, ba tare dama tabi ta matakin kama wa da wuta ba!

Daga cikin abubuwan da Armad yafi maida hankali akai, tun bayan fara koyar dabarun yaƙi da Izza shi ne banbance-banbance akan aljanu da kuma matakai daban-daban da ake iya amfani dasu, misali; duk da cewa zaka iya samun mutun biyu, dukkaninsu aljanunsu na sarrafa abu iri ɗaya, amma kuma ƙarfin waɗannan mutane su banbanta.

Ba kuma komai yake jawo haka ba illa banbancin Izza! Saboda hatta ɗalasimai akwai waɗanda idan Izzar ka bata kai wani mataki ba, to baza ka taɓa iya amfani dasu ba.

Armad ya daɗe da sanin irin wannan koriyar wuta, wadda suke cewa 'Jukísa' da yaren Alderiya.

Ita dai Jukísa zaka iya cewa tana daga cikin manyan hara-haren da masu bautar da aljanun da suke sarrafa wuta suka ji dashi, kuma kusan duk wanda yakai matakin Izza ta ɗari zuwa sama, zaka samu cewa Jukísa ita ce ƙure adakar sa!

Domin abu ne sananne cewa indai ka riga ka bari ka shiga ta cikin wannan ƙawanya, to lallai sai dai ka fice a matsayin toka. Wato ka riga ka ƙone ƙurmus.

Tun daga kan masu Izza ɗari da hamsin har zuwa ƙasa, babu wanda a tarihi ya taɓa shiga cikin wannan ƙawanyar koriyar wuta mai suna Jukísa ba tare ya ƙone izuwa toka ba!

Sannan kuma wani babban sharrinta shi ne yadda take da tsananin sauri wajen faɗaɗa girmanta, domin tuni a wannan lokaci faɗin ƙawanyar ya haura taku ɗari a dama da hauni daga inda Armad yake, saboda haka yasan a yadda yake, gujewa wannan ƙawanya ba abune mai yiwuqa ba.

Duk waɗannan abubuwa su ne abbubuwan da suka sa Armad ya shiga cikin firgicin da yake ciki.

Shi kuwa wannan dattijo kallo ɗaya zakai masa kasan cewa yakai matuƙa wajen yadda da wannan fasaha da yai amfani da ita mai suna Jukísa.

Wanda a ɗaya ɓangaren kuma Armad na tsaye cikin zufa yana wasu-wasin mai ya kamata ya aiwatar!!!

***
Ku biyomu a ci gaban wannan babi domin jin yadda Armad zasu ƙarke da wannan mutun wanda tunda aka fara fafatawar bai bawa Armad ko dama ɗaya ta kai masa hari ba!

Ina buƙatar comment ɗinku musamman akan abinda kuke hasashen shi ne zai faru da Armad a babi na gaba.
A gaskiya comment ɗinku shi ne zai ƙara min ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da fassara muku wannan littafi nawa dana rubuta da turanci! Thanks.

Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...