Babi na 53: Baƙar guguwa
___
A kowanne yanki na Ikwatora dake kowacce ɗaya daga cikin ƙasashe bakwai na duniya, akwai wani tsibiri wanda shi ne waje da ma'abota wannan yankin suke gani a matsayin tsarkakakken waje. Wannan tsibiri shi ake cewa Tsibirin-guguwa.
A duk bayan kowacce shekara sittin wata guguwa mai ƙarfin gaske na tasowa daga Tsibiri. Wannan guguwa ita ake kira da Baƙar guguwa. Duk lokacin da aka fara ta akanyi watanni kamar biyar ana yinta, kuma anyi ittafaƙi wannan iska tana da ƙarfin da zata iya tarwatsa duwatsu da ƙarafa da al'amudai komai girmansu.
Amma acikin wannan guguwa ake fitarda shugaban da zaiyi mulki a kowanne shashi na ikwatora a shekaru sittin masu zuwa. Hanyar kuwa mai sauƙi ce, duk wanda yake so ya tsaya takarar wannan kujera saiya fito ya kuma tsaya a tsakiyar wannan guguwa har tsahon wannan watanni biyar, indai aka kammala iskar duk wanda yai ragowa shi ne zai zama shugaba a wannan sashi na Ikwatora har tsahon wasu shekaru sittin masu zuwa.
To amma mulki dai bashi kaɗai ne abinda ake muradi ba a shiga cikin wannan guguwa ba. Babban abinda ake muradi shi ne sadakar baiwa da ake acikin wannan iska. Babu wata irin baiwa a duniya ko kuma wani sihiri ko kuma wata fasaha wadda baza a iya tsinta ba acikin wannan iska ba. Sabida haka nema wasu sukan siyar da ransu su shiga duk da kuwa sunsan cewa ƙarfin Izzarsu bai kaiba, amma saboda kwaɗayin wannan baiwa da ake samu.
To wannan dai shi ne kaɗan daga cikin Tarihin wannan sashi na Ikwatora inda a dai-dai wannan lokaci Nusi take kwance rai a hannun ALLAH tana jira Dordor mai kai biyu yayi layya da namanta.
Sai dai kuma kash, lallai naman Nusi yafi ƙarfin wannan Dordor, domin kuwa a dai-dai wannan lokaci ne aka fara busa wata sarewa wadda duk wanda ya rayu a sashin Ikwatora yasanta. Sarewar da take nuni da cewa lokaci yayi. Wato shekaru sittin sun kewayo kenan.
Ai kuwa wannan busa tana isa kunnen wannan Dordor yai tsalle gami da cilli da wuƙar dake hannunsa, sannan ya taka a guje. Bawai shi kaɗai bama, duk wani Dordor dake wajen babu abinda yake face gudu izuwa maɓoya. Tunda dama a wannan lokaci tuni lissafi ya cika, kuma a kowanne lokaci ana jira ne kawai aga baiyanar wannan guguwa. Hakan nema yasa a lokacinda Nusi ta bayyana ta iske manyan Dordor suna tsaye cirko-cirko a wannan waje.
Ba jimawa da fara wannan busa sarkin dake mulki a wannan lokaci wanda ya kasance Dordor ne mai kai tara ya bayyana sanye cikin kayan yaƙi. Kowanne ɗaya daga cikin kayikansa tara yasha kwalliya ta kayan yaƙi. Lallai kana ganinsa kasan ya shirya saiya koma kan wannan mulki. Izzaraa kaɗai shekaru dubu bakwai da tamanin ce. Sannan kuma fatar jikinsa da komai na jikinsa Ja ne.
Sai dai kuma amma bawai shi kaɗai bane, akwai sauran zaratan tsofaffin Dordor da mutane ma'abota Izza wanda suma suke neman wannan muƙami da kuma baiwa da za'a raba a cikin wannan baƙar guguwa.
Babu wanda yake cikin filin nan wanda Izzarsa bata kai dubu biyar ba acikinsu, sannan kuma babu wanda baiyi shekaru samada da hamsin yana shirin wannan rana ba sai mutun ɗaya. Wato Nusi kenan.
Ba jimawa gari yai duhu, ko tafin hannu ba'a gani, sannan kuma daga bisani Baƙar guguwa ta fara sauka. Sadaukai suka fara fitowa da shirye-shiryensu da suka tanada.
_______
Babu wanda yasan taƙamaimai maike faruwa acikin wannan baƙar guguwa, domin a duk bayan shekaru sittin mutun ɗaya ne kaɗai yake samun nasara, shi kuma tarihi yazo cewa indai ya bayyana abubuwan da suka faru aciki to duk wata baiwa daya samu zai nemeta ya rasa.
Hakan yasa sai dai kawai ka samu shaɗi faɗi, amma taƙamaimai babu wanda yasan maike faruwa.
To haka dai wannan iska taci gaba da wanzuwa tsahon lokaci, wata ɗai-ɗai har wata biyar. Sannan daga bisani ta fara lafawa. Inda alƙalan kowanne yanki suka fara fitowa domin suga wane ne sabon sarkinsu.
Saida aka ɗauki wasu kwananki ukun cir, sannan komai ya lafa gari yai haske. Alƙalai suka gabato cikin filin da aka gudanar da wannan gasa. Amma bisa mamaki maimakon su tararda sarki sai suka tararda da sarauniya.
Wata mace ce mai kyawun sura baƙar fata. Tsaye take riƙe da kambun nasara wanda duk wanda yaci nasara yake samu. Babu alamun ciwo ko rauni a tattare da ita. Kana ganinta kasan ta cika jaruma irin ta mutanen farko. Idanunta suna fitarda farin hasken mai ɗauke da Izza abar girmamawa. Abin aljabi wata ƴar ƙaramar tukunyar dinare ce a hannunta na dama, sannan kuma a hannunta na hagu wata ƴar ƙaramar bishiya ce mai yawan koren ganye.
Amma da dama zasu fi yadda dani idan nace babban abin mamakin shi ne wannan sarauniya ba wata bace illa Nusi.
Wannan alƙalai suna ganinta suka zube a ƙasa cikin gaisuwa da biyayya.
To wannan dai shi ne abinda ya kasance da Nusi bayan rabuwarsu da abokinta Armad wilbafos.
____
A can cikin fadar Ururu kuwa yau ankai wata biyar kenan aljani Kalkuta da aljani Netti suna azabtar da Armad duk domin Littafin takobi, amma babu labari. Tuni hankalin Arnad ya gushe yafi sau ɗari yana dawowa. Amma a kowanne lokaci sai dai aljanun su ƙara ƙarfin azabar da suke yi masa.
Tuni Armad yaci alwashin kashe wannan aljanu guda biyu da danginsu da kuma Uznu Ururu. Yayi kuma alƙawarin lallai bazai mutu ba saiya ɗau fansar abinda sukai masa. Idan kuwa a sakamakon tsare shi da sukai anan babarsa ta mutu, to lallai saiya kashe duk wani ma'aboci Ururu sannan zai huce.
Ana cikin haka ne Armad yaga watarana wannan aljanu guda biyu sun shigo wannan ɗaki. Suna zuwa suka ɗaure shi, sannan suka rufe masa fuska suka fice dashi daga cikin wannan ɗaki sannan suka ɓace sukai yamma.
***
Babi na 54: Cinikin Bayi
_______
Aljani Kalkútu da aljani Netti na keta hazo suna tattauna al'amuran da suka shafi wannan yaro mai suna Armad da suke azabtarwa.
Aljani Netti dai shi yake magana a wannan lokaci, "Babu abinda ba muyiwa wannan yaro ba amma littafin takobi yaƙi fitowa. Yau wata biyar kenan, indai abu sunansa azaba a duniya to munyi masa shi, amma babu labari. Ni ina ganin shawarar da shugaba Uznu ya bayar tayi dai-dai amma kai naga hankalinka bai kwanta ba."
Kalkutu yai kyaran murya gami da kallon Armad wanda ke ɗaure a bayansa ya ce, "Eh.... Haka ne, amma kana ganin siyar dashi a matsayin bawa shi ne zaisa Littafin-takobi ya fito. Kada ka manta da irin azabar da muka gana masa. Ai ina ganin azabar da mukai masa tafi azabar siyarwa a matsayin bawa."
Netti ya gurgiza kai tare da cewa, "Eh da wannan dan wannan, amma koma dai mene ne yadda aka umarce mu haka zamu yi. Zamu je mu siyar dashi a matsayin bawa ga ɗaya daga cikin sarakunan Jinzidal ɗinnan. Sannan kuma zamu ci gaba saka ido a kansa har illa mashaALLAH, har sai sanda Littafin ya fito. Wataƙila idan yaji azabar bauta Littafin ya bayyana."
Haka dai suka ci gaba da tattauna yadda suke shirin siyarda Armad a matsayin bawa.
____
Ranar sha tara ga watan goma na kowacce shekara, ita ce ranar da aka tana da domin yin gagarumin taron da za'a gabatar da dukkan bayin da aka samo ta hanyar gasar Jinzidal. Duk wani mai iko yazo ya siyi abinda yake so.
To kamar dai yadda aka sani sarakunan Jinzidal guda biyar sune suke gudanar da wannan ciniki, kuma sukan rarraba wajen gudanarda wannan gasa a kowacce shekara a tsakaninsu. Idan wannan shekara a ƙasar wannan sarkin akai, wata shekarar sai aje ƙasar wani sarkin. To a wannan shekara a ƙasar sarki Rafiya ake wannan taro.
Sarki Rafiya ɗaya ne daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal, kuma yana da iko akan miliyoyin mutane da kuma ɗaruruwan ƙasashe.
Wajen da aka tanada domin yin cinikin bayin dai wani ƙatoton ɗakin taro ne mai hawa-hawa har guda uku.
A hawa na farko akwai mutane gama gari na zaune, a hawa na biyu kuma ƙananun sarakuna ne, a hawa na uku kuwa anan sarakunan Jinzidal da muƙarrabansu suke.
Daga gaban filin akwai dandamali mai ɗan tudu. Akansa akwai wani ɗan akwati da akayi da gilashi. Ba sai ma ka tamabaƴa ba, kana gani kasan acikin akwatin gilashin ake saka wannan bayi domin gabatar dasu ga maiso.
Taro yayi taro kuma babu wanda bai hallara ba, saboda haka ba jimawa aka fara shigo da bayi kala-kala ana gabatar dasu acikin wannan gilashi ga mai buƙata.
Mai gabatarwar wani ɗan dogon mutun ne mai yawan ƙasumba. Muryarsa tuni ta dusashe, koda yake dai dama ba zaƙi ne da ita ba.
Bayan an gabatarda sama da bayi ashirin saiga wani saurayi nan an fito dashi. Yana tafiya dakyar cikin ankoki na baƙin ƙarfe. Duk jikinsa jini ne, sannan kuma rigarsa ta yayyage.
Aka shiga da wannan saurayi cikin wajen nan, sannan alƙalin ya saka masa kuɗi kimanin kuɗin Ayrid dubu sittin kacal. Wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos.
Ga dukkan alamu aljani Netti da aljani Kalkutu saida suka saka wasu ɗalasimai a jikin Armad tayadda babu wanda zai iya gane shi. Domin lallai da mamaki ace jaruminda yai suna a gasar Jinzidal ta wannan shekara amma duk taron dubunnan jama'un nan dake wajen cinikin bayin babu wanda ya gane Armad.
Sai dai kuma wani abin Alajabi ana shirin siyarda Armad ga wani attajirin birni kawai sai aka ji murya daga cikin wajen hawa na uku, wato wajen da sarakunan Jinzidal ke zaune.
Wannan murya ba wata bace illa muryar gimbiya Nostalgiya. To koma dai ya ake ciki idanun Nostalgiya sun gano wannan saurayi, kuma ga dukkan alamu babu yadda za'ai aƙi siyar mata dashi.
Ana jin muryar daga inda take duk wani mai so yai jayayya akan cinikin Armad ya fasa. Lallai babu wanda zai iya jada sarakunan Jinzidal koshi wane ne.
Armad na cikin wannan gilashi yana rantsuwa da dukkan abinda ya taɓa isa ai rantsuwa dashi cewa lallai tunda aka saka shi acikin wannan gilashi to kuwa sai yaga bayan Jinzidal. Kuma lallai ya maida shi dalilin rayuwarsa cewa sai ya kawo ƙarshen ranar da za'a ringa saka mutane acikin keji kamar wasu kaji ana siyar dasu. Armad dama can ya tsani harkar cinikin bayi, to amma bai taɓa sanin haka waɗanda ake siyarwa a matsayin bayi suke ji ba sai a wannan lokacin. Ai kuwa nan take Armad yai rantsuwa ya ƙara rantsewa cewa sai yaga bayan dukkan sarakunan Jinzidal da dukkan Ururu waɗanda suka kafa harkar cinikin bayi. Sai yaga ranar da zai kawo ƙarshen komai. Sai ya hana dukkan cinikin bayi kafin ya daina numfashi.
A wannan lokaci Armad yaji jinin jikinsa ya fara balbalin wuta yana soyuwa saboda baƙin cikin rashin ƙarfin Izzarsa. Domin babu wanda Armad yafi zarga a abubuwan dake faruwa dashi irin kansa. Armad yana zargin kansa da rashin ƙarfin Izza, da rashin tsayawa ya koyi abubuwa a lokacinda yayarsa taso ta koya masa. Amma yanzu komai yazo ƙarshe. Yana da ragowar wata ɗaya daya rage masa ya nemo Tarifil-fakta sannan kuma ya fara shirye-shiryen ruguza dukkan sarakunan Jinzidal da Ururu. A taƙaice dai a wannan rana ta sha tara ga watan goma na shekarar 1853 bayan Amri Armad yai alƙawarin yin faɗa da dukkan duniya ya kawo sabon tsari wanda bai yadda da cinikin bayi ba.
Ai kuwa abin alajabi, tamkar wani sirri acikin jinin Armad dama jira yake Armad ɗin yayi wannan rantsuwa, sai nan take ya fara juyawa. Armad yaji idanunsa suna zafi tamkar ana tsire su. Gashin jikinsa tamkar anan tsitstsige geshi saboda zafi. Bada ban bashi da ƙarfin yin ihu bama da tuni ya kwalla ƙara. Nan take ya fara zubarda gumi ta ko'ina. Idan ka ganshi fassarar kawai da zakai ita ce yana tsoron mai zaije ya tarar a wajen waɗanda suka siyeshi.
Sai dai kuma abinda shi Armad da dukkan ƴan kallo basu sani ba shi ne a wannan lokaci ƙarfin da Armad ya gada na zuri'ar Wilbafos a jininsa yake farkawa.
***
Babi na 55: Sabon Farin Wata
***
Wata ne daren sha bakwai a sararin samaniya, hasken wannan wata ya cika ko'ina a sararin samaniya da sauran ƙasashen duniyar ƙasa bakwai.
Kwatsam sai aka wayi gari hasken wannan wata ya fara dusashewa yana duhu. Idanun duk wani abu mai rai ya koma sama da kallo. Ba jimawa dukkan hasken wannan wata ya ɗauke ɗif tamkar an ɗauke wuta.
Da dama mutane sun fara tunanin zazzaɓin wata ke faruwa kuma tuni an fara shiga zulumi, malaman addinai da dama suma sun fara nasu aikin. Kwatsam sai aka ga wannan wata ya dawo ya fara yin haske, sai dai kuma hasken nasa ba irin hasken da aka saba gani bane. Wannan hasken ruwan ƙasa ne mai launin toka.
Ba jimawa mutane gama-gari suka fara shiga tashin hankali ana raɗe-raɗen cewa masifa ce zata sauka. Amma tsofaffin ma'abota Izza wanda suka ga jiya suka ga yau sun san sarai maike faruwa.
A daular sarkin Jinzidal sarki Bihanzin mai dauwamammen ciwo wani tsohon mutun ne ya farka daga cikin wani akwatin gawa, yana buɗe idonsa wata Izza wadda girmanta ya haura shekaru dubu goma ya cika wannan ɗakin.
Wannan mutun dukkan jikinsa a bushe yake, fatar jikinsa tayi ɓawo-ɓawo, bashi da maraba da gawa. Amma duk da haka sai gashi ya buɗe bakinsa yana magana, "Jinin gidan Wilbafos ya bayyana."
Yana gama magana ya koma ya rufe idonsa ya ci gaba da bacci. Wannan magana daya faɗa babu inda ta isa sai kunnen sarki Bihanzin mai dauwamammen sara.
Haka dai irin wannan mutun mai kama da gawa ya ƙara tashi a daular Denizawa dake ƙarƙashin ƙasa ya kuma ƙara faɗar irin abinda na farkon ya faɗa.
A can wani sashi kuwa na duniya dake kan wani siririn tsibiri, wani mutun ne riƙe da AL'ƘURANI mai girma a hannunsa. Idanun wannan mutun daɗe a rufe kuma babu wamda zai iya kwatanta shekarunsa a duniya. Yana buɗe idanunsa saiga irin hasken wannan wata aciki. Murmushi kawai yayi irin na mutanen Sannan ya ƙara rufe idanunsa.
Haka ire-iren wannan abubuwan al'ajabi suka ci gaba da faruwa a dukkan dauloli na faɗin duniya.
Wannan sabon hasken farin wata kuwa ruwan ƙasa ko ajikinsa, haka ya ci gaba da ƙaruwa yana game duniya.
A tsakiyar wannan ɗakin cinikin bayi kuwa wani saurayi ne acikin gilashin da ake tallan bayin nan dashi. Saurayin ya miƙe ya tsaya a tsaye yana kallon dukkan mutanen dake wajen. Duk wanda ya ganshi zai iya tunanin tsoron siyarwa ne yake damunsa.
Amma ba jimawa dukkan hasken wannan farin wata mai ruwan ƙasa da ratsin toka ya fara raguwa a dukkan sassa na duniya yana curewa a waje ɗaya.
Kan kace meye wannan dukkan hasken ya gama curewa a waje ɗaya sannan ya fara sakkowa ƙasa a hankali a hankali har saida yazo dai-dai idon wannan yaro dake cikin wannan gilashi, sannan dukkaninsa ya shige cikin idon wannan saurayi.
Wannan saurayi dai ba wani bane illa Armad Wilbafos. Nan da nan idanunsa suka fara haske suna bada launin hasken wannan wata wato ruwan ƙasa mai ratsin toka.
Komai da yake faruwa a idon kowa ya faru, saboda haka a dai-dai wannan lokaci wannan mutumi dake bada rahoton akan bayin da aka saka acikin gilashin ya fara karkarwa yana matsawa baya.
Armad ya kalli wannan ankoki dake jikinsa, nan take dukkan ankokin suka zube ƙasa, sannan dukkanin ciwukan jikinsa suka warke nan take. Sannan ya ɗaga idonsa ya kalli jikin wannan gilashi, ai kuwa hasken nan ruwan ƙasa na dukan gilas ɗin ya tarwatse.
Armad ya bayyana a waje kamar wani ɗan ƙaramin bajimin aljani. Inda ya haska idonsa akan dukkan mutanen dake cikin wannan waje, nan take da dama daga cikinsu suka fara jin karkarwa suna rawar ɗari tamkar wanda akace mutuwa ce tsaye ke kallonsu. Koda yake a wannan lokaci Armad bashi banbanci da mutuwar kanta.
Idanunsa kawai haske suke suna fitarda tsananin azabar yaƙi da ƙarfin Izza. Armad ya miƙa hannunsa sama, nan take wata taga ta buɗe akam iska inda ya miƙa hannu ya zaro takobinsa ta Wilbafos. Abin mamaki sai ga taurari guda biyar a saman takobin. Armad yai murmushin girma bayan da yaga adadin taurarin dake kan takobin kuma ya tuna wanda suke kai a lokacin da yayi faɗa Ikenga. Lallai Armad ya samu gagarumin canji a jikinsa wanda keda ban al'ajabi.
Tun daga kan hawa na farko har zuwa na uku kowa yayi shiru ba'a cewa komai. Ana haka kawai sai aka ga Armad ya ɗaga takobinsa ya nufi kan waɗannan bayin da aka riga aka siyar. Ko ba'a tambaya ba kasan nufin Armad ya kwance su ya kuma ƴantar dasu a gaban dukkan duniya. Wanda zarar Armad ya aiwatar da wannan abu, to dai-dai yake da fito na fito da dukkan ƙabilar Ururu da kuma Sarakunan Jinzidal biyar. Kuma lallai a wannan lokaci zaka ga ma'abota baƙaƙen ido sun fara sauka daga ƙasa ta farko domin kama Armad. Lallai hatta sarakunan manyan gidajen Ururu goma sai sun sauka idan Armad ya aikata wannan abu. Domin wannan shi ake kira da fito na fito da Ururu.
Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne kwatsam gimbiya Nostalgia ta bayyana a gaban Armad tana mai murmushi. Babi shiri Armad ya tsaya, kuma duk da ɓacin ran da yake ciki zuciyarsa bata fasa tunano masa wannan kyakkyawar gimbiya ba da suka haɗu a shekarun baya ba. Gimbiyar da ta ceto rayuwarsa sau adadi da dama tun bai ma fuskanci yadda yanayin duniya ke gudana ba.
Armad yana tuno sanda ta hanashi faɗawa rami da kuma hawayenta guda ɗaya daya faɗa idonsa.
Sannan kuma lallai Armad yana sane da wannan sirri daya jiyo musu acikin wannan allon tsafi, sirrin dazai rikita duniya baki ɗaya.
Armad bai manta da fasahar Izza ta musamman, wadda ake iya duba cikin kwakwalwar mutun aga mai yake tunani ba wadda wannan gimbiya mai suna Zahra wadda akewa laƙabi da Nostaljiya take da ita ba.
"N.....nostaljiya? Mai kike anan, babu ruwanki da tsakani na da wannan mutane da suke so su ringa bautar da bil adama. Idan kuma kika shiga tsakani na dasu, to lallai zan manta da duk wani abu daya taɓa faruwa a tsakaninmu na yaƙe ki, sannan kuma...."
Armad yana magana amma dole ya tsaya cak, badan komai ba sai dan saboda kwalla daya gani acikin idanun Nostaljiya bayan da tayi arba da kayan jikinsa a yayyage, kuma duk sunyi faca-faca da jini.
Armad ya buɗe baƙi zai ci gaba da magana, amma a wannan lokaci yaji hayaniyar ƴan kallon dake wajen suna cewa, "Kai.... Wai wannan yaron ba shi ne Armad Djinn ba daya fafata a gasar Jinzidal ba? Lallai shi ne, ya akai da bamu gane shi ba? Wai ya akai ma za'a siyar dashi a matsayin bawa? Mai yake faruwa?"
To ga dukkan alamu an cire dukkan hijabin dake hana wannan mutane gane Armad, kuma lallai a wannan lokaci kowa ya gane wanene Armad.
***
Babi na 56&57: Nostaljiya Nára
____
_______
Nan take Nostalgiya ta juya ta kalli waɗannan ƴan kallo da suka zo wannan cinikin bayi, ai kuwa daga cikin girman Izzar ta sai ga SANYIN BABBAN SIHIRI nan ya fara sauka acikin wannan waje a yanayinsa na ƙanƙara ruwan toka. A wannan lokaci ya fara bin jikin dukkan mutanen dake wajen, kuma duk wanda ka kalla babu abinda zaka gani sai ƙanƙara ruwan toka nannaɗe a jikinsa.
Nostalgiya tai ƙaraji na ɓacin rai, ta ɗaga takobinta sama takai sara kan iska. Ai kuwa saiga wasu aljanu nan guda biyu sun bayyana suna ƙoƙarin kare wannan sara mai ɗauke da Izzar sanyin babban sihiri.
Abu ne sananne idan ka ɗauke Farar-laya babu abinda aljanu ke tsoro irin Sanyin babban sihiri. Nostalgiya tasan haka kuma ga dukkan alamu tayi niyyar halaka wannan aljanu ne baki ɗaya.
Inda tayi tsalle sama ta dira akan ruwan cikin wannan aljanu da ƙafafunta ma'abota Izza.
Yau waye ya isa ya jada ƴar gidan Bihanzin mai Dauwamammen Sara.
A wani irin yanayi mai kama da hauka da tsananin ɓacin rai Nostaljiya ta hau saran wannan aljanu baji ba gani. Jinin aljanun yayi sama, kan kace meye wannan yayi faca-faca da ko'ina. Ko dama ɗaya bata bawa wannan aljanu ba na kare kansu ba kafin ta aikasu lahira.
Ta juyo da idanunta ga wannan bayi da aka riga aka siyar, idanunta na sauka akansu nan take duk ankokin dake ɗaure dasu suka zube a ƙas.
Armad na gefe yana kallon tsananan ɓacin rai wanda har yaso yaɗan ɗara nasa. Abu na gaba daya ji shi ne hannun Nostaljiya ta jashi sun tashi sama inda suka fice daga cikin wannan waje suka tashi sama.
A can cikin wajen hawa na uku kuwa manyan jarumai ne masu wakiltar sarakunan Jinzidal. Daga ɓangaren dama jaruman sarki Rafiya ne guda uku. Dukkaninsu Izzarsu ta haura shekaru ɗubu biyar. Kai ɗaya daga cikinsu ma shi ne wanda muka gani a wannan Jinzidal wadda Armad ya taka rawar gani, wato Asifu wanda akewa laƙabi da Ruwan Bala'i.
Asifun ne ya fara magana yana cewa, "Wannan yarinya bata da hankali. Bansan maike faruwa ba, amma ga dukkan alamu sa'a tana tare damu domin kuwa akwai alamun soyayya a idanun wannan yarinya, kuma wannan soyayyar dake idonta ta rufe mata ido ta aikata abinda zai taimake mu mu ruguza daular babanta baki ɗaya. Saboda haka baza mu bita ba, kuma baza muyi mata komai ba anan. Mu barta ta gudu dashi wannan yaron. Kaga da haka zamu samu damar cin galaba akan tsohon ɗan adawar mu wato babanta Bihanzin. Tunda kunga duk laifin daya faru anan kawai saimu ɗora shi akan babanta kuma rubuta a rubuce mu aikewa da Ururu."
Asifu na zuwa nan a zancensa yai dariya mai cike da farin cikin, sannan ya ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryarsa domin kada sauran mutanen dake wajen suji, "Ban taɓa tunani babbar dama kamar wannan zata samu ba a garemu. Lallai wannan babban labari ne muyi maza mu tashi mu gabatar dashi izuwa sarki Rafiya."
Sauran manyan ma'abota Izzar guda biyu dake tare dashi suka girgiza kai alamun amincewa.
_______
Babu inda gimbiya Nostalgiya ta sauke Armad sai cikin wani sihirtaccen kogo. Wannan kogo dai waje ne na musamman wanda ke cikin daular babanta sarki Bihanzin, kuma babu wanda yasan dashi inba ita. A sau da dama idan tana so ta nutsu ta tuno babarta wadda ta mutu wannan kogo take zuwa tayi kwana da kwanaki tana hutawa tana kewar mahaifiyar tata.
Acikin kogon dai akwai ƙorama mai bada sanyi mai ciƙe da ni'ima da annushuwa. Ga kujeru da shimfiɗu na alfarma, ga kuma kayan ci da sha duk na sarakuna wanda Armad ma bai taɓa yin tsinkaye da suba.
Tana ajiye Armad ta ɗakko wata sabuwar rigarta ta wadda akaiwa ado da dinare ta fara goggoge masa datti da jinin dake jikinsa. Har a wannan lokaci ta kasa ɗago kai ta dubi Armad saboda hawaye da tausayin dake idanunta. Armad ɗin shima ya kasa cewa komai, abu ɗaya dai daya sani shi ne abinda ta aikata a wajen cinikin bayin can lallai saiya jawo wa babanta babbar matsala. Saboda haka bai san mai zai fara ce mata ba. Tunda dai saboda shi take duk wannan abun, kuma koma mai ya same ta shi ne zai zamo shila.
Amma abu guda ɗaya daya kasa ganewa shi ne mai yasa take wannan abubuwa. Wai anya kuwa tana cikin hankalinta kuwa? Sai dai kuma Armad ya tuna ba wannan ne lokaci na farko ba data fara sadaukar da rayuwarta ba domin ta ceto shi. Yana tunano lokacinda zai faɗa wannan rami kuma wannan dordor ya so ya halaka ta, amma taƙi sakarsa.
Can bayan wani lokaci Armad ya riƙe hannunta ya tsayar da ita, sannan ya ɗago da kanta domin yaga maike faruwa acikin idanunta. Amma bisa mamaki sai kurum Armad ya ƙara arba da irin sak abinda ya taɓa ji a shekarun baya, wato yaji tamkar ya santa a wani zamani mai tsaho daya gabata. Nan da nan ya cika ta yana haki. Yau dai koma mai ake ciki sai yaji amsar dukkan tambayar daya daɗe yana so yayi mata.
Nostalgiya taja dogon numfashi sannan ta goge fuskarta da hankici. Ta miƙe daga inda take tana murmushi sannan ta fara da cewa, "Ka taɓa gani na babu hijabi?" Tambaya ce amma ga dukkan alamu ba amsa take nema a wajen Armad ba, domin kuwa tasan cewa bai taɓa ba.
Shima Armad ɗin yasan haka, kuma nan take ya fara ƙinƙina a lokacinda yaga kamar tana nufin cire rigar dake jikinta. Muryarsa na rawa yana cewa, "Ehm.... Tsaya.....tsaya..... Ba saikin cire komai ba, na taɓa....."
Kawai Armad yaji Nostaljiya tasa hannu ta doke shi aka.
Nan da nan ya haɗe gira, "Laifin me kuma nayi miki harda duka?"
Nostalgiya ta ɓata rai matuƙa tana mai cewa, "Mai ka ɗauke ni, a gaban naka zan cire kaya. Kawai kai mana shiru kaga mai ake yi mana, a'a!"
Bayan data gama magana saita durƙusa a gabansa tana mai murmushi tana lallashinsa, "Kayi haƙuri na dake, ba zafi ko?"
Armad yana rasa mai zaice, tambayar kansa kawai yake, towai mai take nufi ne? Waishin mai ake ciki nema?
Ai kuwa ba jimawa Armad yaga dukkan wannan kogo ya cika da wani irin haske mai matuƙar ƙayatarwa. Da farko Armad yayi tunanin wata fitilar aka kunna, amma a lokacin ne Nostaljiya ta kashe fitilar dake ɗakin amma hasken kawai ƙara ƙaruwa yake. Ba jimawa Armad ya gano cewa wannan haske daga jikinta yake fitowa. Fatar ta gaba ki ɗaya ta juye izuwa wani abin kyalkyali da walƙiya mai tsananin kyawu. Armad ya fara tunowa da labarai daya karanta na tatsuniya akan wata wadda ake kira da Lasina Naitingele wadda aka ce tafi kowa kyau a duniya. Nan take Armad ya gano cewa wadda take gabansa lallai ta ma fita kyau. Idanun Nostaljiya na kaɗawa da tsananin ƙauna da tausayin Armad. Nan da nan Armad yaji jikinsa ya mutu murus.
Dama Nostaljiya tama ɗan fishi tsaho saboda haka koda ta jashi ya tashi ya tsaya a gefenta ya kuma kalli dattin dake jikinsa sai yai matuƙar raina kansa. Lallai Armad ya tabbatar babu wata mai kyawun wannan yarinya a duniya. Fuskarta madaidaiciya ce kuma Armad bazai iya siffanta ta taba sai dai kawai yasan cewa wannan fuska ta ƙunshi duk wani abu da kyau zai iya bayarwa. Jikinta ya ingantu matuƙa sama da na duk wata budurwa da Armad ya taɓa gani, ba shiri Armad ya fara kamuwa da surar wannan mace dake gefensa.
Nostaljiya ta fuskanci hakan sabida haka kawai tayi murmushi ta kuma ja hannun Armad izuwa ƙarshen wannan kogo. Suna zuwa ƙarshe suka ga wata ƴar ƙaramar ƙofa. Suna shiga ƙofar suka tsinci kansu a wani ƙaton lambu mai bada yanayin ni'ima da annushuwa. Armad ya fahimci cewa ashe wannan kogo a tsakiyar lambu yake.
A wannan lokaci ne Nostaljiya Sisiyu da Armad Wilbafos sukai tafiya a matsayin saurayi da budurwa a karo na farko a tarihi.
Nostaljiya ce ta fara magana, "Bari na fara, nasan kana da tambayoyi da yawa, amma idan na gama wataƙila ba sai kace komai ba.
"Kaga dai mahaifina Bihanzin ya daɗe yana neman hanyar da zai ruguza wannan Rukunai na Jinzidal guda biyu. Amma hakan ba abu ne mai yiwuwa ba indai baka da ƙarfin Izzar da zaka iya cin galaba akan sauran sarakunan Jinzidal biyar ba. Hakan ne ma yasa zaka ga ma'abota Izza wanda suke ƙin jinin cinikin bayin amma dole sai dai suyi biyayya saboda al'amarin na girman Izza ne da kuma girman runduna. Babu wanda ya isa ya fito shi shi kaɗai ya ce yau zaiyi fito na fito da dukkan manyan ma'abota Izzan dake kare cinikin bayi. Hatta mahaifina wanda ɗaya ne daga cikin sarakunan Jinzidal bashi da wannan ƙarfi. Kai hasalima bari kaji, na taɓa tambayar mahaifina akan irin ƙarfin Sarakunan Jinzidal yake cemin hatta daular Ururu da kanta baza ta iya yin fito na fito da dukkan sarakunan Jinzidal ba, koda kuwa zasu yi nasara to kuwa zasu rasa sama da rabin rundunarsu da mutanensu wanda kuma Ururu baza su yadda da hakan ba. Hakan nema yasa zaka ga Ururu na bawa wannan sarakuna na Jinzidal ƙima da mutunci sosai da sosai.
"Mahaifina yayi bincike ya gano cewa idan ka ɗauke Tarifil-fakta wanda har yanzu ba'a san waye ba ko kuma a ina yake ba, akwai wani mutun ɗaya wanda ya taɓa yin faɗa da Ururu kuma yaci nasara. Wannan mutun kuwa shi ne Bayajidda, kuma shi ne wanda kaji muryarsa a cikin wannan gari dana ceto ka daga ciki.
"To a binciken mahaifina ya gano cewa Bayajidda ya bar wani allon sihiri. Tun daga ranar da mahaifin nawa ya gano wannan allo yake ta bincike a kansa har zuwa wannan rana da muke magana. Wanda idan kai lissafi shekaru dubu ɗari da uku kenan, kaga shekaru tamanin da biyar kenan kafin a haifeni.
"Mahaifna ya bani labarin yadda ya gano sirrin wannan allo amma a yanzu bamu da lokacin da zan baka wannan labari domin kuwa ba ƙaramin dogon labari bane. Amma dai kai sani cewa wannan allo shi ne dai wannan allo wanda muka baka kaji mana muryar Bayajidda aciki shekaru da suka gabata. Mahaifina ya gano cewa sirrin Izzar da yake buƙata ya rusa Jinzidal dashi yana cikin wannan allo, kuma kaida kaji wannan murya da kunnenka zaka fi kowa gane mai nake nufi da wannan Izza. Dalilin da yasa kaga mun neme ka domin kaji mana wannan murya ta dake cikin wannan allo shi ne babu wanda ya isa yaji wannan murya sai wanda yaji muryar Bayajidda a cikin wannan gari wanda kuma dani da ƴan uwana duk mun kasa, hasalima ni kaɗai nake iya shiga garin amma nima ɗin ban taɓa jin komai ba. Ranar dana fara ganinka kwance cikin jini acikin wannan gari nasan cewa ƙaddararka da tamu ta riga ta haɗu a wannan duniya kuma babu wanda zai iya rabata domin kuwa kai kaɗai zaka iya jiyo mana sirrin wannan allo wanda shi kaɗai muke buƙata mu cimma burinmu.
"Da farko da na ganka acikin garin nan jikinka yana ci da wuta kawai na ceto kane sabida ina so kazo ka fassara mana wannan allo. Amma daga baya dana karanta tunaninka naga kana so ka taimaki mahaifiyarka ne sai naji tausayin ka ya kamani. Nakan so duk wanda naga yana son ya taimaki iyayensa.
"Amma a lokaci na farko dana taɓa jikinka sai naji tamkar na taɓa ganinka a wani zamani mai tsaho daya gabata, harma inajin cewa dani da kai mun taɓa soyayya wadda aka rubuta a tarihi. Da nayi zaton ni kaɗai nake jin hakan idan na taɓa jikin naka, amma sai na gano cewa kaima kana jin irin abinda nake ji. Bansan yadda abubuwan suka ci gaba da faruwa ba a cikin zuciya ta ba, amma tun daga wannan rana na kasa daina tunaninka. Na tambayi mahaifina ko irin hakan zai iya faruwa a gaske, amma yace min bai taɓa samun labari ba a tarihi. Saboda haka sai naci gaba da bincike.
"Haka na ci gaba da bincike amma har ila yau ban samu komai ba.
"Amma daga baya nayi alƙawarin zan taimakeka ka samarwa mahifiyarka lafiya koda kuwa zan rasa raina.
"Kayi sani cewa yanzu naga ka farkar da Izza mai ƙarfi acikin jininka, amma kana da buƙatar lokaci kaje ka sami horo ka gane yadda zaka sarrafa ta. Kuma idan ka ɗakko faɗa da Ururu yanzu baza ka sami wannan damar lokaci ba. Saboda haka nema na hanaka aiwatar da abinda kaso ka aiwatar a baya a wajen cinikin bayin can. Ni kuwa kaga ina da mahaifina dazai kare ni. Kuma kaima kasan saƙon da muka karɓa daga wannan allo, wanda kuma sauran ƙiris mu kammala haɗa wannan Izza. Zarar kuwa muka gama to babu wani Sarkin Jinzidal da zamu ji tsoro.
"Armad.... " Nostaljiya taja hannunsa suka tsaya a gaban wata bishiyar giginya sannan ta matsa kusa da jikinsa tana murmushi, "Ina sonka Armad. Karɓi wannan," Ta kama hannun Armad ta saka masa wani zobe a jiki, "Ba lalle mu ƙara haɗuwa ba a wannan duniyar. Amma wannan zoben zaisa ka ringa tunawa akwai wata data taɓa sonka wai ita Nostaljiya. Ba jimawa mahaifina zaizo nan, kuma bazan so ku haɗu ba. Sabida haka ka shiga wannan ƙofa zata maida kai ƙasa ta uku. Nayi bincike na gano akwai wani sharri a tattare da wannan ɗan duba Babara, kaje kaga halin da mahaifiyar ka take ciki kafin ka ci gaba da neman wani Tarifil fakta wanda babu wanda yasan taƙamaimai inda yake. Idan kana so kaje kayi horo a shashin Ikwatora to akwai ruhi na a jikin wannan zoben zai nuna maka hanya. Akwai ajiyar abinci da abinci da shekarun Izza ɗari biyar aciki da mahaifiya ta barmin a lokacin da zata mutu. Idan kana so zaka iya amfani dasu."
Ga dukkan alamu Noltajiya bata so taji amsar da Armad zai bata a yayin ta buɗe wata ƙofa ta tsafi ta tura Armad ciki ta rufe. Armad yana shiga ya waiwayo da niyyar yayi mata magana amma sai kawai yaji wani ƙarfin Izza na musamman yana zuƙe shi ciki kuma bashi da damar magana.
Abu na ƙarshe da Armad ya gani shi ne kwalla guda ɗaya daga kowanne idon Nostalgiya na fitowa. Sannan kuma daga bayanta yaga wani mutun ya bayyana wanda ganinsa ma kaɗai yasa Armad yaji ruhinsa yana neman fashewa ya tarwatse. Ba komai ya jawo hakan ba illa Izzar wannan mutumi. Armad baya jira a gaya masa cewa wannan mutun shi ne Bihanzin mai dauwamammen sara kuma lallai ransa a ɓace yake matuƙa.
Armad yaso a ransa ya fito ya tsaya a gaban wannan mutumi duk wani abu da zaiyi wa Nostaljiya yayi masa, idan ma kashe shi zaiyi yayi, amma dai kada ya sake ya taɓa Nostajiya, amma ina kafin yayi wani motsi wannan ƙofa ta ɓace dashi.
***
Babi na 58: Sabuwar Izza
Bayanda Armad ya shiga wannan ƙofa sai yaji wata irin Izza mai ƙarfin gaske ta zuƙe shi ciki. Idanun sa suka rufe saboda ƙarfin iskar da yaji.
Ba jimawa Armad ya buɗe idanunsa inda ya tsinci kansa a fili fetal babu kowa sai shi kaɗai.
Ya duba hagu da dama amma babu wani mahaluƙi sai ƙasaitaccen daji da manyan bishiyu. Armad yai ajiyar zuciya inda ya nemi waje ya zauna ya fara tunano abubuwan da suka faru dashi. Domin kuwa abubuwan sun faru da sauri ta yadda har izuwa wannan lokaci bai samu damar zama ya hakaito suba.
Ya tuno da watannin da yayi yana shan azaba a hannun wannan aljanu guda biyu. Ya tuno da yadda ya rantse saiya ɗauki fansa akansu amma sai gashi acikin daƙiƙa kaɗan Nostaljiya ta gama dasu. Ya tuno da maganar data gaya masa akan sarkin duba Babara dama sauran maganganu da dama data faɗa akan wannan allo da Bayajidda ya bari dama sauran sirrika data gaya masa.
Ya tuno da kalmar data gaya masa cewa tana son sa. A dai-dai wannan lokaci Armad ya tsaya yai duba izuwa wannan zobe data bashi. Yana murza zoben, zoben yana walƙiya tamkar ita mai zoben. Armad ya kula cewa da wani irin dinare na musamman akayi wannan zobe tayadda jikinsa har wani ƙanshi yake irin na musamman.
Armad yaro ne amma duk da haka bazai rasa sanin ma'anar kalmar so ba, kuma lallai yasan cewa abu ne mai matuƙar wahala mace ta fara gaya maka hakan, amma gashi Nostajiya ta ajiye kunya ta kuma gaya masa. Lallai ya amince acikin ransa cewa Nostaljiya da gaske mai ƙaunarsa ce da gaskiya. Amma babban abinda ya ɗaga masa hankali shi ne maganar data faɗa cewa ba lallai su ƙara haɗuwa ba. Abin ya tsaya masa a rai kuma ya kasa mantawa. Amma koma dai menene Armad ya yanke shawara cewa da kansa zai nemi Nostaljiya a duk lokacin daya samarwa mahaifiyarsa lafiya.
*N.....nusi?* A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya tuno cewa tun bayan lokacin da hankalinsa ya gushe a tsakiyar fafatawarsu da Ikenga da Uznu Ururu bai ƙara ganin Nusi ba. Hankalinsa yai matuƙar tashi domin kuwa yasan cewa shi tazo taimako a yayin wannan gasa. Saboda haka koma mai ya same ta shi ne sila.
Hankalinsa ya ƙara tashi yayin da ya tuno cewa ba wannan ne karo na farko ba da Nusi tai ƙoƙarin sadaukar da kanta ta taimake shi ba. Nan take Armad ya miƙe. A wannan lokaci yasan lallai zama bai same shi ba.
Abu na farko da Armad ya fara yi shi ne duba taskar Izzarsa domin ganin sabuwar Izzar daya samu. Idanunsa suka gane masa abubuwa guda uku: shekaru dubu ɗaya, wani ɗan ƙaramin allo, sannan kuma da wani mutun-mutumi mai kama da Armad amma sai dai idanunsa ruwan ƙasa ne masu launin toka.
Armad ya zauna ya lankwashe ƙafafunsa domin tayarda wannan abubuwa dake cikin ruhinsa. Ya karanta ɗalasiman da ake buƙata a ransa sannan ya kira wannan Izza ta shekaru dubu. Nan take yaji wannan Izza ta shiga jikinsa da wani irin ƙarfi wanda bai taɓa jinsa ba. Armad ya riga yasan cewa duk da cewa yawan shekarun Izza nada muhimmanci amma bayan yawa akwai inganci. Wato tayadda zaka samu cewa wani yana da shekaru wanda basu kai naka yawa ba amma kuma yafi ka ƙarfin Izza. A wannan lokaci Armad yana ji a jikansa cewa hatta ƙasa baza ta iya ɗaukansa. Wannan shekaru dubu na Izza suka shiga jikinsa suka haɗe da ruhinsa. Ya zama su suma suka zama shi. Armad yaji gashin jikinsa ya fara zafi, zuciƴarsa ta fara bugawa da ƙarfi kamar zata fito. Kafin yai wani abu wata kumfa mai zafi ta fara fita daga fatarsa tamkar ana wanke wata cuta daga jikinsa. Kayan jikinsa suka jiƙe sharkaf da datti da wannan kumfa mai haɗe da gumi. Haka ya kasance a wannan hali tsahon sa'a ɗaya kafin daga bisani wannan kumfa ta daina fita. Armad ya miƙe tsaye ya kalli jikinsa yaga hatta yanayin fasalin sa ya canja. Fatarsa kaɗai tana bada wani alamun ƙarfin Izza wanda shi kaɗai zai iya tarwatsa abokan gaba. A wannan lokaci ya gane cewa wannan kumfa shekarun Izzarsa ne guda hamsin da ɗaya aka tarwatsa su aka watso su waje domin baza su iya haɗa kafaɗa da wannan sabuwar Izza ta gidan Wilbafos.
Shi kansa yasan cewa yana jin wani irin ƙarfi wanda bai taɓa tsammanin ɗan adam zai iya jinsa ba a rayuwarsa. Yai duba izuwa wannan mutun-mutumi dake cikin ruhinsa ya kira shi da ƙarfin Izzarsa. Nan take wannan mutun-mutumi ya taho ya shige jikin Armad. Haka na faruwa idanun Armad suka juye izuwa ruwan ƙasa masu alamun toka. Wannan idanu na bayyana Armad yaji ƙarfin Izzarsa na walƙiya ya dawo jikinsa duk da kuwa babu aljani a jikinsa.
Armad yai kira ga wannan allo inda shima ya gabato a gabansa. Ya karanta ɗalasiman dake kan wannan allo a nutse. Yana gamawa yaga takobinsa ta Wilbafos ta bayyana, amma a kanta maimakon taurari biyar yanzu sun koma bakwai. Sannan kuma ƙarfin Nauyi dake cikin wannan takobin ya wuce hatta shi kansa yadda Armad zai iya misaltawa.
Murmushi irin na Izza kawai yayi sannan ya juya ya nufi hanya da niyyar samun kogi domin ya wanke jikinsa ya kuma nufi doron ƙasa ta uku. A dai-dai wannan lokaci Armad ya gane cewa ai Babara bai ma isa ya sashi aiki ba. Ya kuma yanke shawara zai koma izuwa Babara ya tursasa masa yayi wa mahaifiyarsa magani dole ko yana so ko baya so.
***
Babi na 59&60: Ubbaru
______
Armad ya gama wanka, amma babbar matsalarsa kayan sawa. Rigar dake jikinsa har yanzu a yayyage take. Lallai bai kamata mutun mai ƙarfin Izza irinsa ya ringa yawo da ita ba.
Yana zaune a gefen ƙoramar da yai wanka yana lissafin hanyar da zaibi ya gane a wane doron ƙasa yake sai hankalinsa yakai ga zoben dake hannunsa. Armad yai duba izuwa zoben, wanda ba wani bane illa wanda Nostaljiya ta bashi.
Yana ayyanawa a ransa yaya zaiyi amfani da wannan zobe sai ƙofa ta bayyana a saman zoben ta kuma fara girma a hankali a hankali har saida takai yadda Armad zai iya shiga cikinta. Armad baya iya hango komai aciki sai haske saboda haka ya fara tunanin ya shiga ko karya shiga.
Daga ƙarshe dai ya yanke shawarar cewa Nostaljiya baza tayi abinda zata cuceshi ba, saboda haka ya miƙe ya shiga cikin wannan ƙofa. Yana shiga ƙofar ta rufe.
Armad ya tsinci kansa a wata duniya ta musamman. Komai acikin wannan duniƴar kyalkyali yake da haske. Ga wasu ƙofofi nan guda biyu a gabansa. A saman ɗaya ansa Armad a saman ɗaya kuma ansa Nostaljiya. Kowacce daga cikin ƙofofin a buɗe take amma bisa mamaki Armad baya iya hango abinda ke ciki. Idan yai duba izuwa ciki babu abinda yake hangowa sai haske.
Armad ya yanke shawara ya shiga ƙofar da aka sa sunansa a jiki. Inda ya tafi gadan-gadan ya tura ƙofar ta ƙarasa buɗewa sannan ya faɗa ciki. Yana shiga ya tsinci kansa a wani ɗaki mai cike da kantoci sama da goma. Kowacce kanta na ɗauke da kaya na musamman a kanta.
Kanta ta farko da Armad ya fara gani itace ta kayan sawa. Riguna irin na alfarma wanda za'a iya sawa a gari kuma za'a iya fita filin daga dasu kala-kala. Ƙanshi ne kawai ke tashi daga wannan kaya wanda Armad bai taɓa ganin mai kyansu ba.
A ɗaya ɓangare kuma akwai takubba, masu, kulke dama sauran kayan yaƙi na musamman. Sannan kuma a wani ɓangaren kuma ga kwalabe na magani kala-kala. A wani ɓangaren kuma ga kayan ci da sha na marmari irin na musamman.
Wani abu guda ɗaya daya bawa Armad mamaki shi ne wani ingarman doki wanda tsayinsa yakai zira'i da dama. Yana tsaye a ɗaure baya ko motsi, ba kuma alamun abinci ko abin sha a tattare dashi. Lallai kana ganinsa abinda zaizo kanka shi ne wannan dokin na aljanu ne.
Koda ganin wannan kaya da wannan doki na musamman babu abinda yazo zuciyar Armad sai cewa Nostaljiya ta daɗe tana so ta taimakeshi ta bashi wannan zobe, domin lallai wannan shiri bana dare ɗaya bane.
Armad yai ajiyar zuciya, shidai baya tunano lokacin da yayi tunanin Nostaljiya tun bayan sanda suka rabu a shekarun baya amma ga dukkan alamu abin ba haka yake ba a wajenta. Kuma lallai irin wannan halacci da tayi ya shiga zuciyar Armad. Abinda kawai zai hanashi komawa gareta shi ne lashin lafiyar mahaifiyarsa da kuma Nusi. Domin tuni Armad ya yanke shawara saiya koma daular denizawa domin gano inda Nusi take.
Armad ya zaɓa daga cikin kayayyakin ya kuma canja kaya, ya kuma ɗebi kayan itace domin ya cika cikinsa. Sannan ya nufi wannan doki.
Koda isarsa sai dokin ya durƙusa ba tare da gardama ba, inda Armad ya hau kansa a nutse. Hakan na faruwa Armad yaji tamkar yana jin mai wannan doki yake tunani kuma tamkar zai iya magana da dokin. Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen tambayar dokin sunansa. Abin mamaki wannan doki ya amsawa Armad ba tare da ya buɗe bakinsa ba. Wato dai a taƙaice da zuciya sukai magana da ubangidansa, Armad.
"Suna na Ubbaru." Armad yaji muryar dokin tamkar haniniyar ingarman doki. Da farko saida yaja da baya cikin tsoro amma ba jimawa ya ware. Sannan ya umarci dokin daya nufi ƙofa dashi.
Abu kamar wasa dokin ya miƙe ya nufi bakin ƙofa ya fito yana sassarfa. Inda ya tsaya a bakin ƙofar da aka saka sunan Nostaljiya akai amma zuciyar Armad ta gaya masa bai kamata ya shiga wannan ɗaki ba domin kuwa ba sunansa bane akai. Saboda haka Armad ya umarci Ubbaru daya juya ya fita daga duniyar wannan zobe.
Armad na bayyana a wajen wannan ƙofa dake saman zoben, ƙofar ta ɓace baki ɗaya. Daga Armad sai wannan ƙorama, sai kuma jaka mai cike da tuffa da inubi dake hannunsa. Rigar jikinsa doguwa ce ƴar shara ce irin ta mutanda wadda jarumai ke so domin basu dama da take wajen watayawa su sarrafa takobi. Kalarta shuɗiya ce. Sannan kamar yadda ya saba a baya Armad ya samo maɗaurin kai ya kuma ɗaurashi a kansa dai-dai inda yake sawa a baya ya rufe tambarin Miyurarsa. Sai kuma Ubbaru wanda fari ne fat mai yawan faɗin kafaɗu da dogayen ƙafafuwa.
Armad ya ɗakko tuffa ɗaya da inubi ya cilla a bakinsa sannan ya nufi hanya. Bashi da niyyar tsaya har sai sanda yaga gari, a nan kuma zai tsaya ya tambayi a wacce doron ƙasa yake. Sannan ya kara bazama bazai yada zango a ko'ina ba sai doron ƙasa ta uku.
Ubbaru yai haniniya, sannan ya miƙa dogayen fararen ƙafafunsa gaba ya nufi hanya yana matsanancin gudu. Armad ya kula cewa gaba ɗaya gefensa da duniyar dake kewaye dashi ta ɗauke saboda tsananin gudun da Ubbaru yake. Babban abin mamakin shi ne ko kaɗan iska bata damun Armad duk da wannan gudu, sannan kuma yana iya hango abinda ke can gabansa kafin ya tunkaro shi. Armad bashi da wata hanyar dazai iya hakaita iyakacin gudun da Ubbaru yake, amma lallai yasan al'amari ne babba.
Kimanin sa'a biyar bayan fara wannan tafiya Armad ya keta a ƙalla dazuka hamsin. Amma babu abinda ya kawo masa tsaiko domin duk namun dawar dake wajen tamkar ma basa iya ganin Ubbaru. To a wannan lokaci ne Armad hango wani ɗan ƙaramin gida dake can gabansa a tsakiyar daji. Armad ya sanarda Ubbaru ya tsaya idan yaje wannan gida. Ai kuwa ba jimawa Ubbaru ya isa gidan inda ya tsaya cak tamkar matacce babu ko tirjiya.
Yana tsayawa Armad yaji muryar mutane acikin wannan gida. Wani murmushi yazo masa domin kuwa yasan cewa zai samu labari akan a wacce doron ƙasa yake.
__________________________________
Armad ya tura ƙofar wannan gida wadda dama a buɗe take ya kuma shiga ciki. Abu na farko daya fara gani shi ne jerin tebura da mutane zaune akai wasu suna shan barasa wasu suna cin abinci. Sannan daga can gefe kuma ga wani ɗan tsoho mai yawan sanƙo yana ɗago masa hannu yana tambayarsa, "Mai kake so ɗan yaro, abinci ko barasa?"
Nan take Armad ya gane cewa wannan waje irin gidajen nan ne na ci da sha na matafiya da ake gina su a hanya. Kuma ya tuno cewa da dama daga cikin waɗannan gidaje basu da nisa da gari.
Armad ya dubi wannan ɗan tsoho yana mai cewa, "Ruwa kawai nake so."
Tsohon ya kyaɗa kai sannan ya nunawa Armad wajen zama. Ba jimawa aka gabatowa da Armad abinda ya buƙata. Wata yarinya sanye da doguwar riga samfurin al'adar doron ƙasa ta uku. Armad na ganin haka yai mata murmushi sannan bayan ta ajiye ruwan ya tambayeta, "Ina ne nan?"
Yarinyar tana da ƙaton wawulo daga saman dasashinta saboda haka data yiwa Armad murmushi saida ya ɗan buɗe ido cikin mamaki. Yarinyar ta fahimci haka saboda haka ta ɗan rufe bakinta cikin kunya tana mai cewa, "Doron ƙasa ta uku kusa da ƙauyen garin Jari"
"Ehmmm...." Armad yaja numfashi cikin mamaki. Duk da baiyi yawo da yawa yana yaro ba amma yasan cewa wannan ƙauye data faɗa yana kusa da ƙauyensu, nisan baifi tafiyar ƴan kwanaki bace. Nan take wani gagarumin farin ciki ya cika zuciyarsa domin ko ba komai yau zaiga mahaifiyarsa.
"Yauwa nagode. Nawa ne kuɗin ruwan."
Yarinyar ta kyaɗa kai, "A'a ba saika biya ba. Ruwa ai kyauta ne."
Armad na niyyar yin magana ya ga an dako ƙofar wannan gida ta ɓalle, sannan kuma yaji muryar wani bajimin gardi daga ƙofar, "Kai wannan ko dokin wane ne ya zama nawa! Idan kuma maishi nada ƙarfi yazo kwata."
Gardin nada shekaru casa'in na Izza sannan kuma a bayansa akwai girɗa-girɗan mutane wanda duk sunma fishi girma. Suna tsaye akan Ubbaru suna jira Idan ba wanda yai magana su kwance shi su tafi.
Dukkan waje yai tsit kamar mutuwa ta gifta, amma Armad murmushi kawai yayi sannan ya miƙe ya nufi gurin wannan ƴan fashi. Baiyi ko taku biyar ba yaji an riƙe hannunsa ana jawo shi baya. Yana waiwayawa yaga wannan yarinya mai wawulo a bakinta. Yarinyar tana girgiza masa kai alamun kada ya takale. Tana mai nuna masa wawulon bakinta alamun dai wannan ƴan fashin sune suka cire mata haƙoran nata.
Armad na ganin haka tausayin yarinyar ya kamashi domin kuwa yana da tabbashin cewa wannan tsohon ba babanta bane. Domin kuwa an saba ganin yara irinta ƴan shekara goma zuwa ƙasa suna yawo a irin wannan gidaje neman aiki. Badan komai ba saidan cewa an siyarda iyayensu a cinikin bayi na Jinzidal. Wasu da dama daga nan suke lalacewa wasu kuma su shiga duniya. Irin wannan yara na daga cikin babban dalilin da yasa Armad ya tsani gasar ta Jinzidal.
"Yaya sunanki?" Armad ya durƙusa ya tambaye ta.
Yarinyar ta amsa a tsorace, "Aisha." Sannan tai ƙasa da muryarta sosai cikin tsoro ta gayawa Armad wata magana wanda shi kadai yaji.
Armad naji ya miƙe ya nufi kan waɗannan ƴan fashi.
Babban cikinsu mai Izza casa'in ya dunƙule hannunsa saiga ƙawanyar wuta ta bayyana akai. Baya ganin Izzar Armad amma yasan cewa Armad yana da Izza saboda haka ya fara shiri tun kafin Armad yazo. Na bayansa ma suka fara dariyar tsokana suna zare takubbansu. Kana ganinsu kasan sun raina Armad kuma suna tunanin baifi suyi masa ɗauka ɗaya ba.
Amma dukkanin hakan ya canja a lokacin da Armad ya bayyana a gabansu. Yana ajiye ƙafarsa sanyin babban sihiri ya bayyana ya rufe waɗannan ƴan fashi. Idanunsu a kwale cikin tsananin mamaki suka ƙanƙare a tsaye a inda suke. Waye zaiyi tunanin samun ma'aboci izzar da zai iya amfani da sanyin babban sihiri a wannna ƙauye? Armad ya dubi babban cikin nasu sannnan juya izuwa Aisha ya tambayeta, "Wannan ne?"
Ta kyaɗa kai cikin tsoro.
Abu na gaba da aka gani shi ne haƙoran wannan ɗan fashi a ƙas Armad ya zubar dasu.
Armad ya fara magana cikin ƙarfin Izza, "Daga yau wannan waje yana ƙarƙashin kariya ta. Duk wanda ya taba shi, to ni ya taba."
Sannan Armad yayi wa Aisha murmushi kafin ya hau kan dokinsa ya ɓace daga wannan waje ya nufi wajen sarkin duba Babara.
_____________________________
Babu jimawa Ubbaru yakai cikin wannan daji da Armad ya haɗu da Babara shekaru da suka gabata. A wannan waje ne Armad yai bankwana da mahaifiyarsa ya fita nemo mata magani shekaru da dama da suka wuce. A wannan waje ne sarkin duba Babara yai masa alƙawarin indai ya nemo Tarifil fakta to zaiyi maganin cutar dake damun mahaifiyarsa. A wannan waje ne Armad ya fita daga ƙasarsa ta haihuwa zuwa duniya yana da Izza hamsin da ɗaya amma yanzu gashi ya dawo da dubu. Shin mai Babara ya taka? Ta yaya zasu ƙarke? Domin Armad yazo ne yayi wa Babara dole! Dole ya bawa mahaifiyarsa magani. Ko yaƙi ko yaso! Yaya wannan al'amari zai kasance?
***
Babi na 61&62: Abul Babara
______
Armad yai duba izuwa kwazazzabon rafin dake gabansa mai yawan duwatsu. Komai na nan dai-dai tamkar yadda ya rabu dashi a shekarun baya. Yana tuna dai-dai lokacin da ya ɗakko mahaifiyarsa yazo wannan waje yana neman sarkin duba Babara. Yau gashi shekaru da dama sun shuɗe kamar ba'ai ba.
Armad ya sauka daga kan Ubbaru ya mai dashi Cikin zoben sihirinsa sannan ya ci gaba da nufar cikin wannan duwatsu yana tunkarar inda yake tunanin zai samu Babara. A wancan lokaci ya tuna cewa ya samu Babara a cikin ƴar bukka wadda ke cikin wannan daji to amma shekaru sunja, bashi da tabbas zai kara samun Babara acikin irin wannan yanayi daya barshi.
Bai jima da fara tafiya ba yaji motsin halitta a bayansa, inda ya labe sannan yakai hannunsa kan takobinsa. Ba jimawa ya gane motsin na takun sahu ne, kuma ɓangarensa yake yiwowa. Armad ya laɓe a bayan wani ƙaton dutse domin ya ga waye ke tafe. Ai kuwa ba jimawa yaga wata budurwa sanye da farar riga doguwa irin ta ma'aikatan asibiti ta bayyana. A hannunta akwai ɗan tulu na ruwa, yanayin ta na nuna alamun sauri. Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Bai taɓa tunanin ganin mace irin ta acikin wannan daji ba. Idan zai iya tunawa da kyau shi kansa Babara saboda an kore shi daga cikin gari ƴasa ya tsinci kansa a wannan waje.
Bayan da tai gaba sai Armad ya fara binta a baya. Bai san inda zata je ba amma koba komai zata iya sanin inda Babara yake. Ba jimawa suka isa bakin wani ƙaton tanti wanda Armad bai san dashi ba a lokacin daya ziyarci Babara. Nan take ya laɓe a bayan wani farin dutse tayadda zai iya hangen abinda ke faruwa a gaban wannan tanti. Ana haka wannan budurwa daya biyo ta fito daga cikin tantin amma tare da wata budurwa ita ma sanye da kaya irin na ma'aikatan asibiti. A hannunsu suna ɗauke da wata mata sanye doguwar riga. Nan take sukai shimfiɗa sannan suka kwantar da wannan mata suka farai mata fifita.
Kallo ɗaya zakai wa matar da suka kwantar kasan tana cikin ƙoshin lafiya. Abu ɗaya kacal da zai nuna ba'a cikin hayyacinta take ba shi ne idanunta, wanda suke a rufe ruf. Amma fatar ta sheƙi kawai take sannan kuma babu rama a tattare da ita.
Wata ƙwalla ce mai zafi ta fito daga idanun Armad a lokacin da yaga wannan mace, domin kuwa ba kowa bace illa mahaifiyarsa. Ba tare da wani tunani ba Armad ya fito daga bayan wannan dutse ya nufi inda wannan mata suke. Koda ganinsa sai suka miƙe suka jada baya. Amma bai kula dasu ba, kurum yaje ya durƙusa a gaban mahaifiyarsa yana mai kuka da muradin ina ma zatai masa magana.
Abu na farko daya fara fuskanta shi ne babu alamun wuya a tattare da ita. Amma kuma dai kamar ƴadda ya rabu da ita har yanzu tana cikin suma. Yanzu abinda ya rage masa shi ne ya tursasawa Babara ya bata magani ta dole. Saboda haka ya juyo ga waɗannan mata guda biyu.
Amma kafin yayi magana ɗaya daga cikin su ta fara karkarwa tana cewa, "Ma'aikatan asibiti ne mu, babu abinda ya kawo mu face mu kula da ita. B......babara ne ya ɗakko mu."
Armad najin sunan Babara hannunsa yakai kan takobinsa, "Ina Babaran?"
Amma duk su biyun babu wadda ta iya amsa masa. Karkarwa kawai suke. Ana cikin wannan hali Armad yaji muryar Babara kamar yadda yasan ta a shekarun baya da suka gabata.
"Armad Wilbafos! Barka da dawowa, ina fata ka dawo min da abinda mukai alƙawari?"
Armad yai duba izuwa ƙofar tantin nan inda wani wada mai yawan farin gashi ya fito. Wannan wada ba wani bane illa sarkin duba Abul-Babara. Mutumin da shekarun da suka gabata yayi wa Armad alƙawari zai samarwa mahaifiyarsa lafiya zarar ya nemo Tarifil-fakta. Sai dai kuma gashi Armad ya dawo bayan tsahon lokaci amma ba tare da Tarifl-fakta ba. Koda yake duk da cewa Babara bai yiwa mahaifiyarsa tasa magani ba yadda Armad yaga Babaran ya ɗakko ma'aikatan lafiya suna kula da ita yasa ya ɗan rage zargi dake cikin ransa. Amma hakan bai hana Armad zare takobi ba tare da tunkarar Babara.
"Zan baka dama ɗaya tak kayi wa mahaifiya ta magani ko kuma takobi ta tasha jininka."
Babara yai murmushi gami da girgiza kai, "Idan ka kashe ni waye zaiyi maka bayanin ciwon dake damun mahaifiyarka kuma waye zai gaya maka labarin ƴar uwarka Hidaya. Samu waje ka zauna."
Babara ya tafa hannayensa inda wasu kujeru suka bayyana. Babara ya zauna a ɗaya amma Armad ya tsaya da takobinsa a hannu, domin ba komai Babara ya gaya masa zai yadda ba.
"Hidaya kuma?" Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Shi dai dama yana ji a jikinsa yayar tasa na nan da rai. Amma da kakansa da babarsa sunƙi gaya masa wani abu akanta.
Babara yayi kyaran murya tare da fara jawabi, "Sama da shekaru dubu da suka wuce ƙungiyar ƴan-duba ta duniya ta daɗe tana rikici da jinsi daban-daban na aljanu. Asalin rigimar aljanu ne suka fara zargin ƴan duba da keta musu haddi su kuma ƴan duba suna zargin aljanu dayi musu ƙarya. Rigima ce data fara ƙarama amma daga baya ta zama hamshaƙiya wadda ta halaka dubban ƴan-duba da aljanu. Shekaru sittin da huɗu da suka wuce Hidaya ta shiga tsakani ta raba wannan rigima, lamarinda ya kawo zaman lafiyar da ake dashi a yanzu. A sakamakon haka a matsayina na shugaban yan duba nayi alƙawari zan saka mata da sak irin alkhairin datai mana komai daren daɗewa.
"A wancan lokaci bazan manta ba Hidaya ta bugi ƙirji tana cewa bata buƙatar komai daga waje na. Amma sai gashi ko shekara ɗari ba'ai ba yaƙi ya haɗa da ita a tsakanin aljanu masu biyayya ga Ururu da kuma sauran sarakunan aljanu. Yaƙi mai tsananin gaske wanda babu yadda zatai ta iya barin filin daga duk da kuwa mahifiyarta bata da lafiya, kuma ƙaninta yana buƙatar taimako.
"Ciwon dake damun mahaifiyarka ana kiransa da Cutar-Izza. Ciwo ne wanda ake samu a yayinda ma'aboci Izza yake ƙoƙarin ƙara yawan Izzarsa. Duk wata hanya da ake amfani da ita wajen ƙara Izza zata iya jawo wannan cuta amma bansan taƙamaimai wacce hanya ce ta jawo wa mahaifiyarka wannan cuta ba. Kai sani cewa wannan ciwo ciwon ajali ne. Duk wanda ya sameshi ƙarshensa kabari. Kuma wannan ciwo shi ne yasa zaka ga sama da kaso casa'in da tara na mutane sun gwammace su haƙura da izzarsu a iya shekarunta, domin ko yaya aka samu matsala a lokacin da mutun yake ƙoƙarin ƙara yawan Izzarsa to lallai ƙarshensa kabari. Abu guda ɗaya tak dake maganin wannan ciwo shi ne idan mutun ya karɓi shekarun Izza daga wani. Wato a misali ka ɗiba daga cikin shekarunka na Izza ka ƙarawa wannan mutumi.
"Kai sani cewa kamar yadda ake haifar ƙabilar Ururu da baiwar Baƙaƙen idanuwa haka ake haifar iyalan Wilbafos da baiwa ta musamman. Wannan baiwa ita kaɗai ce abarda zata iya maganin wannan ciwo."
"Wannan baiwa kuwa ba wata bace illa fasahar dake cikin idanunku. Idanu ruwan ƙasa masu ratsin toka. Duk wanda yake da irin wannan idanu yana da wannna baiwa, kuma iyalan wilbafos su kaɗai keda wannan idanu.
"Da wannan idanu zaku iya bayarda izza, za kuma ku iya karɓa tamkar yadda ake saka kaya a cire. Wannan ita ce baiwar ka a matsayinka na ɗan ƙabilar wilbafos. Kayi sani cewa turaka da nayi ka nemo Tarifil-fakta bashi da alaƙa da ciwon mahaifiyarka. Sai dai kawai na jefi tsuntsu biyu ne da tsakuwa ɗaya. Kaga tafiyar ka keda wuya na ɗakko waɗannan ma'aikata da kake gani na sasu su ringa kula da mahaifiyarka, ni kuma na tafi duniyar aljanu domin sanarda Hidaya abinda ke faruwa. Nasan duk duniya babu wanda zai iya yi mata magani sai ita, domin kuwa kai baka ma san komai ba acikin alamuran Izza a lokacin. To amma bansan halin da zan tarar da Hidaya ba, wataƙila ma bata raye, saboda haka kaima na tura ka duniya domin kaga yadda duniya take, kayi ƙarfi ka zama ma'aboci Izza tayadda koda ban samu Hidaya ba kaima zaka iya taimakon mahaifiyarka. Amma nasan baza ka iya nemo Tarifil-fakta ba. Kada ka manta hatta Ururu sun kasa nemo shi.
"Sai da na ɗauki shekaru biyu ina bilayin yadda zan shiga filin yaƙin da Hidaya ke ciki amma ban samu damar shiga ba, domin kuwa naji aljanu suna cewa hatta mutuwa tayi hijira daga wannan fili. Wasu aljanun ma suna cewa shi yasa yaƙin yaƙi ƙarewa saboda babu mutuwar da zata ci gaba da ɗaukar rai a wajen. Kai daga ƙarshe dakyar na samu wani tsohon aljani ya shigar dani filin yaƙin. Amma muna shiga wannan aljani ya rasa ransa. Nima ALLAH ne ya taimake ni na tsira dakyar amma duk da haka saida nayi asarar shekarun Izza ɗari biyar kafin na fito daga wannan fagen-daga. Tun daga nan nasan cewa ganin Hidaya ba abu ne mai yiwuwa ba. Kuma lallai babu wanda ƴa rage dazai ceto mahaifiyarka sai dai kai. Saboda haka na dawo na aiko maka da saƙon daka gani na wata bakwai.
"Naso na gaya maka haƙiƙanin mai ake ciki acikin saƙon amma na ƙara baka lokaci naga ko zaka iya farkar da jininka na wilbafos. Kai sani cewa nayi farin ciki kwanakin baya da naga hasken farin-wata ya canja kala. Domin nasan cewa lokaci yayi dazan biya Hidaya bashin da take bin ƙungiyar ƴan-duba ta duniya.
"Amma fa kai sani wani hanzari ba gudu ba...."
Armad ya katse Babara ta hanyar yin ƙaraji ya zare takobinsa yana huci, "Wai kana nufin duk wahalar dana sha ta nemo Tarifil-fakta a banza!!"
Armad bai san lokacin daya kaiwa Babara wani sara ba cikin ɓacin rai. Babara yai tsalle gefe guda yana murmushi, "To yanzu da ban tura kaba zaka farkar da jininka? Kasha wahala, amma yanzu zaka ga amfaninta. Sannan kuma indai hanyar Izza zaka bi wannan baka ga komai ba a fannin wahala. Yanzu duniya tasan dakai, idanun kowa zai dawo kanka. Idan bakai da wuri ba ka farka lallai yanzu ne zaka san wahala."
Babara yana magana amma Armad kawai huci yake yana kallonsa a fusace. Bayan ɗan lokaci Babara yaci gaba da jawabi, "Sai ansha wuya ake samu Izza. Kuma lallai indai kana so ka zama ma'aboci Izza yanzu ka fara. Saboda yayarka Hidaya nayi alƙawari zan koya maka yadda zakai amfani da idanuwanka wanda ita kaɗai ce hanyar da zaka zama ma'aboci Izza na gaskiya ka iya tsayawa a gaban Ururu sannan kuma ka ceto mahaifiyarka ta hanyar bata shekarun Izza. Amma kai sani cewa hatta yayarka Hidaya wadda hatta a duniyar aljanu ana labarin ƙarfin kwakwalwarta da gane abubuwanta saida tayi shekaru uku tana koyar yadda zatai amfani da idanuwanta. Lallai zaka iya yin shekaru goma kana koya wanda kuma mahaifiyarka baza takai wannan lokaci ba.
"Naji daɗin ganinka da wannan zoben domin zai taimaka mana wajen ajiye mahaiyarka aciki." Babara yai nuni da zoben da Nostaljiya ta bawa Armad.
Babara ya tafa hannunsa tantin dake bayansa ya ɓace, babu abinda ya rage sai wata ƴar jaka a hannunsa. Ya zira hannu a jakar ya ɗakko wata leda mai cike da Ayrid ya jefawa matan nan guda biyu ladan aikinsu. Sannan ya juyo wajen Armad yana mai cewa, "Zan koya maka yadda zakai amfani da idanunka dama kuma duk wani abu dana sani a shekaru na dubu ɗaya da ɗari uku a duniya. Saboda Hidaya."
Armad yama rasa mai zaice. Kansa yana nema yai tsawa saboda tsabar caji. Ya za'ai ace abinda yai shekaru yana nema wai dama duk gwada shi kawai ake. Sannan kuma babban abin haushin ma shi Babara yana nunawa ba wani abu bane. Hasalima har ya gama yanke shawara zai koya wa Armad al'amuran Izza kamar ma babu abinda ya faru.
Armad ya kasa daurewa, "Zan bika sabida mahaifiyata, amma idan wannan ma ya zama wani kwajin to lallai sai na sare kanka." Armad ya buɗe ƙofar wannan zobe ya killata mahaifiyarsa aciki sannan yabi Babara.
Babara yai dariya, "Kai sani cewa idan na bari mahaifiyarka ta rasu kona mutu sai Hidaya ta ƙara kashe ni."
A wannan lokaci hankalin Armad ya dawo kan Hidaya, inda ya buɗe baki ya tambayi Babara, "Wai kana da tabbas yayata tana raye? Kakana ya kawo min takobin ta shekarun baya da suka gabata."
Babara ya kyalkyala dariya yana mai kallon sama tare da cewa, "Kasan mai suke cewa yayarka a doron ƙasa ta farko? Hmmm.... Koda yake wasu suna cewa sunan ya samo asali ne daga jinsin Dordor wasu kuma suna cewa daga aljanun farko. Amma dai yayarka hatsabibiya ce ta rubutawa a jarida! Lallai baza ta mutu ta sauƙi ba, kuma idan ta mutu sai labari ya cika duniya."
Armad ya haɗe gira, "Wanne suna suke gaya mata?"
Babara yai murmushi gami girgiza kai, "Bari ta gaya maka da kanta idan kun haɗu."
________
Alhamdullh rabbil alamin. Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAH madaukakin sarki daya bani ikon kammala littafin farko na jerin littattafan Magajin wilbafos. Ina rokon ALLAH ya ci gaba da bani lafiya da ikon rubuta wannan littafi har zuwa karshensa.
Godiya ta musamman ga dukkan makaranta Wanda suka kasance tare dani tun daga farko har zuwa karshe.
Comments
Post a Comment