Skip to main content

WELCOME TO THE WORLD OF MAGAJIN WILBAFOS (THE HEIR OF WILBERFORCE)

I sincerely welcome you all to this amazing world of 'Heir of Wilberforce'!

Here, we'll by the grace of God, take the journey from the beginning to the end. That's to say, my humble self (the author) and my team, will be bringing this amazing serial to you from the first book to the last.

I hope you will enjoy the journey. I welcome you again, and I'm looking forward to your feedbacks.
***
Ina matukar yi muku Barka da zuwa wannan fili na duniyar 'Ƙasa Bakwai', duniyar 'Armad Wilbafos!'

Cikin yardar ALLAH, yadda muka fara da littafi na farko, haka zamu kai har littafi na ƙarshe, sannu a hankali, in ALLAH ya yarda.

Da fatan zaku nishaɗantu da wannan labarin, sai naji daga gareku.

Comments

  1. Allah yara lfy mujin datsi sosai

    ReplyDelete
  2. The greatest Doctor, we are appreciate with this blog.

    ReplyDelete

Post a Comment

Most Popular

Babi na sha biyar : Sanyin Babban Sihiri

A can wannan daji kuwa duwatsu ne iyakacin hangen ɗan-adam, inda daga cikinsu mutane sanye da kayan yaƙi suke ta ƙara ɓulɓulowa su na nufo wajan da su Zahra suke tsaye cirko-cirko tun bayan jin wannan murya. Kafin kace meye wannan mutane da dama sun kewaye su ta kowanne ɓari. Ana cikin haka wasu manya-manyan mutane waɗanda su kaɗai ne fuskarsu bata naɗɗaɗe da rawani suka fito fili daga bayan wasu jajayen duwatsu. Su na fitowa, kai tsaye suka fara kusantar inda su Hasanu suke tsaye. Dukkaninsu manya-manyan halittu ne tayadda in baka kula ba sosai ba, sai kace samudawa ne. Na tsakiyar tasu ya ɗan ɗara ragowar tsayi yana sanye kuma da jan rawani wanda kamar kamar rawanin sauran mutanen dake kewaye da wajan ba, bai rufe masa fuska ba. Yana ɗauke da wani ƙatoton farin gatari. Idan kuma ka duba zakaga cewa duk da duhun wajen bai hana idanunsa walƙiya ba, wanda idan ka ƙura ido zaka fahimci cewa acikin idon nasa akwai waɗansu abubuwa guda biyu acikin kowanne ido. Idan ka ƙara ...