Daga gefe, idanun Hasanu da wannan budurwa acike suke da mamaki, kuma zuwa wannan lokaci su na da cikakkiyar masaniyar cewa shima Armad, koma daga ina yake, lallai ya sami horo na musamman.
Dukkaninsu sun san irin ƙarfin da farar takobin Kiru ke dashi, amma bisa mamakinsu Armad ya iya tare sara daga gareta kuma ba tare da yaje ƙasa ba.
Hasanu ya ja numfashi sannan ya ƙara matsawa gaba, gami da ƙara ƙurawa Armad ido.
Ya kalleshi sama da ƙas, sannan bayan wani ɗan lokaci sai kawai idanunsa suka canja, kamar wanda yake so yaga wani abu a tattare da Armad, amma kuma ya kasa.
Yana shirin ɗauke ido daga kan Armad, sai idonsa yakai kan wannan jan ƙyalle dake ɗaure a gaban goshin Armad.
Nan take ya ƙura masa ido tsahon daƙiƙu, kafin kwatsam idonsa ya cika da firgici sannan jikinsa ya fara karkarwa.
Cikin ɗimuwa ya fara magana aciki, "madauwamiyar Miyura... ina ba abu bane mai yiwuwa... to amma...
''Hmmm.... ko madai ba ita bace a goshinsa ba, kashe shi a yanzu ganganci ne, ya zama wajibi na koma dashi Sisiya, in yaso na ƙara duba littafin 'Matsayin-Izza' na shugaba Jána Sisiyu, kafin na kaiwa sarki wannan babban labarin!''
Yana zuwa nan a zancansa ya ɗaga kai domin kawo ƙarshen wannan fafatawa dake faruwa, tsakanin Armad da Kiru da niyyar tafiya da Armad ɗin can garin Sisiya, wajan sarki.
To amma a dai-dai wannan lokaci ne Kiru ya ƙara kawo wa Armad wani wawan saran.
Amma abinda Kiru bai sani ba shi ne tuni ya bayyana ga Armad cewa lallai, idan ya bari suka ƙara haɗuwa da wannan farar takobin ta Kiru, a irin karo na farko, tofa lallai sakamakon bazai masa kyau ba. Saboda haka tuni ya riga yayi wata sabuwar shawara acikin ransa.
Yayi shawara cewa zaiyi amfani da wani hari na musamman shima, ya kuma afkar da wani gagarumin ɗauki akan Kiru wanda zai bashi dama ya ci nasara cikin sauri ba tare da bawa abokin karawar tasa dama ba.
Saboda haka tuni ya gama shiri, a lokacin da Kiru yake ƙoƙarin afka masa da wannan farar takobi.
A dai-dai wannan lokaci takobin Armad ta fara fitar da wani irin hayaƙi.
Kan kace meye wannan gaba ki ɗaya kewayen Armad ya cika da irin hayaƙin, ta yadda da kyar ake iya hangoshi a tsaye cak a tsakiya.
Dukka wannan baisa ko kaɗan Kiru ya dakata ba, illa kawai ƙara azaba da yai wajan afkawa Armad ɗin.
Kamar ana ziga wannan farar takobi dake hannun Kiru, wani farin haske mai tsananin haske ido ya fara ambaliya daga jikin ƙarfenta.
Sannan kuma idan ka lura ma zakaga kamar ta ƙara tsayi da kimanin kamu ɗaya To a dai-dai lokacin ne, su biyun suka haɗu kuma suka afkawa juna da sara, takubbansu suka haɗu a sama, ga mi da fitarda wata ƙara mai rikitarwa, wadda tasa saida Zahra ta rufe kunnuwanta da hannayenta.
Iska mai ƙarfin gaske ta kaɗa, wadda tayi ƙoƙarin cilli dasu daga wajan da suke tsaye. Iskar ta ƙarasa ta daki bishiyun dake kewayen wajen wanda hakan yasa nan take reshinansu suka fara girgiza, kamar zasu cire.
Kan kace meye wannan ƙura ta turnuƙe, har takai basa iya ganin koda tafin hannayen su. Babu abinda suke ji illa girgizar ƙasar da suke kai kurum.
''Dukkanin abinnan dake faruwa sara ɗaya ne kurum ya janyo, daga jikin takubbansu!!!''
''Eh...'' Hasanu ya ja dogon numfashi, yayinda baki a buɗe, fuska a yamutse cike da mamaki ya bar ƴar uwar tasa, acikin ƙurar nan ya nufi cikin wajen da su Kiru suke fafatawa da gudun gaske.
Ba wani abu bane ya jawo haka ba illa wata halitta da yaji a jikinsa ta fito daga cikin Bangon Arewa tana kuma gabato wajen da suke.
Wannan halitta ba wata aba bace, illa ɗaya daga cikin fatalwowi na musamman dake cikin wannan waje.
Kasancewar dama tunda farko wajan da suka kafa tantin nasu bashi da nisa da Bangon-arewar ta yadda zaka iya hangensa daga nesa.
Akwai wani karin magana da kusan kowa ya sani a wannan zamani, wanda indai kaji shi, to kawai kasan ana magana ne akan waɗannan bangwayen ruwa biyu.
Wannnan karin magana kuwa shi ne, ''Mafakar mutuwa!''
Wanda ya samo asali ne tun da daɗewa, saboda wani dalili guda ɗaya.
Wannan dalili kuwa shi ne, da dama daga cikin al'ummatai na wannan zamani su na da fahimtar cewa, dukkan mutumin daya mutu anan ruhinsa yake fara yada zango kafin wani lokaci.
Hakan kuma ya samo asali ne daga yawan fatalwowi da suke zaune akan wannan ruwa.
Kuma babban abun mamakin shi ne, da dama mutane sukan ga fatalwar wani wanda suka taɓa sani a lokacin yana raye a wannan waje musamman a wasu lokuta na shekara.
Babban tashin hankali ga al'amarin waɗannan fatalwi shi ne yadda suke cin naman mutun ɗanye wanda har takai sukan kifarda jirage, sannan su halaka fasinjoji.
To amma a dai-dai lokacin da Hasanu ke ƙoƙarin isa wajen wannan fafatawa dake faruwa,
Wannan haɗuwa da farar takobin Kiru sukai da takobin Armad mai fitarda hayaƙi, ya haddasa wata mummunar girgizar ƙasa, wadda cikin ɗan ƙanƙani lokaci ta fara zagwanyar da dukkan ƙasar da suke kai.
Abin ya fara ne a iyakacin kewayen ƙasar dasu Armad kekai, amma cikin daƙiƙa kaɗan ya fara bazuwa ko'ina.
Kan kace meye wannan dukkaninsu sunyi tsalle sama izuwa kan ƙasar dake gabansu, domin kaucewa faɗawa rami, sai dai kuma bisa rashin sa'a, ƙafafunsu na dira kan ƙasar ita ma ta fara rududduge wa.
Kuma kan kace meye wannan ƙasar da Zahra ke kai, ta rabe gida biyu kuma tana neman afkawa ciki. Lamarin da yasa cikin tsananin zafin nama Hasanu ya juyo da niyyar riƙota, amma tun kafin ya ƙarasa ya ji a jikinsa cewa wannan fatalwa data fito daga cikin wannan ruwa ta kusa cimma su Kiru.
Nan take Hasanu ya ƙara azama, inda yai maza ya riƙo Zahra, ya hanata faɗawa wannan rami.
Sannan kuma cikin sauri ya ajiye ta acan gefe guda, ya kuma juyo da niyyar ceto Kiru daga harin sumame da wancan fatalwa take neman yi musu.
To amma abinda bai sani ba shi ne, tuni Kiru yasan abinda ke faruwa kuma ya yanke shawarar me zaiyi.
Kan kace meye wannan, sunyi hannun riga, Kiru yayi yamma Armad yayi gabas, shi Kiru yana ƙoƙarin gujewa fatalwar, shi kuma Armad yana ƙoƙarin gujewa wannan ramika.
Kan kace meye wannan, ratar dake tsakaninsu takai kimanin taku bakwai. Hakan kuma ya faru ne ba tare da saninsu ba, domin su kawai gudu suke suna tsallake rigiya da baya daga wannan waje zuwa wannan a tsakanin wannan girgizar ƙasa.
Wani abu da duk su biyun suka fuskanta shi ne, lallai bawai kaɗai harin da sukai amfani dashi bane ya janyo wannan girgizar ƙasa ba, dole akwai wani abu a ƙas.
Duk inda suka taka kafin ma su ajiye ɗaya ƙafar, shima ya fara zaizayewa, to amma daya ke dukkanin su biyu ba mutane bane wanda suka daɗe acikin duniyar horo ba, kawai yara ne waɗanda aka haifa da baiwa, wanda kuma hakan lallai bai kai a wannan lokaci yasa su tsere daga mahaukacin saurin da zaizayar ƙasar ke faruwa dashi ba.
Hakan ne yasa bayan kimanin daƙiƙu shida ta cimmusu, ta yadda takai ƙafafunsu suka dira a dai-dai lokacinda itama ƙasar take cinyewa, saboda haka suka rufta ƙas ba shiri.
To amma ga dukkan alamu sa'a tana tare dasu a wannan lokaci, inda wannan girgizar ƙasa ta tsaya a dai-dai lokacin da sukai amfani da hannayen su wajen riƙe ƙarashen ƙasar da bata ƙarasa rushewa ba.
Hakan na faruwa suka miƙa hannayensu, suka kuma riƙe waɗansu tubalin ƙasa waɗanda suma sauran ƙiris su cire.
Kasancewar kuma duk su biyu a gine suke da jiki murɗaɗɗu, kuma wajajen da suka riƙe basu da kwari sosai, bai ɗau lokaci ba kafin wajan da suka riƙe ya fizgine, su ƙara nufar faɗawa.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne Hasanu ya isa wajen, inda ya riƙo hannun Kiru, ya kuma fara janyoshi waje.
To amma a dai-dai lokacin ne idanunsa suka cika da mamaki saboda abinda yai arba dashi.
Zahra, wadda bai daɗe da ajiyeta a can gefe ba, ita ce a kwance a rigingine, dai-dai wajen da Armad ke ƙoƙarin faɗawa inda hannunta na hagu ke miƙe a gabanta riƙe da hannunsa.
Shima Kiru wanda yake jira a janyoshi waiwayawa kawai yayi, yayinda ya fuskanci inda Hasanu ke kallo.
Armad ya dubeta idanunsa cike da yanayi na rashin fahimta.
Nan take ya shiga wani yanayi mai tsananin ban mamaki da alajabi. Irin wanda bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa.
Hannunta na taɓa nasa, yaji wani a jikinsa cewa lallai ya taɓa ganin wannan budurwa, kai bama iya haka ba, har wasu hotuna yake gani acikin kansa wanda suke nuna masa wasu mu'amaloli da suka faru tsakaninsa da wannan budurwa a baya, lamarinda yai matuƙar ɗimauta hankalinsa.
Ya cika da mamaki, domin kuwa yasan lallai duk waɗannan abubuwa basu taɓa faruwa ba. Hasalima bai taɓa ganinta ba, sai a wannan lokaci.
To amma bisa mamaki, abubuwan da yake ji, sunfi gaban ace mafarki yake. Domin kuwa a zahiri yake ganin abin, kamar ma bai daɗe da faruwa.
Dukkan abin daya gani, bai haura daƙiƙa biyar ba, amma shi yana jin kamar ya kai daƙiƙa dubu a jikinsa.
Ya buɗe baki zaiyi magana, to amma duk da cewa akwai samada tambayoyi dubu da zaiso ta bashi amsa, amma bisa ya kasa cewa komai!
Kafin ya iya rufe bakinsa kawai sai wata kwayar hawaye ta fito daga idanun Zahra ta kuma nufo idanunsa.
Kuma saboda yanayin yadda suke a lokacin, kai tsaye hawayen ya ɗisa acikin idonsa.
Lamarinda baiyi wani abu naya hanashi faruwa ba.
Babu abinda yake ta kai-komo a ransa sai tunanin a ina ya taɓa ganin wannan kyakkyawa??
Zahra ta buɗe baki kenan zatai masa magana, fuskarta acike da murmushi, sai kawai yaga murmushin fuskarta ta ya dusashe a lokaci ɗaya, sannan kuma an maye gurbinsa da tsananin tsoro da firgici.
Kafin yayi wani abu tuni Zahra ta saka dukkan ƙarfinta wajan ƙoƙarin janyoshi waje.
Idanunta nakan wani abu dake doso wajan da suke ta baya.
Bai ɗauki lokaci ba ya fahimci cewa akwai wani abu mai hatsari dake kusanto shi ta baya.
Kafin ma ya ƙarasa juyawa muryar Kiru wanda tuni Hasanu ya fito dashi, suke kuma nufosu da gudu, ta isa cikin kunnensa, yana kwala ƙara kamar maƙokwaransa zai fashe, ''Kinsan cewa idan fatalwa ta taɓa shi kina riƙe dashi har kema abin zai shafa, KI CIKASHI!!!''
To a dai-dai wannan lokacin ne Armad ɗin ya juya ya hango wata siffa mai tsananin firgitarwa tana nufoshi daga nesa da wani mugun sauri mai kamar walƙiya.
''So kike yi ki mutu, saboda wannan yaron da ba kowan kowa ba!!'' Inji Kiru wanda ya ƙara azama a ƙoƙarinsa na isa wajanda suke.
Shima Hasanu wanda fuskarsa ke cike da rashin-fahimta da mamaki, da kuma ɗimuwa, musamman ma yasan shi alhakin kula da ita ke kansa, ya fara roƙonta, ''kinsan muhimmancinki a gurin mahaifinki, dama dukkan al'ummar ƙasar Sisiya, kada kiyi haka, koma me kike tunani akansa, kuma ko meye dalilinki!!''
A dai-dai wannan lokaci saboda tsananin saurin da wannan halitta ke tafiya dashi tuni ta iso inda Armad yake, wanda har a sannan Zahra bata ƙarasa janyo shiba.
Nan take ya gane mai maganganun su Hasanu suke nufi, ya kuma fuskanci dukkan abinda ke faruwa, kasancewar duk da bai taɓa ganin irin waɗannan fatalwowi a gaske ba, amma ya taɓa karanta su a littafi;
Ya fahimci cewa saurin da wannan fatalwa take yi, yafi wanda su Hasanu keyi, kuma tabbas kan su ƙaraso wajen da suke, wannan fatalwa zata rigasu.
Saboda haka komai yana hannunsa da wannan budurwa, mai suna Zahra, kodai ta sake shi ta tsira, kodai taci gaba da riƙeshi su halaka tare.
Amma ga dukkan alamu bata da niyyar sakarsa, koda kuwa wannan halitta zata cimmusu!!
''Hmmmm,'' yayi ajiyar zuciya, sannan kuma ya kalli idanun wannan budurwa wadda ke ta ƙoƙari iyakacin ƙarfin ta wajen zaroshi amma ina saurin wannan halitta yafi gaban misali tuni ta cimmusu.
Tana kuma dab da taɓa jikin Armad!
***
Shin kuna ganin zai yiwu, baka taɓa ganin mutun ba, amma kaji kamar ka taɓa ganinsa, harma kana tuno wasu abubuwa da suka faru a tsakaninku kamar a gaske???
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved.

Comments
Post a Comment