Skip to main content

Babi na sha hudu : Ikenga O Bayajidda

AA shekarar 1851 After Amri (A.A), a wani gari mai suna Jíha, dake kan doron ƙasa ta bakwai ɓangaren Arewa.

Tsakiyar dare ne, kuma a wannan rana ma wuni akai ana azababben yaƙi tsakani ɓangaren Ururu da kuma ɓangaren ƴan adawa dake da shalkwatarsu a wannan gari.

Babu abinda kake gani sai gawarwakin jama'a duk inda ka duba, dan kusan a wannan rana zaka iya cewa aka kawo ƙarshen wannan babban yaƙi.

Wannan yaƙi dai shi ne wanda mahaifiyar Armad ta samu rauni ashi, kuma harma Armad yaci alwashin sai ya kawo mata mutumin data fita nema ta samu wannan ciwo har gida, komai rintsi komai wuya.

To acikin wannan gari dai, duk inda ka kalla gawarwaki ne a kwance fululu, amma duk da haka idan ka samu ɓangaren da ba mutun a kwance, zaka ga cewa gaba ɗaya ƙasar wajen ta juye izuwa launin ja da baƙi, saboda yawan jinin daya kwarara a wannan rana.

A ƙasa kaɗai al'ummar dake kwance a mace sun haura dubu ɗari, wani ba kai, wani ba ƙafa, wani kayan ciki a waje, wani a caccake da takubba, haka dai kowa ka kalla zaka ga akwai sanadin mutuwarsa.

Babu abinda yake kewayawa a saman wannan gari sai hankakan mutuwa, wanda shi kansa saboda yawan jinin da aka zubar ya fara komawa canjawa daga fari izuwa launin ja.

Acikin waɗannan gawarwaki, idan ka duba zaka gano cewa, mafi yawa daga ciki mata ne da ƙananan yara da tsafaffi, waɗanda kasan tabbas irin waɗanda ake bari a gida a fita yaƙi ne.

Amma duk da haka babu ko ɗaya mai rai acikinsu!

Can bayan wani lokaci wata gawa daga cikin waɗannan mutane, wadda idan ka kalle ta, to zaka iya lissafa mashi sama da biyar a jikinta a cake, amma a haka ta motsa ƴan daƙiƙu kaɗan da suka wuce.

Lamarinda yasa hankakan mutuwar dake wajen tashi sama.

A hankali a hankali, wannan gawa ta miƙe tsaye ta kuma tsaya akan sauran gawarwakin dake ƙasanta.

Kallo ɗaya kacal zakai mata kasan cewa yaro ne wanda bazai haura shekara sha biyu zuwa sha uku ba.

Amma wannan yaro sama da awa goma kenan tun bayan da aka cake masa waɗannan mashi ka a jikinsa, amma yake ta fafatawa a tsakanin mutuwa da rayuwa, yana rantsuwa da mahaliccin sarkin Bayajidda na farko, akan cewa lallai bazai mutu ba.

Tuni hankalinsa baya jikinsa, kuma babu abinda ke zagaye a jikinsa banda jini ko'ina da ina, idanunsa sun canja izuwa jajaye kamar garwashi, kana ganinsa zaka tabbatar da cewa ya kamata ace shekaru da dama da suka wuce ya mutu, amma ina, rantsuwa kawai yake, yana ƙara rantsewa akan lallai bazai mutu ba a wannan rana ba.

Yana haka jini ya ɗebe shi ya ƙara faɗuwa, amma ba jimawa ya tashi ya ci gaba da wannan rantsuwa.

Sai da wannan yaro yai kwana goma acikin wannan hali, sannan ana sha ɗayan, yana gabda mutuwa, wani mutun ya bayyana, fuskarsa a rufe bubu abinda kake gani sai kwayar idanunsa guda biyu. Waɗanda kallo ɗaya kacal zakai musu kasan cewa baƙaƙe ne ƙirin, babu alamar wani fari ko kuma haske acikinsu. Hasalima, yana bayyana duk ilahirin hasken wajen ya fara dusashewa.

Yana bayyana ya isa wajen wannan yaro, inda ya dube shi ya ce, "yaro, ka rantse ka kuma rantsewa akan baza ka mutu ba, kuma ka ƙi mutuwa..

"Shin mai yasa kake son kaci gaba da rayuwa, bayan duk wanda ka taɓa sani a duniya ya mutu, bayan duk wanda zai taimake ka ya mutu?"

A wannan lokaci tuni muryar wannan yaro ta dashe kuma bata fita ko kaɗan, amma a haka ya dubi wannan mutum ya buɗe baki ya faɗi wata kalma guda ɗaya cikin firgici, "U....ururu??" Ya tambayi kansa ne, domin akan idonsa yaga baƙaƙen idanuwa guda biyu a jikin fuskar wannan mutun, kuma yasan cewa ƴan ƙabilar Ururu su kaɗai suke da irinsu.

To amma babban abinda ya firgita shi, shi ne, Ururun dai sune suka jagoranci wannan yaƙi dayai sanadiyyar halin daya tsinci kansa aciki. Hasalima su suka sa, yana ɗan gawurtaccen sarki, amma ya dawo wanda bashi da kowa acikin dare ɗaya. To amma yanzu ga wani mai baƙaƙen idanuwan nan ya bayyana a gabansa!

Sautin muryarsa bai fito ba sosai, amma tsananin fushi da tsana dake ƙunshe acikin wannan kalma guda ɗaya ta 'Ururu' daya furta, sai daya jawo gaba ɗayan ilahirin wajen ya ƙara duhu, gami da cika da tsananin yanayi irin na Fansa da Tsana.

Haka dai bayan wani lokaci, wannan ma'aboci baƙaƙen idanuwa ya ɗanyi wani murmushi wanda komai iya karanta fuskarka, baza ka iya gane ma'anarsa ba, sannan ya miƙa hannunsa yai nuni izuwa wannan yaro, wanda hakan yasa yaron tashi akan iska ya taho wajenda yake tsaye, inda ya tsaya a gabansa riƙe akan iska idanunsa suna kallon waɗannan baƙaƙen idanuwa ciki da ciki.

An ɗauki lokaci a haka, kafin daga bisani a wani al'amari mai cike da al'ajabi, ya juya ya fara tafiya izuwa gabas, wannan yaro kuma ya biyo bayansa ɗaure akan iska.

Sunan wannan yaro Ikenga O. Bayajidda!
***

Acikin wannan sihirtaccen fili kuwa, bayan tsahon lokaci, Armad da wannan budurwa na zaune, kana kallonsu zaka fuskanci dukkansu sun nutsa acikin tunani; shi Armad na tunani akan wannan shekaru har sama da biyu daya bayyana cewa sun wuce ba tare da yasan ya akai yayi su ba, kamar wani a mafarki.

Ita kuma tana ta tunani akan dukkan labarinsa daya gaya mata, musamman ma tayadda ya ce mata ya shigo wannan waje, wanda a iya saninta babu wani mahaluƙi daya isa ya shigo inba da yardar ƙabilar da ake kira da Maikironomada ba.

To haka dai suka wanzu tsahon kusan rabin sa'a, kafin daga bisani ta dubi Armad gami da cewa, "wato dai kana gayamin kaima a zahirin gaskiya baka ma san tayadda ka shigo wajen nan ba?

"Kawai kayi amfani da wata fasaha ce, kuma kamar yadda kace, ka buɗe ido ka ganka anan!

"Sannan kuma kana gayamin cewa kwata-kwata baka da masaniya akan shekaru biyun da suka wuce?

Wannan budurwa ta ɗaga ido ta kalleshi babu alamun canjin yanayi kwata-kwata a tattare da ita. Sai dai duk da haka zaka iya gane cewa acikin zuciyarta abinda ke kai-komo bai wuce zantuttukan da Armad ya gaya mata, shin gaskiya ko ƙarya yake faɗa!

Bayan wasu ƴan daƙiƙu kawai sai ta ɗauke kai daga Armad gami da yin ajiyar zuciya, inda ta fara da cewa, ''wannan ƙasar da kake kai tana daga cikin yankin sihirtattun ƙasashe uku dake ƙarƙashin mulkin ƙabilar Maikironomada.

''Kuma waje ne wanda a iya sani na an killace shi ne saboda jarabawa ta musamman ga jaruman da suke takarar zama zaɓaɓɓun babban birnin Maiki na duniyar Maikironomada.

''Ban san taya akai ka shigo wannan waje ba, saboda hanya ɗaya kaɗai da ake shigowa shi ne ta ƙofar sihiri guda ɗaya kacal dake garin Arewar Maikironomada.''

Tayi ɗan shiru tana karantar Armad da ido da kuma yanayin yadda taga fuskarsa ta canja.

Bai ɗauke ta dogon lokaci ba ta fahimci cewa Armad ɗin bashi da wata masaniya bisa abubuwa da dama data faɗa.

Ta sunkuyar dakai gami da ajiyar zuciya, sa'annan kuma a lokaci na farko tun bayan haɗuwarsu da Armad fuskarta ta ɗan nuna alamun ɗan tausayi, wanda bai ɗauki sama da daƙiƙa ɗaya ba ya ɓace.

Sannan ta ce, ''toh! koma dai meye ka gane cewa yanzu tunda kariga ka shigo nan abu ne mai wahalar gaske ka tsira, kasancewar nima ka ganni anan shekara ta uku kenan ina ƙoƙarin cin wannan jarabawa na fita daga wannan waje, amma abin ya ci tura!''

Bayan wasu ƴan daƙiƙu kawai sai ta ɗauke kai daga Armad gami da yin ajiyar zuciya, inda ta fara da cewa, ''wannan ƙasar da kake kai tana daga cikin yankin sihirtattun ƙasashe uku dake ƙarƙashin mulkin Maikironomada.

''Ban san taya akai ka shigo wannan waje ba, saboda hanya ɗaya kaɗai da ake iya shigowa shi ne ta ƙofar sihiri guda ɗaya kacal dake garin Arewar Maikironomada.''

Sannan ta ce, ''toh! koma dai meye ka gane cewa yanzu tunda kariga ka shigo nan, ka shigo kenan, kasancewar nima ka ganni anan shekara ta uku kenan ina ƙoƙarin cin wannan jarabawa na fita daga wannan waje amma abin ya ci tura!''
***
To fa! Ana dara ga dare yayi, Armad ya shiga inda ba fita!!!

Sannan kuma munga kaɗan daga cikin yaƙin daya janyo mahaifiyar Armad ta samu rauni, a shekarar 1851(After Amri), har ya ɗauƙi alwashin cika mata burinta na kawo mata abinda take nema har gida.

To amma waye wannan yaro, kuma waye wannan mai baƙaƙen idanu daya ceto shi, kuma saboda me, bayan cewar dasu sukai yaƙin. shekarar 1851 After Amri (A.A), a wani gari mai suna Jíha, dake kan doron ƙasa ta bakwai ɓangaren Arewa.

To amma waye wannan yaro, kuma waye wannan mai baƙaƙen idanu daya ceto shi, kuma saboda me, bayan cewar dasu sukai yaƙin.

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...