Tun daga yadda Abul'Babara yai tambayar kasan cewa akwai wani abu a ransa, wanda hakan yasa Armad ya fuskanci lallai ƙarya ba zata fitar dashi daga wannan tarko ba, saboda haka nan take ya amsa da cewa, "na biyun; Armad Wilbafos!"
Tsahon lokaci idanun Abul Babara na kansa, kuma kallo ɗaya zakai masa kasan ransa a ɓace.
Babu abinda zuciyar Armad keyi sai bugawa, saboda yasan ya riga yayi kuskure, kuma Abul Babara na da dukkan haƙƙin dazai ƙi duba babar tasa, kuma a ƙarshe Armad bazai iya yafewa kansa ba, idan ta rasu ta dalilin wannan. Saboda haka kan kace meye wannan gumi ya gama jiƙa masa riga.
Sai dai kuma bisa mamaki abu na gaba daya biyo baya daga ɓangaren AbulBabara shi ne murmushi, inda kwata-kwata baima koma takan wancan zance, tamkar ma bai faru ba, ya ɗora da cewa," yanzu saura sharaɗi na biyu.
"Shi wannan sharaɗi ba tambaya bace irin na farko ba, umarni ne.
"Ina so kayi tafiya aban ƙasa, ka nemo min wani mutum da akewa laƙabi da Tirifil-fakta!"
"Indai ka nemo wannan mutun, ni kuma nai maka alƙawarin komai daren daɗewa zaka dawo ka sami mahaifiyarka, a warke, nayi mata magani!"
Armad na gama jin wannan batu ya dubi Abul Babara cikin tsananin mamaki, gami da maimaita wannan suna 'Tirifil-fakta!!'
Babban abinda ya jefa Armad cikin wannan mamaki shi ne, da daɗewa mahaifiyarsa tasha gaya masa cewa da ita da mutanenta su na neman wani mutun ne mai su na Tirifil-fakta.
Kuma ta gaya masa cewa an haramta zancen wannan mutun akan doron ƙasa ta uku, shi yasa ba'a sanshi ba kwata-kwata a garin nasu ba, amma kamar yadda ta labarta masa cewa amsar da zata kai ga cimma wannan mutun, bata kan ita wannan ƙasa, saboda haka ta gaya masa wannan shi ne babban dalili daya zama wajibi akanta da tayi tafiya bisa doron ƙasa domin neman wannan mutun.
Wata biyu da suka gabata, sukai maganar ƙarshe akan wannan mutun da mahaifiyar tasa, gab da zata fita wannan yaƙi.
Inda ta gaya masa cewa su na gab da cimma burinsu, kuma mataki na ƙarshe ya ta'allaƙa ne kacokam da wannan yaƙi, saboda haka ya wajaba da taje ta bada gudummuwarta.
Har kullum Armad ya daɗe yana so ta ringa tafiya dashi a duk lokacinda zatai irin waɗannan tafiye-tafiye, amma a kodayaushe sai tace masa sai ya ƙara girma, kuma saiya gama karatunsa.
Yana daga cikin maganganun da Armad yafi tunawa na babar tasa, inda take gaya masa cewa, "kayi haƙuri bazan iya tafiya dakai ba, idan banyi nasara ba wajan nemo wannan mutun a wannan karan ba, to ya rage naka ka ɗora daga inda na tsaya."
Irin wannan maganganu, dama sauransu, da Armad ya saba ji daga mahaifiyar tasa, dama kuma yadda yaga ta zuba dukkan ƙarfinta akan neman wannan mutum, shi ne ya sa Armad ya daɗe yana ji a ransa kamar dalilin rayuwarsa ma nada alaƙa da nemo wannan mutun, koma wane ne kuma koma a ina yake.
Saboda haka tun baikai haka ba ya ƙudure a zuciyarsa yana gama lodin littattafan da aka wajabta masa, zai ƙara himma wajen karɓar horo, domin shima ya fara taimaka mata cikin wannan aniya ta ta.
Hakan nema yasa yana jin sunan wannan mutum a bakin AbulBabara ya cika da mamaki.
Armad na cikin waɗannan tunane-tunane ne, ko yanke shawara baiyi ba, yaji muryar Babara ta katse shi, "Armad Wilbafos, kana ganin zaka iya?"
To amma abinda Abul Babara bai sani ba shi ne, koma babu wannan sharaɗi nasa, Armad ya daɗe da ƙudure niyyar zuwa nemo wannan mutumi kawai yarjewar mahaifiyarsa yake jira.
Saboda haka a wajen Armad, kamar faɗuwa ce tazo dai-dai da zama.
To amma wani hanzari ba gudu ba, wanda ya hana Armad saurin amsawa shi ne, hankalinsa yaƙi kwanciya akan ya tafi ya bar mahaifiyarsa a wajen wannan mutum.
Bai ɗauki lokaci ba ya yanke shawara, inda ya fara magana da cewa, "na yarda, amma bis sharaɗi guda ɗaya, kaka na shi ne zaiyi jinyar baba ta, kai kuma can zaka ringa zuwa kana duba ta, idan ka amince ni kuma nayi alƙawarin daga nan ko gida bazan koma ba, zan bazama neman wannan mutun, idan kuma baka amince ba to....''
Babara yai murmushi kawai baice komai ba, kafin daga bisani ya tafa hannunsa biyu, lamarinda yasa wata iska mai kama da guguwa ta tashi sama, wadda ta lafa bayan ƴan daƙiƙu.
Bayan lafawar wannan iska, a dai-dai inda wannan guguwar tai tsiri saiga ƙofa ta bayyana aka gabansu a inda da ba komai.
Ƙofar shuɗiya ce gaba ɗayan ta, mai matsakaicin faɗi. Saboda tsabagen shuɗinta bama kewayenta kaɗai ba, hatta gaba ɗaya muhallin da suke tsaye saida ya fara komawa shuɗi duk da kuwa akwai ragowar duhun dare a lokacin.
Bata da girma sosai, kuma idan da zaka auna da ka fuskanci cewa tsayinta dai-dai yake dana Babara, domin ko Armad bazai iya wucewa ba saiya durƙusa.
Nan take Abul Babara ya dubi Armad, sannan cikin sauri ya fara bayani, "bazan iya riƙe wannan ƙofa sama da daƙiƙa ɗari ba!
"Idan ka shiga cikinta zaka fice daga cikin wannan ƙasa zuwa wata ƙasar ba tare da ka fuskanci matsalar caje ba, musamman saboda wannan yaƙi da bai daɗe da kammala ba.
"Saboda haka ya zama wajibi kai sauri ka shiga idan har kanason tafiya!
"Zancen kula da mahaifiyarka kuwa, kamar yadda ka buƙata a wajen kakan ka zatai jinyarta ba'a nan ba.
"Sannan kuma zancen alƙawarin mu, yana nan; Idan ka nemo Tirifil-fakta nai mata magani, idan kuma baka nemo ba, to...."
Tun kafin ya rufe baki, ƙofar ta fara yin dishi-dishi, alamun ɓacewa.
Sai dai kuma shima Armad a lokacin ne ya fara tafiya da sauri domin shiga cikin ƙofar, wadda yana kusa zuwa ta buɗe.
Amma har ya ɗaga ƙafa zai shiga, sai ya juyo da sauri, lamarinda yasa AbulBabara yin ajiyar zuciyar da buɗe baki da niyyar magana, amma kan ya ce wani abu ya fuskanci abinda Armad yake nufin yi.
Wannan kuwa ba wani abu bane illa yin sallama da mahaifiyar sa, inda ya durkusa, idanu cike da tausayi.
Bakinsa ne kawai yake motsi amma sauti baya fita, lamarinda yasa hatta Babara dake kusa dashi baiji mai yace ba.
Can bayan kimanin daƙiƙa goma ya tashi tsaye, gami da miƙa hannu ya ciro takobin dake ɗaure a bayanta, ya rataya, sannan ya miƙe cikin sauri ya nufi cikin wannan shuɗiyar ƙofa da sauran ƙiris ta ɓace gaba ɗaya.
Yana gabda shiga yaji murya a kunnuwansa tana ce masa, "ka kula da ma'abota Ururu!"
Cikin sauri fuska cike da mamaki ya waiwaya dama da hagu sama da ƙasa amma baiga mai maganar ba, kuma ya tabbata ba maganar AbulBabara bace, sannan kuma baya tuna lokacin daya taɓa jin wannan magana a iya tsahon rayuwarsa.
Nan take ya tamabayi kansa koma kawai kunnensa ne, amma kuma kalma ɗaya daya kasa cirewa daga zuciyarsa ita ce kalmar, "Ururu", lallai yasan yaji wannan kalma, duk da bai taɓa jinta ba, kuma bai san mai take nufi ba!
Amma a lokacin ne Abul Babara yai masa tsawa gami da nuni da cewa ƙofar ta kusa rufewa, saboda hakan nema nan take Armad ya manta da wannan magana daya ji ya faɗa cikin ƙofar.
Abu na farko da yai wa Armad sallama yana shiga cikin ƙofar shi ne tsananin duhu, amma ko kaɗan hakan baisa ya canja shawara ba, duk da kuwa yasan cewa Abul Babara ba abin yarda bane, amma kuma yasan bashi da wani zaɓi.
Hakan ne yasa duk da haka zuciyarsa gaya masa take kawai ya ƙarasa, saboda haka baiko waiwayo ba, ya danna kai ciki, inda ƙofar ta rufe, kafin daga bisani ta ɓace gaba ɗaya.
Koda rufewarta sai Armad yaji wani irin yanayi, kamar ana cillashi sama, nan take kansa ya fara juyawa, kuma kan kace meye wannan ganinsa ya zama dishi-dishi, inda jiri ya ɗebeshi ya faɗi ƙas.
Bai san iyakacin tsahon lokacin da yai a cikin wannan yanayi ba kafin daga bisani ganinsa ya dawo dai-dai ba.
Kawai abu daya ɗazai iya tunawa bayan ganinsa ya dawo dai-dai shi ne ganinsa da yayi a wani fili wanda babu komai a cikinsa sai wasu fararen bishiyu masu kama da na kuka wajan girma, saidai kuma sun banbanta ta yadda ko ganye ɗay babu a jikinsu, illa kawai wani abu mai kama da ƙaya.
Armad ya duba gaba da baya amma babu wani mahaluƙi mutun ko aljan a wurin, kai ko gida babu, sai kurum shi kaɗai a tsaye kwallin kwal.
Sai dai kuma bai daɗe acikin wannan yanayi ba ya fara jin takun ɗan adam yana gabato shi daga nesa, ɓangaren kudu maso gabas.
***
Kalmar 'Izza' acikin wannan littafi tana ɗaukar ma'anar abu daban ne, da yadda aka saba amfani da ita a harshen hausa.
Kamar yadda akai bayani cewa shekarun da mutane gama gari zasu iya yi a duniya da kuma wanda Sadaukai suke yi sun banbanta matuƙa acikin wannan labari.
Misali; mafi yawancin mutane gama gari sukanyi shekaru sittin zuwa saba'in ne, amma shekarun da Sadauki zai iya yi sun ninninka haka, kuma irin wannan shekaru na musamman su ake kira da suna 'Izza!'
A taƙaice dai wannan kalma tana ɗaukar ma'anar adadin shekarun da sadauki zai iya yi a duniya!
Iyakacin yawan shekarun da Sadauki zai iya yi a duniya kan ya mutu, iyakacin yawan Izzarsa, kuma hakan kamar wani mizani ne na gwada ƙarfi da buwaya tsakanin sadaukai.
***
Armad na tsaye cak, baiko motsa daga inda yake ba. Can bayan wasu daƙiƙu saiya fara hangar inuwar wani mutun tana dososhi, saboda haka nan take ya miƙa hannunsa kan takobinsa dake rataye a kafaɗarsa ta hagu.
Daƙiƙa biyar, daƙiƙa goma, daƙiƙa sha biyar...'aaarrgh', mamaki ya fara shiga zuciyar Armad saboda yanzu daƙiƙa ashirin wannan inuwa ƙaruwa kawai take amma Armad baiga mai ita ba, lamarinda yasa ya fara tunanin cewa idan dai har inuwa tana da wannan tsayi, to mai ita fa, ya yake!
To amma baima gama tunani ba yaga wani dattijo ya bayyana daga bayan wannan inuwa, rataye da takobin jan ƙarfe.
Babban abin mamakin shi ne, duk da mugun tsayin wancan inuwa da Armad ya gani amma wannan mutun va wani mugun dogo bane, hasalima ƙafa huɗu da rabi ne, wato dai da kaɗan yafi Armad tsayi.
Kuma sannan gashinan a zahiri wannan inuwa tasa ce!
Kallo ɗaya Armad yai masa yaji zuciyarsa tana neman ficewa daga ƙirjinsa saboda tsananin bugawa, badan komai ba sai dan kasa iya karanta Izzar wannan mutun da yayi!
Armad ya daɗe da koyar yadda ake iya karanta Izzar sadauki a gane nawa ce, kuma yana da cikakkiyar masaniyar cewa indai mutun bai ninninka Izzar ka ba, to zaka iya karanta Izzarsa.
Sabida haka yana ganin ya kasa karanta Izzar wannan mutun ya gane hakan mai yake nufi.
Armad na cikin wannan hali na mamaki yaji murya acikin kansa tana cewa, "idan kana so ka wuce wannan waje to lallai saika ci nasara akaina tukun!"
Murya ce kawai, amma saboda ƙarfin Izzar dake ƙunshe acikinta saida Armad yaji tamkar an ɗora masa nauyin dukkan ƙauyensu akansa. Domin tuni ya fara haɗa gumi, data ci gaba da magana da lallai sai ya faɗi ƙas, saboda kurum nauyin da yaji tana ɗauke dashi.
Wannan murya bata kowa bace illa wannan mutun dake tsaye a gaban Armad fuska babu alamun komai aciki tamkar wanda ke magana da dutse. Yaci gaba da cewa, "a duk tsahon ɗaruruwan shekarun danai a wannan duniya, kaine mafi ƙaranci Izza dana taɓa gani!"
Wannan ba wani abin mamaki bane, saboda a wannan lokaci Izzar Armad hamsin ce kawai da ɗaya!
Dattijon yaci gaba da cewa, "kayi sani cewa ƙa'idar wannan hanya ita ce, kodai ka samu nasara akaina ka wuce ko kuma ka rasa ranka anan, duk kai ya shafa!
"Sai dai kuma, ka godewa ALLAH, shekara da shekaru na daɗe banga wani ɗan adam ba, sabida haka zanso muɗan daɗe muna fafatawa. Hakan nema yasa zanyi maka taimakon rage Izza ta zuwa ɗari kawai a wannan fafatawa da zamu yi."
Jin wannan magana ƙara firgita Armad yai kawai, maimakon ya kwantar masa da hankali, badan komai ba saboda yana da cikakkiyar masaniyar irin nisan dake tsakanin Izzarsa wato hamsin da ɗaya da kuma Izzar mai mataki na ɗari.
Musamman idan ya tuna irin wahalar da mutun yake sha, kafin ya haura daga casa'in da tara zuwa ɗari. Sannan kuma duk wannan ba wani abu bane idan aka kwakwanta da ainihin girman Izzar wannan mutun dake gabansa.
Yana cikin wannan tunani ne ya ƙara jin muryar wannan dattijjo a kunnensa, "duk sanda ka shirya zaka iya farawa!"
To amma da yake Armad mutun ne mai saurin lissafi musamman a yanayi na buƙata, nan take ya yanke shawarar mai ya kamata ya aiwatar.
***
Aljanu kala-kala ne, akwai daga cikinsu masu aman wuta, akwai masu aman ƙanƙara, wasu kuma iska, wasu turɓaya wasu ƙarfe, wasu tsawa, wasu ruwa......
Kai duk wani abu da zaka iya tunani akwai aljanin da yake iya sarrafashi!!!
To kamar dai yadda aka sani, kusan kowanne ɗan adam yana da aljaninsa; wasu ana haihuwarsu suke yin hannun riga da nasu aljanin, wasu kuma basa rabuwa da nasu, wasu suna bautar dasu, wasu kuma saidai aljanun su bautar dasu.
To waɗanda daga cikin mutane suka samu damar bautar da irin waɗannan aljanu, sune wanda zaka ga suna iya amfani da irin waɗancan abubuwa kamar su wuta, ƙanƙara, iska, tsawa, ƙarfe, ruwa, turɓaya,...kai dadai sauransu!
Kuma suna hakan ne ta hanyar arar ƙarfin waɗannan aljanu nasu!
To badan komai ba saboda horo da Armad ya samu daga wajen kakansa, shima ya samu ya bautar da nasa aljanin, wanda kuma wannan aljani nasa 'tsawa' yake iya sarrafawa!
Lamarinda yasa shima Armad ya zamanto yana iya sarrafa tsawa a duk sanda yaso!!
***
Nan take Armad ya zare takobinsa, lamarinda yasa tsawa da walƙiya ta fara rawa akan takobin tana fitarda wani sauti.
Abin mamaki a wannan lokaci sai shima wannan dattijo ya zare takobinsa, inda bisa mamaki wata irin wuta ta fara tashi daga jikin takobin, lamarinda yake nunawa a fili cewa shima wannan dattijo ya bautarda aljaninsa, kuma aljanin nasa wuta take sarrafawa!!!
Ba tare da tsayawa ɓata lokaci, Armad yayi wo kan wannan dattijo gadan-gadan da niyyar aiwatar da shawarar daya yanke.
Babu abinda ke tashi daga jikin takobinsa illa walƙiya da alamun tsawa, acikin udanunsa babu tsoro ko kaɗan.
Jan kyallen dake ɗaure a gaban goshinsa kawai kaɗawa yake akan iska.
Hannayensa a buɗe; na dama a dunƙule na hagu kuma rike da takobinsa. Duk inda ya wuce sai kaga ita kanta iskar wajen ta fara tarwatsewa acikin wannan walƙiya.
Daga nesa idan ka hangi Armad cikin farar riga, baƙin wando, riƙe da takobi mai walƙiya, saika rantse wani ɗan saƙon mutuwa ne.

Comments
Post a Comment