Skip to main content

Babi na takwas : Sirrin dazai rikita duniya

Abu ɗaya da Armad yake iya tunawa a lokacin da yake tsaka da faɗawa cikin wannan wawakeken rami shi ne riƙe takobinsa da yayi, ya ɗaure ta a jikinsa.

Amma bayan wannan, gaba ɗaya hankalinsa dusashewa yayi, kafin daga bisani ya sume gaba ɗaya.

To koma dai mai ya faru bayan wannan, wanda bazai iya tunawa ba, to yana ganin bai halaka shi ba tunda a dai-dai wannan lokaci ya tsinci kansa a kwance a kan tantagaryar ƙasa da kuma ragowar numfashi a jikinsa, ga kuma waɗansu abubuwa daya kasa tantancewa a tsaye a kansa...

"Hmmmm...." Cikin firgici Armad yai ajiyar zuciya, acikin ransa bayanda kwatsam abin ya faɗo masa a rai cewa ko mutuwa yayi.

A hankali a hankali, ganinsa yana ƙara dawowa, waɗannan halittun dake bisa kansa su na ƙara bayyanuwa, sai ya gano cewa ashe mutane ne!

Ba daɗewa ya gano cewa ashe maza ne guda biyu da mace ɗaya.

wadda ke tsaye a bayansu.

Mamaki ya cika zuciyar Armad kuma hankalinsa ya ɗan kwanta, lokacin da yaga macen dake cikinsu ta cillo masa bututun ruwa.

Amma kafin ma ta ƙaraso wajensa ɗaya daga cikinsu wanda ke tsaye a daman Armad yasa ƙafa ya doke bututun, yana mai cewa, ''meye amfanin shayar dashi!''

Babu wanda ya ce uffan acikinsu akan wannan abu daya afku, kuma akan idon Armad wannan mutun ya gabato gareshi da farar ankwa ya ɗaureshi gaba da baya.

Sannan suka ɗaureshi shi akan wani doki ƙarami samfurin ak-wali, sannan suka hau nasu dawakan suka nufi gabas.
Lokaci bayan lokaci Armad zai farka ya ji basu daina sukuwar da suke ba kafin ya ƙara komawa.

Bai san tsahon lokacin da sukai su na tafiya ba, abu na gaba daya gani shi ne, farkawa acikin wani ɗan tanti ɗaure acikin ankwa.

Bayan ya nuts, abinda ya fara lura dashi shi ne, kwata-kwata jikinsa babu alamun ciwo ko kaɗan, lamarinda ya bashi mamaki sosai, saboda sanda ya fara buɗe idonsa bayan faɗowarsa daga wannan waje, baya ko iya motsa jikinsa saboda ciwo.

Yana ɗaga ido yai arba da waɗannan mutane ne uku da suka ɗakko shi, zaune akan kujerun alfarma da akaiwa ado da jan dinare, inda ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Yana kwance, baya iya motsa komai a jikinsa face idanunsa, wanda yayi amfani dasu wajen ƙurawa suturar dake jikin wannan mutane kallo.

Dukkaninsu a sanye suke da kayan yaƙi, wanda kallo ɗaya ya isa mutun yasan cewa masu tsadar gaske ne, kuma na sarauta.

Mafi tsayi acikinsu namiji ne, yana tsaye bisa saitin kan Armad, sai kuma mai biye masa, wanda ke tsaye a gwiɓinsa, sai kuma macen, Babban cikinsu magidanci ne wanda tabbas zaifi shekaru talatin.

Yana da ƙira cikakkiya abar dacewa da sadaukai. Domin tun daga inda Armad yake yana iya hangen murɗaɗɗen zubin jikinsa. Da kafaɗunsa masu faɗin gaske duk da cewa bashi da tsayi sosai.

Fuskarsa tana da ɗan tsayi, amma saboda faɗin ta ba sosai mutun zai iya kula da tsayin ba.

Babu gashi da yawa a fuskar tasa, face wani ɗan gemu mara tsayi sosai.

Sai kuma mai biye masa, wanda a karon farko da Armad ya kalleshi ya yanke shawarar cewa ƙanin wancan zabgegen ne.

Badan komai ba saboda kama da suke da juna, duk da kuwa cewa babban ya fishi girma sosai da sosai, amma kana ganinsu zaka ga kama.

Dukkanin su, su na sanye da ƴar shara ta jan alharini, wadda akaiwa ado da zinare daga wuya zuwa ƙasa.

A wannan lokaci ne kuma idanunsa suka kai ga macen dake gefensu.

Yana ɗora idonsa akanta ya ce, "kai!!!" Cikin mamaki ya ƙara wara idanuwansa saboda wani abu dake faruwa a dai-dai wannan lokacin.

Ba komai bane yake faruwa illa kasancewar Armad acikin waniyanayi da yake ji a ransa cewa lallai ya taɓa ganin wannan budurwa, sai dai kuma a lokaci guda hankalinsa na tambayarsa a ina!

Bakinsa a buɗe, mamaki kawai yake akan abinda ke faruwa, sannan kuma yana ƙara tambayar kansa akan wace ce taƙamaimai wannan budurwar!

Duk da ƙarancin shekaru na Armad amma bai daɗe yana kallonta ba, ya tabbatarwa da kansa cewa lallai bai taɓa gani ko jin halitta mai kyawunta ba, kai koda a zane ko kuma a labarai da tarihin fararen aljanu!

Tuni Armad ya ƙurawa wannan budurwa, wadda bata fi sa'ar sa ba ido, bama tare da ya sani ba. Badan komai ba saboda kwatsam yaji a ransa cewa lallai akwai yiwuwar idan ya fiya kallon fatar jikin wannan budurwa,  zai iya samun damar ganin wucewar jini da idonsa, kamar yadda ya ji ya faru a 'Hikayar Lasína Naitingel', macen da aka ce ba'a taɓa haifar wata data kaita haske ba!

Sai dai amma Armad bai samu damar cimma burinsa na ganin hakan ba, domin a dai-dai lokacin ne ya fuskanci cewa ashe a ɗaure yake tamau acikin ankoki!!!

Ba shiri ya dawo hayyacinsa, tare da canja fuska gami da cewa, "wai su waye ku, kuma me nayi muku da zaku ɗaure ni acikin ankoki haka!"

Bai ƙarasa rufe baki ba, saurayin dake ɓangaren dama ya dubeshi a fusace gami da cewa, "mu zamuyi maka tambaya, bakai zakai mana ba.

"Saboda haka abu na farko daya kamata ka sani shi ne, muna so kayi mana wani abu guda ɗaya, idan kayi shi, zamu sake ka ka tafi, idan kuma baka yishi ba to...!" Saurayin na zuwa nan a zancensa sai ya ja numfashi tare da kallon doguwar takobinsa yana kuma yiwa Armad inkiya da ita.

Mamaki ne kawai ya cika zuciyar Armad, ya kuma rasa mai zaice, lamarinda yasa nan take ransa ya ɓaci. Amma koda ya duba ya ganshi ɗaure acikin ankoki sannan kuma ga takobinsa can a ajiye a gabansu, sai yasan babu abinda zai iya a wannan lokaci, banda sauraronsu yaji mai suke tafe dashi.

Ba tare da ɓata lokaci ba, ɗaya namijin ya taso daga inda yake, ya gabato gaban Armad a hankali. Inda yana zuwa ya zaro wani ɗan allo daga cikin ƙasaitacciyar alkyabbarsa ya nunawa Armad.

Sannan kuma a lokaci guda da ɗanyatsansa na dama ya nunawa Armad wasu rubuce-rubuce a gaban allon wanda aka yisu tayadda suka kewaye izuwa fasalin ƙawanya, gami da cewa, "abinda kawai muke buƙata da kai shi ne ka ɗisa jininka acikin wannan ƙawanya." Muryarsa a nutse take, tamkar babu wani tashin hankali aciki ko kuma damuwa aciki, amma kana kallon idanunsa zaka ga wani abu mai kama da buri, wanda zai tabbatar maka da cewa ko ma mai suke nema a game da Armad, lallai babban abu ne.
Wannan allo ya kasance yana da matsakaicin girma, kuma fari ne mai ɗan duhu. Sinadarinsa kuwa yana kama da sinadarin haƙorin bakin ɗan adam.

 Sheƙi kawai yake da ɗaukar ido duk da rana bata haska shi ba.

A tsaye baifi kamu biyu ba, sannan bashi da kauri kwatakwata.
Ƙurawa wannan rubutu ido kawai Armad yayi tsahon lokaci yana nazari, kafin daga bisani ya gane anyi shi ne da tsohon yaren Aldurish! Yaren da kusan zaka iya cewa an manta dashi kwata-kwata a wannan lokaci.

Saboda sama da shekara dubu aka maye gurbinsa da sabon yaren Aldurish, wanda akewa laƙabi da Aldurish-Amri saboda alaƙarsa da Amri. Kuma kusan kowa ya iya Aldurish-Amri, amma samun mutun ɗaya daya iya Aldurish-tsoho, dai-dai yake da samun raƙumi acikin kuratandu.

Armad na ganin wannan yare yasan cewa lallai waɗannan mutane dake gabansa kodai ƴaƴan manyan sarakuna ko kuma sun fito daga cikin manya-manyan ƙungiyoyi, domin a iya tunaninsa indai ba haka ba to babu yadda za'ai su samu wata alaƙa da wannan yare.

Armad ya iya wannan yare sosai da sosai, duk da cewar sai da ya ɗauki lokaci mai tsahon gaske yana koyonsa a wajen mahaifiyarsa.

Saboda haka yana gani wannan rubutu, ya karance shi. Ya kuma ƙara tabbatar da cewa abinda suke nema lallai babban abu ne. Saboda haka sai ya fara tunanin mafita.

Badan komai ba, sai dan cewa daga cikin ƴan dabarun daya ilmantu dasu a iyakacin ƴan shekarunsa, yasan cewa abu ne mai sauƙi bayan yayi musu abinda suke so, su halaka shi.
Ƙurawa wannan rubutu ido kawai Armad yayi tsahon lokaci yana nazari, kafin daga bisani ya gane anyi shi ne da tsohon yaren Aldurish! Yaren da kusan zaka iya cewa an manta dashi kwata-kwata a wannan lokaci.

Saboda sama da shekara dubu aka maye gurbinsa da sabon yaren Aldurish, wanda akewa laƙabi da Aldurish-Amri saboda alaƙarsa da Amri. Kuma kusan kowa ya iya Aldurish-Amri, amma samun mutun ɗaya daya iya Aldurish-tsoho, dai-dai yake da samun raƙumi acikin kuratandu.

Armad na ganin wannan yare yasan cewa lallai waɗannan mutane dake gabansa kodai ƴaƴan manyan sarakuna ko kuma sun fito daga cikin manya-manyan ƙungiyoyi, domin a iya tunaninsa indai ba haka ba to babu yadda za'ai su samu wata alaƙa da wannan yare.

Armad ya iya wannan yare sosai da sosai, duk da cewar sai da ya ɗauki lokaci mai tsahon gaske yana koyonsa a wajen mahaifiyarsa.

Saboda haka yana gani wannan rubutu, ya karance shi. Ya kuma ƙara tabbatar da cewa abinda suke nema lallai babban abu ne. Saboda haka sai ya fara tunanin mafita.

Badan komai ba, sai dan cewa daga cikin ƴan dabarun daya ilmantu dasu a iyakacin ƴan shekarunsa, yasan cewa abu ne mai sauƙi bayan yayi musu abinda suke so, su halaka shi.

Amma kuma bayan ɗan lokaci kaɗan, yana kallonsu suna kallonsa. Gashi acikin ankwa, gashi shi kaɗai su uku, sai kawai ya yanke shawara duk abinda zai aiwatar zai ta'allaƙa ne da mai ya faru a gaba bayan ya ɗisa jinin nasa.

Badan komai ba, saboda baiga wata hanya dazai ƙi saka jinin nasa kuma su ƙyaleshi ba. Kuma idan suka samu matsala tun daga ɗisa jinin, ya tabbatar da cewa yiwuwar kuɓutarsa a gaba ta ƙara raguwa.

Saboda haka ya yanke shawara ya nuna musu ya amince zai aikata hakan.

Lamarinda yasa wannan saurayi daya taso ya zare farar doguwar takobinsa tare da nunawa Armad kakkaifan tsininta, yana mai cewa, "ina kake so na fasa?" Babu alamun tausayi ko kaɗan a tattare dashi, sai dai kuma shima Armad babu tsoro a tattare dashi. Domin tuni yayi masa nuni da tafin hannunsa na dama.

Haka kuwa akai ba jimawa jinin Armad ya ɗisa akan wannan allo acikin wannan ƙawanya.

Hakan na faruwa ragiwar mutun biyun dake zaune, suma suka taso suka tsaya akan Armad, inda macen tai wani ɗan ƙaramin murmushi wanda bai ƙunshi alamun komai, tare da cewa, "Nan bada jimawa, sak irin muryar da kaji acikin wancan gari zatai magana daga cikin wannan allo.

"Abinda kawai muke so shi ne ka gaya mana abinda tace!!"

Duk da ƙarancin shekaru irin na Armad, amma a dai-dai wannan lokaci abu ɗaya ne kawai yake ta kai-komo a zuciyar sa, wanda shi ne kawai yanayin yadda maganar wannan budurwa take shafar hatta iskar dake ilahirin wajen; kasancewar Armad zai iya rantsewa indai ba mafarki yake ba, to lallai yaga iskar cikin wannan tanti tana ƙara kyau.

Bai gushe ba yana cikin wannan hali ba, har sai da yaga takobin ɗaya daga cikin samarin nan biyu a wuyansa tukun. To sai a wannan lokaci ne ya fara tuno abinda yaji ta faɗa na game da wancan murya.

Sannan kuma ya fara mamakin yadda akai ta san al'amarin shigarsa wancan gari.

Sai dai kuma tunda dama Armad ya kasance mutun ne mai saurin gane abubuwa, ba jimawa ya biɗe baki cikin mamaki yana kallon wannan budurwa tare da cewa, "Gimbiya Nostalgiya Nára?"

Tsahon daƙiƙu bata ce masa komai ba, kafin daga bisani ta kalli Armad ido cikin ido sannan a yanayi daya kamace ta ce, "to kaga na cece ka a baya, to kaima yanzu ya kamata indai kaji wannan murya kada ka ɓoye mana domin tana da muhimmanci a garemu."

Armad shima baice komai ba sama da daƙiƙa sittin tamkar ma bazai ƙara magana ba, kafin can daga bisani ya ja dogon numfashi ya fara bayani da godiya, "na gode Gimbiya, lallai kin ceci raina a baya, kuma nima yanzu zan saka miki da alkhairi!

"Ina mai tabbatar muku da cewa koda kun kwance bazan je ko'ina har sai wannan murya tayi magana! Wannan shi ne aƙƙawari na a gareki gimbiya!"
Armad bai sani ba, amma tuni ya fara kallon wannan mace a matsayi na musamman!!

Suna jin haka suka kalli juna, sannan bayan sun ja gefe, sun kuma gama yin ƙus-ƙus, sai suka dawo suka kwance Armad.

Ba jimawa tuni har Armad ya fara jansu da hira, musamman ma gimbiya Nostalgiya, inda yake tambayarta tayi masa bayanin yadda akai ta same shi acikin wannan gari da kuma yadda ta ceto shi ta kaishi bakin wannan ruwa da kuma yadda har tasan takardarsa ta ƙone kuma ta canja masa wata.

Sai dai kuma kash, duk tambayoyinsa babu wadda ta samu amsa. Domin kuwa ga dukkan alamu daga kan gimbiyar har samarin guda biyu basu da saurin sabo, ba kamar shi Armad ɗinba; wanda yake da saurin sabo da kuma son raha.

Amma dai duk da haka daga ƙarshe saida yaji cewa dukkansu ƴan uwa ne, kuma babban sunan sa Hasanu Sísiyu Nára, ƙaramin kuma Kíru Sísiyu Nára, sai kuma ita gimbiyar wadda tace masa sunanta na asali Zahra Sísiyu, amma saboda wasu dalilai kowa yanzu Nostalgiya Nára Sísiyu yake kiranta.

Duk da a lokacin Armad ya lura da cewa ƴan uwan nata biyu basu ji daɗin wannan sirri data gaya masa ba!! Amma kawai dai suka ɗauke, duk da daga baya saida babban ya gaya masa cewa wannan sunan nata kada ya gayawa kowa, domin ba'a faɗa yanzu!

Armad baice komai ba kawai ya amsa da "eh!"

Haka Armad yai ta ƙoƙarin jansu da hira amma bai samu nasara sosai ba, duk da kuwa kusan ya gama ɗebe labarinsa kaf ya gaya musu in banda sunan sa na gaskiya dabai faɗa ba; inda ya ce sunansa Armad Djinn!

Suna cikin haka kwatsam sai ji sukai Armad yai shiru yana cikin magana! Lamarinda ya tabbatar musu da cewa wannan allo dake hannunsa ya fara maganar.

Nan take suka tattaso daga inda suke, suka tsaya akansa. Inda a lokacin tuni hankalinsa ya fara gushewa, baima san inda kansa yake ba.

Sai dai kuma ba kamar a cikin wancan gari ba, a wannan lokaci cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗari biyu ba ya farfaɗo!

Inda bayan ya farka ya dawo hayyacinsa ya ɗaga kai ya kalle su, fuskarsa cike tsananin mamaki da firgici, saboda yaji abinda bai taɓa zato ba bai kuma taɓa tsammani ba.

Amma kafin ya fara magana, bisa ƙarin mamakinsa kawai sai yaga duk su biyun sun juya sun kalli gimbiyar. Inda ita kuma ta kyaɗa musu. A dai-dai lokacin da Armad yaji kamar wani abu ya shiga cikin kansa ya karanta wannan murya da yaji sannan kuma ya fice.

Duk su biyun suna ganin haka sukai wata dariya mai cike da murna da annushuwa da nuna cikar buri.

Kafin daga bisani babban nasu ya dube su cikin murna tare da cewa, "ta wacce hanya kuke ganin yafi kamata mu kashe wannan yaro, mu ƙarasa aikinmu!!"

Magana ce mai kama da tambaya, amma kana gani kasan ba amsar kowa yake nema ba, illa tasa. Domin kuwa kawai Armad yake kallo yana murmushi.

A dai-dai wannan lokaci Armad  ƙoƙari yake ya gane meke faruwa, saboda acikin ƴan daƙiƙun da suka wuce, lallai yaji gilmawar wani abu a kwakwalwarsa, amma yaƙi amincewa ya yadda da cewa kwakwalwarsa suka duba, sai dai kuma cewa lallai yasan cewa hakan ne ya faru daga abinda yaji babban nasu ya faɗa, wanda ke nunawa Armad, kamar basa buƙatar suji abinda yaji.

Ba jimawa Armad ya haɗa ɗaya biyu, ya kuma gane cewa lallai akwai yiwuwa wani daga cikin wannan mutun uku nada Izzar da take iya duba abinda ke cikin kan mutane.

Kuma akwai yiwuwar anyi amfani da ita akansa, a wannan lokacin.

Wannan tunani na shiga kansa ya ɗaga ido ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Yana zuwa kan wannan budurwa ya tsaya.

Ba dan komai ba, saboda wani abu a jikinsa na gaya masa cewa tabbas, koma mai ya faru ita ce, musamman idan ya tuno da yadda yaga samarin biyu sun kalle da farko.

Armad ya gayawa kansa cewa koma dai mai ya faru, lallai a wannan lokaci basa buƙatar ya gaya musu wani abu, domin kuwa gashinan a gabansa ana tattauna ta wacce hanya yafi kamata a kashe shi, wanda hakan ya bashi dukkan tabbashin da yake nema.

Abin al'ajabi mutanen da basu daɗe hira dasu ba amma gashi suna tattauna ya zasu halaka shi a gaban idonsa kamar ma baya wajen; babban nasu ya ce kawai su ɗaureshi su cillashi acikin ruwa, ƙaramin ya ce kawai su sare masa kai da takobi a wajen, macen kuma bata ce komai ba da farko.

Sai da taga sun rasa wacce zasu zaɓa aciki, har suna neman jefa ƙuri'a, sannan ta dubi babban nasu tace, "ahhh, mai zai hana, a haɗashi da yaya Kiru su fafata, in yaso idan suka gama faɗan sai ku san mai zaku yi dashi daga baya." Kamar wadda take tsoron kada suƙi yadda da shawararta, sai tayi sauri taci gaba da cewa;

"Badan komai ba, saboda inason naga faɗan Yaya Kiru, da kuma sabuwar fasahar da kace ka koya masa!"

Tana rufe baki babban nasu yai murmushi gami da girgiza kai, ya ce, "a'ah, ki bari idan munje gida....."

Amma ina tun kan ya rufe baki ƙaramin da ta kira da Yaya Kiru ya miƙe tsaye gami da duban babban nasu ya ce, "Yaya Hasanu, kullum kana gaya mana wataran mu zamu kare Burja, kuma wataran mu zamu tsaya a gaban filin daga mu jagoranci yaƙi ko, to ina roƙonka daka bani wannan dama na nuna maka Izza ta!"

Yana gama faɗa ya sunkuyar da kansa ƙasa, amma tun daga nesa zaka iya jin yanayin marmarin yaƙi na tashi daga jikinsa. Babu abinda yake jin tsoro face Yayan nasa ya ce a'a.

Amma yana cikin wannan hali yaji yayan nasa ya ce, "tohhh!

"Nuna min na gani! Kai sani ina sa ran ganin abinda zai faranta min rai!!"

Amma yana cikin wannan hali yaji yayan nasa ya ce, "tohhh!

"Nuna min na gani! Kai sani ina sa ran ganin abinda zai faranta min rai!!"

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...