Skip to main content

Babi na sha Uku : Wacce Shekara Muke wannan??

Tun bayan ɓacewar Armad daga wannan waje, hankalinsa ya dusashe ta yadda shi kansa bayan farkawarsa bai san a inda yake ba, bai san kuma tayadda yaje wajen daya farka ya tsinci kansa ba, sannan kuma bai san kwana nawa yai ba, tun bayan dusashewar hankalinsa ba.

Amm abu ɗaya da yake iya tunawa shi ne, gab da kafin hankalinsa ya dusashe, ya kasance yana ta kai-komo da abubuwan sirrin da yaji daga wannan murya wadda take magana akan Rukunai guda biyu na Ururu. Sirrin da Armad ya tabbatar indai ya fita to lallai sai ya rikita dukkan duniyar ƙasa bakwai, tayadda zaman lafiya ma zai iya zuwa ƙarshe!!

Da farkawarsa abinda ya fara yin arba dashi shi ne fili fetal gabas da yamma, gudu da arewa ko ina ya duba baya iya gano ƙarshensa.

Babban abun mamaki da wannan waje shi ne babu alamun wata halitta a wajen ko kaɗan; kama daga kan namun daji zuwa tsirrai zuwa tsuntsaye, ko'ina ka duba ba komai a wajen kawai sai fili fetal da tsandaurin ƙasa.

Sai dai kuma Armad bai shiga al'ajabin ganinsa a wajen ba, saboda ba wannan karonsa na farko ba da yayi amfani da irin wannan fasaha, kuma ya samu kansa acikin wannan yanayi ba.

Kuma daya tambayi kakansa dake koyarda shi, sai ya ce masa sakamakon rashin kwarewa ne.

Amma wannan bai hana Armad yin amfani da wannan fasaha ba, lokaci zuwa lokaci idan ya tsinci kansa a mawuyacin hali. Kuma kamar koda yaushe yakan farka a wani waje tafiyar wuni ko kwana ɗaya daga wajen da yayi amfani da ita.

Iya hangensa baya iya ganin koda shuka guda ɗaya a wannan waje. Babu komai sai kurum tsandauri iyakacin hange.

Armad ya samu kansa a kwance bayan farkawarsa, sannan kuma daga bisani bayanda hankalinsa ya fara dawowa kansa sai ya lura cewa kayan jikinsa ma ba nasa bane.

Yana ganin haka yasan tabbas duk da alamun wajen baya nuna wani ɗan adam zai iya rayuwa a wajen, lallai bashi kaɗai bane a wajen ba.

Saboda haka abu na farko daya fara faɗo masa a rai shi ne  takobinsa, wadda a iya tunaninsa ita kaɗaice abinda yake gani ya tuno da mahaifiyarsa.

Cikin sauri ya juya ɓarin kafaɗarsa ta hagu inda ya saƙale takobin tasa, amma babu ita babu alamarta.

Nan take ya miƙe tsaye ya kuma fara dubu-dube.

Amma idanun nasa basu gane masa komai ba, banda filin turɓaya kurum dake gabansa iya hangensa.

A wannan lokaci ya juya bayansa, inda bisa mamaki yai arba da wani abu, wanda gaba ɗaya acikin wajen nan shi kaɗai abinda ya gani tun bayan farkawarsa.

Wannan abu ba komai bane illa wani ƙaton allo mai rubutu a gabansa.

Ba komai bane a jiki illa suna ye masu yawan gaske, kowanne da lamba a jikinsa da kuma shekara.

Sunayen sunyi wa Armad wahala, saboda bai saba jin irinsu ba a ƙasa ta uku, duk da cewa abune mara wahala ka samesu acikin littattafan daya karanta, to amma anan ɗin ma ba son su yake ba.

Saboda haka kawai sunayen da suke da lamba ɗaya a jikinsu su ya iya karanta uku daga ciki.

Inda ɗaya yaga ansa Bihanzin Djinn shekarar 1833, ɗaya kuma ansa Ikenga O. Bayajidda shekarar 1852 sai kuma ɗayan ansa Deniz Bizáya shima shekarar 1852.

Zaka iya cewa ganin shekarar 1852 shi ne abu mafi girman mamaki da Armad ya fuskanta tun bayan barin sa gida.

Badan komai ba kuwa saidan cewa yasan kamata yayi ace wannan shekara da suke ciki ta zama 1851, wato shekarar da aka gama wancan yaƙi da mahaifiyarsa ta samu wannan ciwo a ciki.

Kuma daga fitowarsa daga gida zuwa wannan lokaci kaf iyakacin lissafinsa ƴan kwanani ne kawai. Amma yanzu gashi yana ganin 1852, wanda hakan ke nuna tuni yayi shekara ɗaya da barin gida.

MEKE FARUWA? Ya tambayi kansa.

Amma idan da a haka abin ya tsaya masa da da sauƙi, to amma a lokacin ne idanunsa suka kai kan wani sunan wanda a jikinsa akasa shekarar 1853!!

Kafin kace meye wannan tuni tunane-tunane sun cika ziciyarsa, kuma a lokaci guda sama da hakaice-hakaice ɗari sun bayyana a ransa; ko kaza ko kaza. Amma duk ciki babu wanda ya bashi amsa mai ma'ana.

Yana cikin wannan hali ne sai ya fara hangen wata inuwa daga nesa, inda nan take ya fara shirya zuciyarsa cikin shirin ko ta kwana.

Ba'a daɗe ba halittar dake bada wannan inuwa ta bayyana, inda ya fara hango kanta.

Wanda hakan yasa kaɗan daga cikin tashin hankalin da yake ciki ya ragu, badan komai sai dan cewa ya gani da idonsa cewa wannan mai ƙarasowa mutun ne kamarsa.

Kuma a lokacin ya ƙara jin sanyi acikin ransa, saboda yasan cewa indai wani mutun zai iya rayuwa a wannan waje to fa shima yana da dama.

Halittar mai ƙarasowa bata ɗauki lokaci ba ta iso gareshi, inda idanunsa suka gane masa mace budurwa mai kalar fata irin tasa sak wato 'wankan tarwaɗa'.

Tana da gashi mai tsayi da yawa wanda ta tattareshi ta ɗaure.

Fuskarta na nuna alamun yarinta, tayadda Armad ya yanke shawarar baza ta wuce shekaru ashirin ba, wato dai baifi ace ta bashi shekaru huɗu ko uku ba kenan.

Amma duk da ƙarancin shekarun da fuskarta ke nunawa idanunta su na ƙunshe da alamun kafiya da saiti, wanda ke nuni cewa duk abinda wannan mace ta saka a gaba saita cimmasa.

Duk da cewa kyakkyawa ita ma ta gaske, amma Armad bashi iya bata lambar girma a kyau a wannan lokaci, badan komai ba sai dan cewa a zuciyarsa yana hangna mai suna Nostalgiya.

Tana ƙarasowa ta tsaya kimanin taku biyar kafinsa, sannan kawai ta ɗan ƙura masa ido na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta zira hannunta na dama acikin baƙin mayafin da take sanye dashi, inda ta fito da takobi sanye acikin kufe mai adon baƙi da yalo ta kuma jefawa Armad ita.

Kallo ɗaya kacal Armad yayi wa takobin ya gane cewa kufensa ne kuma takobinsa ce.

Ya miƙa hannu ya cafe, wanda a lokacin ne yaji hankalinsa ya kwanta kamar wanda aka bawa wata nutsuwa.

A lokacin ne kuma ya ƙara lura cewa kayan jikin nasa shima baƙaƙe ne, kuma sunyi kama dana wannan budurwa dake gabansa. Nan take ya haɗa ɗaya da biyu ya gane duk abinda ke faruwa.

Baiyi wata-wata ba ya sunkuyar da kai alamun girmamawa ya kuma ce mata, ''na gode sosai da kayan da kika bani da kuma kula dani da kikai tsahon wannan lokaci.''

Armad ya ɗago kai ya kalle ta yaga babu alamun komai a fuskarta tamkar ma bata ji mai yace ba.

Saboda haka kawai ya yanke shawara, ya juya da niyyar tafiya, to amma a wannan lokaci ne yaji tayi magana, ''Ya sunanka, kuma ya akai kazo nan wajen?''

Muryar tata bata ɗauke da taushi ba kuma ta ɗauke da kaushi, tamkar kwata-kwata bata damu da amsar waɗannan tambayoyi da tayi ba.

Armad ya ci birki, inda ya juya ya fuskance ta idonsa cike da son ya gane meke faruwa a wajen.

Ya ɗanyi shiru yana kai-komo da abinda ya kamata ya faɗa, inda a lokacin ya gane cewa lallai bashi da wani zaɓi da yafi yayi mata bayanin kansa.

Tunda ko ba komai, baya jin zuciyarsa na ɗarsa masa wata mugunta a tattare da wannan mace, sannan abisa mamaki yaji kurum zuciyarsa ta fara nutsuwa da ita, wato yana ji kamar ba cutar dashi tazo ba.

Kuma mafi muhimmanci ma idan ya rabu da ita ya tafi a yaushe ne yake tunani a irin wannan waje zai ƙara ganin wani ɗan adam ɗin, sannan gashi yana jin yunwa da ƙishi.

Nan take ya tako ya nufeta, bayanda ya kusa isa, sai ya tsaya kawai ya nemi waje ya zauna ya kuma ɗaga kai ya kalleta yana yi mata bishara data zauna ita ma.

Ta ɗau kimanin minti ɗaya kawai tana kallonsa, kafin daga bisani ta zauna ta zauna nesa dashi.

Bayan ta zauna sai ta juya kai ta kalleshi tana kuma bashi alamar cewa ya fara jawabi.

Abu na farko daya fara tambaya cikin mamaki shi ne, "kafin na gaya miki yadda nazo nan, da... ALLAH... ko zaki gayamin a wacce shekara muke yanzu haka???"

Cikin mamaki ta dube shi gefe da gefe, sannan a hasale ta amsa masa da cewa, "kanka ya bugu ne? A ƙarshen shekarar 1853 mana muke!"

Nan take Armad yai zumbur ya miƙe, baki a hangame, ido a kwale. Cikin ƙinƙina ya ce, "1853?????

"Kin tabbata! Saboda ƴan watanni kaɗan da suka wuce na na baro gida, kuma ina da tabbas a shekarar 1851, shekarar da aka gama wancan yaƙin na fito!!!"

Kallonsa kawai tai, tana ƙoƙarin tabbatar wa da kanta cewa ba'a cikin hayyacinsa yake ba, amma duk yadda tayi sai taga cewa idonsa yana nuna gaskiya yake faɗa.

Saboda haka kawai tai shiru tana tunanin mai ya kamata tayi dashi. Tana cikin wannan tunani ne taji muryar Armad, wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye, "dan ALLAH ko zaki bani aron Ayrid guda ɗaya, ina son na tura saƙo gida!"

Kallonsa kawai tayi, irin kallon mai nuna rashin yadda, sannan ta ɗauke kai.

Yana ganin haka ya fuskanci yana da buƙatar yayi mata bayanin kansa dalla-dalla da kuma yadda yazo wannan waje indai yana buƙatar haɗin kai daga gareta.

Saboda haka nan take ya kwashe dukkanin abinda ya faru dashi ya gaya mata. Sannan ya ƙara jaddada mata buƙatar Ayrid ɗin da yake.

Bayan tsahon lokaci tana kallonsa, sai ta zira hannu cikin mayafinta ta ɗakko kwayar Ayrid guda ɗaya ta cilla masa.

Nan take Armad ya fasa ɗan yatsansa guda na dama ya ɗisa jini akai, sannan ya miƙa hannu ya ɗan gitsiri wannan jan kyalle dake ɗaure akansa, kafin daga bisani ya haƙa ƙasa a wajen ya binne.

Suna zaune babu wanda ya ce ƙala a cikinsu, shi Armad yana jiran amsa daga kakansa wanda dama shi yai niyyar yana nutsuwa ya iso ƙasa ta huɗu, ya turawa saƙo cewa yaje lafiya.

Sannan kuma ya tambayi lafiyar mahaifiyarsa.

Amma bayanda ya farka sai ya tsinci kansa a tare da waɗancan mutanen, kuma yanzu gashi ya faɗo nan wajen. Duk a tunaninsa baifi ƴan watanni ba, amma gashi ana ce masa shekara biyu ta wuce.

Ita wannan budurwa tana nata tunane-tunanen.

Ba jimawa ƙasar dake wajen ta fara motsi, inda kan kace meye wannan ƴar shuka ta bayyana, wadda a samanta kwayar Ayrid ce guda ɗaya.

Armad ya miƙa hannu ya tsinka. Yana riƙewa a hannunsa, ta juye izuwa takarda.

A jiki an rubuta; ; ;
***
kai jika Armad!

Ina ta turo maka saƙonni baka bada amsa, to amma tunda na jika yanzu nasan komai lafiya.

Naji matakin daka ɗauka na neman Tirifil-fakta, kuma kai sani ina alfahari dakai.

Da fatan acikin wannan shekaru biyu da suka wuce kana gabda nemoshi, inma baka riga ka nemoshi ba.

Mahaifiyar ka ta fara samun sauƙi tuntuni, kuma idan bakai sauri ba idan ta tashi ban san mai zan gaya mata, taƙi biyoka ba!

Kayi ka gama ka dawo, ina jira kazo naga ci gaban Izzar daka samu!

Ka kula da ma'abota Ururu!!

Sune suka sawa mahaifiyarka wannan cuta!

Zanso idan na ƙara ganin saƙon ka naga ka cika wannan aiki!!!
***

Armad na gama karanta wannan saƙo yai wata mummunar ajiyar zuciya, inda wani mugun gumi ya keto masa, bai san ya fara jin jiri ba, ba shiri ya nemi waje ya zauna.

Tsahon lokaci baice komai ba, kawai kallon sama yake, yama rasa mai zaiyi tunani!!
***
To fa! Armad yayi shekaru biyu, amma bai san a ina ba! Domin bama ya tuno wucewarsu ko kaɗan acikin ransa!! Mai kuke tunani ya faru ne??

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...