Skip to main content

BABI NA BIYAR : Koriyar Duniya

A babi na hudu mun tsaya a inda Armad ya tsinci kansa yana faɗawa cikin rami ba tare da shiri ba, yanzu zamu ci gaba.
***
Hankalin Armad tuni ya gushe, a lokacinda yake cikin halin ruftawa wannan waje, zuciyarsa cike da jimamin ina zai faɗa, kuma a wanne hali zai faɗa.

Abu na gaba da Armad ya gani bayan hankalinsa ya dawo jikinsa shi ne tsintar kansa da yayi a wata duniya ta musamman.

Tun kafin idanunsa su ƙarasa buɗewa wani haske wanda gaba ɗayansa kore ne babu ko garwaye, ya fara yi masa sallama ta hanyar haske masa ido. Kafin daga bisani ya ƙarasa buɗe idanunsa ya kuma ga zahirin wannan duniya daya tsinci kansa aciki.

Bayan buɗe idon nasa ne ya kuma ɗaga kansa sama, inda ya fahimci cewa dukkan abinda ke wannan wajen kore ne shar. Kama daga kan sararin samaniyar wannan duniya har zuwa kan tantagargar doron ƙasar. Ba shiri ya durƙusa gami da dantsi ƙasar dake kusa dashi domin ya ƙara ganewa idonsa launinta.

Wani abu daya ƙara bashi mamaki shi ke babu wani alamun rauni a jikinsa, duk da kuwa cewar bai san yadda akai yazo wajen ba, amma kuma abu na ƙarshe da yake tunawa shi ne faɗawa cikin wannan rami wanda a iya lissafinsa, a tayi masa da kyau ya sha da karaya biyu zuwa biyar.

Yana tsaye cikin mamaki da talazzuzin yanayin daya samu kansa a wannan duniya sai kawai jin alamun motsi yai a samansa.

Ai kuwa yana ɗaga kai yai arba da wani ƙatoton shaho kore shar, wanda yakai kimanin ƙafa uku a kwance, yana ƙoƙarin kawo masa wata muguwar wafta da niyyar tsinke masa kai.

Bakin shahon yana da tsayi da tsini matuƙa, sannan kuma ga kyalli da sheƙi da yake yi. Daga can ƙarshen bakin kuma akwai wani koren abu mai kama da yawu da yake ɗisa daga cikin bakin shahon.

Wani abun mamaki shi ne, wannan koren abu, babu abinda yake sai tiriri, tamkar daga cikin wuta yake futowa!!

Ba shiri Armad yai sauri ya sunkuya ƙasa, lamarinda yasa ya kubuta da ɗan taƙi kaɗan daga tsinin bakin wannan shaho.

Sai dai kuma kafin Armad ya ƙarasa ɗagowa tuni wannan shaho ya juyo a fusace, tamkar wanda aka hana abincin daya halatta a gareshi ko kuma wanda aka hana haƙƙinsa, ya kuma ƙara nufo Armad ta baya.

Kan kace meye wannan tuni yayi ƙasa-ƙasa ya kuma ɗaura azamar ƙara kawowa Armad wata suka mai cike da mugun nufi irin wanda shi kaɗai zai iya karayar da rundunar abokin gaba hamsin da ɗoriya.

Ba shiri Armad ya wartsake daga halin da yake ciki, gami da miƙa hannu ya kuma zare takobinsa.

Wata muguwar ƙara ce ta tashi, irin wadda ke tashi idan ƙarfe ya haɗu da ƙarfe, a lokacinda tsinin bakin wannan shaho ya haɗu da kaifin takobin Armad.

Wani abun mamaki daya firgita Armad shi ne bayan haɗuwar takobinsa da bakin wannan shaho, kawai sai allankatafur suka ƙi rabuwa da juna tamkar ansa wani abu an ɗaure su a tare; a dai-dai lokacin Armad fincikar takobinsa kawai yake amma ina, ko motsi bata yi.

Shi kuwa wannan shaho ya caka bakinsa akai shima baya ko motsi. Lamarinda ya ƙara bawa Armad mamaki.

Abu na gaba da Armad yai shi ne dunƙule hannunsa na dama, inda ya dubi wuyan wannan shaho, cikin zafin nama ya kai masa wani mugun duka ya kuma ci sa'a ya sameshi.

Amma bisa mamaki shahon ko gezau baiyi ba da niyyar kaucewa hannun na Armad, haka ya barshi yaje ya haɗu da wuyan nasa, lamarinda yasa wata ƙara ta tashi sama mai kama da ana dukan dutse.

Idanunsa cike da mamaki Armad ya janye hannunsa cikin mamaki da ɗimuwa, hannunsa yana karkarwa kamar ba'a jikinsa yake ba.

Ba komai bane ya jawo haka ba illa abinda Armad yaji bayanda ya daki wuyan wannan shaho. Wanda duk da cewa gashi a ido wuya ne mai ɗauke da nama da jini, amma a zahiri taurinsa yafi na jan dutse.

To amma da ace lamuran da Armad yake fuskanta anan suka tsaya, toda da sauƙi matuƙa, to amma a dai-dai wannan lokaci ne hannunsa dake riƙe da takobinsa ya fara fuskantar wani abu.

Wannan kuwa ba wani abu bane illa ji da yayi takobinsa ta fara rage nauyi, lamarinda yasa ya ƙurawa takobin tasa ido domin tabbatarda ko abinda yake ji a hannunsa gaskiya ne!

Sai dai kuma amma a lokacin ne akan idonsa ya fara ganin takobin tasa ta fara rage tsayi da faɗi.

Duk da wannan abubuwa da suke faruwa, mamakin Armad bai kai ƙololuwa ba, saida idonsa yakai kan wannan shaho ya kuma ganshi acikin halin limshe ido, bakinsa a kafe ajikin ƙarfen takobin.

Nan take Armad ya lissafa abubuwan dasuke faruwa ya kuma gano cewa lallai wannan shaho mayarda takobinsa abinci yai kurum, abinda ke faruwa kuwa shi ne shahon yana zuƙe ƙarfen takobin ta Armad ne kawai ta wata hanya da Armad bai taɓa jinta koda a karance-karancen littattafan tarihi da yaƙi da yai a iyakacin tsahon rayuwarsa.

Mamaki da ɗimuwa su ne abubuwan da suka cika masa zuciya a wannan lokaci.

Sai dai kuma a lokacin ne ya fuskanci cewa wannan ba lokacin ya tsaya yana mamaki bane, kasancewar wani mummunan ƙaraji da yaji mai tsoratarwa ta bayansa, wanda yasa nan take Armad ya juya izuwa ɓangaren da yaji wannan ƙaraji.

Sannan kuma a lokaci guda wani abu ne yake faruwa wanda Armad bai sani ba, wannan kuwa ba wani abu bane illa haske da wannan takarda da wannan dattijo mai suna HanDiyúza ya bashi, take tayi acikin aljihun wandonsa!

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...