Nan take abubuwa da dama, musamman hikayoyi da suka shafi wannan mutun-mutumi dake wannan waje, suka fara kai-komo acikin ranta. Cikin tsammani ta buɗe baki da niyyar fara yi masa tambayoyi, to amma da yake shima kamar sunyi anko ne, domin babu abinda ke kai-komo a zuciyar ta, banda tambayoyin nan guda biyu; wai shin wanene wannan yaro da har ya isa ya ga mutun mutumin Daikirin, kuma daga ina ya fito? Hakan ne yasa duk su biyun sukai anko wajan buɗe bakunan su da niyyar yiwa juna tambaya, amma a dai-dai wannan lokaci ne kwatsam babu tsammani idanun Armad suka rufe ruf, sannan babu alamar rai a tattare dashi, ya faɗi kasa da ƙarfi a sume. Kallo ɗaya kacal zakai masa kasan yayi zazzafan suma ne irin wanda bashi da nisa sosai da mutuwa. Cikin tsananin mamakin abinda ke faruwa da Armad tayi firgit ta matsa daga kusa dashi zuwa nesa, inda ta zauna tana haki. Ta dubeshi cikin mamaki da firgici zuciyarta cike da tunanin maike faruwa ne, kuma mai ya kamata tayi? T...