MAGAJIN WILBAFOS na A M Ibrahim Babi na ashirin da uku : Matafiyan Alwashi Tuni labari ya bazu kusan ko'ina acikin garin Khan, cewa ga abinda ke faruwa, kasancewar da dama sunada masaniyar me wannan hasken yake nufi. Saboda haka tuni mutanen garin suka fara tattauna abubuwa da dama, wasu suna farin ciki wasu baƙin ciki wasu kuma mamaki, kai wasu ma tuni sun fara azama domin isa bakin wannan ƙofa domin ganewa idanunsu. Amma ina haƙarsu bai cimma ruwa ba domin kafin ma su kansu ƴan tsirarun mutanen da ke wajen su ƙarasa suga fuskar Armad, sun nausa cikin garin. Sannan kuma wata sa'a data faru, shi ne da dama na mutanen baƙi ne, saboda haka suna da buƙatar subi ta cikin wannan ƙofa a hankali, domin yana daga cikin amfanin waɗannan mutun-mutumi duba zuƙatan masu shiga garin, domin tabbatar da cewa basu zowa garin da sharri ba. Kuma hakan nema yasa a daular Maikironomada ake auna girman gari da kuma falalar na cikinsa, da adadin wa...