Skip to main content

Posts

Babi na sha hudu : Ikenga O Bayajidda

AA shekarar 1851 After Amri (A.A), a wani gari mai suna Jíha, dake kan doron ƙasa ta bakwai ɓangaren Arewa. Tsakiyar dare ne, kuma a wannan rana ma wuni akai ana azababben yaƙi tsakani ɓangaren Ururu da kuma ɓangaren ƴan adawa dake da shalkwatarsu a wannan gari. Babu abinda kake gani sai gawarwakin jama'a duk inda ka duba, dan kusan a wannan rana zaka iya cewa aka kawo ƙarshen wannan babban yaƙi. Wannan yaƙi dai shi ne wanda mahaifiyar Armad ta samu rauni ashi, kuma harma Armad yaci alwashin sai ya kawo mata mutumin data fita nema ta samu wannan ciwo har gida, komai rintsi komai wuya. To acikin wannan gari dai, duk inda ka kalla gawarwaki ne a kwance fululu, amma duk da haka idan ka samu ɓangaren da ba mutun a kwance, zaka ga cewa gaba ɗaya ƙasar wajen ta juye izuwa launin ja da baƙi, saboda yawan jinin daya kwarara a wannan rana. A ƙasa kaɗai al'ummar dake kwance a mace sun haura dubu ɗari, wani ba kai, wani ba ƙafa, wani kayan ciki a waje, wani a caccake da takubba,...

Babi na sha Uku : Wacce Shekara Muke wannan??

Tun bayan ɓacewar Armad daga wannan waje, hankalinsa ya dusashe ta yadda shi kansa bayan farkawarsa bai san a inda yake ba, bai san kuma tayadda yaje wajen daya farka ya tsinci kansa ba, sannan kuma bai san kwana nawa yai ba, tun bayan dusashewar hankalinsa ba. Amm abu ɗaya da yake iya tunawa shi ne, gab da kafin hankalinsa ya dusashe, ya kasance yana ta kai-komo da abubuwan sirrin da yaji daga wannan murya wadda take magana akan Rukunai guda biyu na Ururu. Sirrin da Armad ya tabbatar indai ya fita to lallai sai ya rikita dukkan duniyar ƙasa bakwai, tayadda zaman lafiya ma zai iya zuwa ƙarshe!! Da farkawarsa abinda ya fara yin arba dashi shi ne fili fetal gabas da yamma, gudu da arewa ko ina ya duba baya iya gano ƙarshensa. Babban abun mamaki da wannan waje shi ne babu alamun wata halitta a wajen ko kaɗan; kama daga kan namun daji zuwa tsirrai zuwa tsuntsaye, ko'ina ka duba ba komai a wajen kawai sai fili fetal da tsandaurin ƙasa. Sai dai kuma Armad bai shiga al'ajabin ...

Babi na sha biyu : Urúrú

Kwanaki huɗu bayan ɓacewar Armad bayanda yayi amfani da wannan hatasabibiyar hanya ya ceto su Zahra daga wannan baƙin ruwa da shuɗin Dordor ya harba musu. Zahra tayi shiru su na tafiya bata kuma yiwa kowa magana ba tun bayan tahowar tasu, duk da kuwa ƙoƙarin kwantar mata da hankali da Hasanu yayi tayi, kai hatta Kiru ma da ya nuna aniyarsa a fili ta so ya halaka Armad a baya, sai da ya sauko ya kuma fara lallamar Zahran yana gaya mata cewa shi dai bai gane mene ne a tsakaninsu ba, amma koma mene ne ta gane cewa, Armad ba irin mutanen da zasu mutu cikin sauƙi ba ne, ya kuma gaya mata da Armad ɗin zai iya mutu da wuri aida tuni ya rigaya ya halaka shi da farar takobinsa. Ya gaya mata hakan ne da wasa duk da niyyar ko zata ɗan saki fuska, amma ina ko kaɗan bata ma nuna ta jishi ba, idanunta kawai na nuna nutsawa acikin tsananin tunanin wani abu ne kawai. Tun da farko bata yarda sun baro wajan ba sai da suka kwashe awa ashirin da huɗu cir, tana kallon wajan da Armad ya ɓace. Babu yad...

Babi na Sha ɗaya : Dordor

Dordor!! Wannan suna ne wanda jama'ar wannan zamani suka laƙabawa waɗansu halittu, waɗanda ba mutane bane, hasalima a zahiri fatalwowi ne. Sai dai kuma amma su na da irin sura ta mutane sak, in banda waɗansu banbance-banbance da suka raba. Girmansu ya haura na mafi yawancin mutane misali, tsaka-tsakinsu sune waɗanda girmansu yakai kimanin girman ƙarti biyu na mutane a haɗe. Kalar fatar jikinsu zata iya ɗaukar kowacce irin kala, kama daga kan baƙi, fari, ja, kore, shuɗi kai dama dukkan sauran launuka. To ɗaya dai daga cikin irin waɗannan fatalwowi ne, ya nufo Armad ta baya, da tsananin muguwar niyya taya halaka shi. Kuma shi ne wanda Hasanu ya gano yana tahowa tunda farko, kuma shi ne dai wanda Zahra/Nostalgiya ta gani, lamarinda yasa take ta ƙoƙarin janyo Armad waje. A dai-dai lokacin da Armad ya waiwaya, sukai ido biyu da wannan fatalwa, mai suna Dordor, kamanninta suka shiga kwakwalwarsa. Nan take yasan cewa lallai a kowanne lokaci, mutuwa zata iyai masa sallama idan baiy...

Chapter ten : Gimbiya Zahra

Daga gefe, idanun Hasanu da wannan budurwa acike suke da mamaki, kuma zuwa wannan lokaci su na da cikakkiyar masaniyar cewa shima Armad, koma daga ina yake, lallai ya sami horo na musamman. Dukkaninsu sun san irin ƙarfin da farar takobin Kiru ke dashi, amma bisa mamakinsu Armad ya iya tare sara daga gareta kuma ba tare da yaje ƙasa ba. Hasanu ya ja numfashi sannan ya ƙara matsawa gaba, gami da ƙara ƙurawa Armad ido. Ya kalleshi sama da ƙas, sannan bayan wani ɗan lokaci sai kawai idanunsa suka canja, kamar wanda yake so yaga wani abu a tattare da Armad, amma kuma ya kasa. Yana shirin ɗauke ido daga kan Armad, sai idonsa yakai kan wannan jan ƙyalle dake ɗaure a gaban goshin Armad. Nan take ya ƙura masa ido tsahon daƙiƙu, kafin kwatsam idonsa ya cika da firgici sannan jikinsa ya fara karkarwa. Cikin ɗimuwa ya fara magana aciki, "madauwamiyar Miyura... ina ba abu bane mai yiwuwa... to amma... ''Hmmm.... ko madai ba ita bace a goshinsa ba, kashe shi a yanzu gangan...

Babi na Tara : Farar Takobi

Armad ne da Kiru a tsaye su na fuskantar juna, kowa da tasa takobin a zare! Tun dai ƴan mintuna da suka gabata, Hasanu wanda shi ne babban wannan tawaga ya kwance Armad ya kuma bashi takobinsa. Abinda kawai ya rage shi ne Kiru ya nunawa Hasanu da wannan budurwa, wadda ta kasance ƙanwarsa, irin sabuwar fasaha, da ya koyo. Fuskar Armad bata canja ba ko kaɗan, tamkar babu abinda ke faruwa, yana riƙe da ƙotar takobinsa. A wannan lokaci ne Kiru yayo kan Armad, yana zuwa ya ɗaga takobinsa ya kawo masa wani wawan sara. Wata ƙara mai kashe kunne ta tashi sama yayinda waɗannan takubba nasu suka haɗu a sama, lamarinda yasa dukkan tsuntsaye da sauran dabbobi dake kewayen fara guje-guje. Kan kace meye wata iska ta tashi daga kewayen su, inda ta bazu ko'ina, har saida ta kaɗa bangon ruwan dake arewa, wanda bashi da nisa da inda ake fafatawar. Kiru ya kalli takobin Armad idanunsa cike da mamaki, wanda a wannan lokaci fuskarsa taɗan canja, kana gani kasan haɗa takobin da sukai yasa ya...

Babi na takwas : Sirrin dazai rikita duniya

Abu ɗaya da Armad yake iya tunawa a lokacin da yake tsaka da faɗawa cikin wannan wawakeken rami shi ne riƙe takobinsa da yayi, ya ɗaure ta a jikinsa. Amma bayan wannan, gaba ɗaya hankalinsa dusashewa yayi, kafin daga bisani ya sume gaba ɗaya. To koma dai mai ya faru bayan wannan, wanda bazai iya tunawa ba, to yana ganin bai halaka shi ba tunda a dai-dai wannan lokaci ya tsinci kansa a kwance a kan tantagaryar ƙasa da kuma ragowar numfashi a jikinsa, ga kuma waɗansu abubuwa daya kasa tantancewa a tsaye a kansa... "Hmmmm...." Cikin firgici Armad yai ajiyar zuciya, acikin ransa bayanda kwatsam abin ya faɗo masa a rai cewa ko mutuwa yayi. A hankali a hankali, ganinsa yana ƙara dawowa, waɗannan halittun dake bisa kansa su na ƙara bayyanuwa, sai ya gano cewa ashe mutane ne! Ba daɗewa ya gano cewa ashe maza ne guda biyu da mace ɗaya. wadda ke tsaye a bayansu. Mamaki ya cika zuciyar Armad kuma hankalinsa ya ɗan kwanta, lokacin da yaga macen dake cikinsu ta cillo masa bu...

Babi na bakwai : Gimbiya Nostalgiya Nára?

A babi na shida mun tsaya a inda Armad ya faɗi a sume cikin wannan gari, bayan jin wannan murya. Yanzu zamu ɗora; *** Babban abinda Armad bai sani ba shi ne, wannan murya da yaji ta kasance kullum saita maimaita sak irin abinda yaji tana faɗa sau casa'in da tara. Bata taɓa fashin yin hakan ba, sannan kuma babu wani mahaluƙi daya taɓa shiga cikin wannan garin tun bayan da muryar ta fara maganar, sama da shekaru dubu kenan, sai Armad. A dai-dai wannan lokaci, Armad yana kwance a sume baisan inda kansa yake ba, sannan kuma bashi da masaniyar cewa duk sanda wannan murya ta gama maganarta, gaba ki ɗayan iskar wannan gari kamawa take da wuta, badan komai ba sai dan tsananin ƙarfin Izzar dake ƙunshe cikin muryar. Kuma hatta a wannan lokaci, abinda ya afku kenan; ɗaukewar muryar keda wuya, gabaki ɗayan ilahirin iskar dake cikin garin ta fara ɗaukan zafi. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne wasu tafka-tafkan jajayen kunami masu kafafu Irin na mutane, wanda a tsaye sunkai girma...