MAGAJIN WILBAFOS NA A M IBRAHIM
Babi na ashirin da biyu : Shiga garin Maikironomada
Armad na zaune jingine a gindin wata bishiyar darbejiya, kansa yana kallon wata daren goma sha bakwai a sararin samaniya.
Irin iskar daren nan mai ɗan sanyi tana kaɗa rigar jikinsa da kuma maɗaurin kansa.
Babu abinda kake ji face kukan tsuntsaye da namun dawa a kusa da nesa. Amma ga dukkan alamu, dukkanin waɗannan abubuwa basu isa su katsewa Armad tunanin da yake ba, domin kuwa kallo ɗaya kacal zakai masa kasan cewa ya tsunduma cikin kogon tunani.
Can bayan wani lokaci mai tsaho, ƙarar bushasshen ganyen bishiya da ake takawa ta bayansa yasa ya farka inda ya waiwaya domin yaga wake kusato shi.
Nan kuwa yayi arba da Nusi, ita ma ta fito daga cikin tantin da suke, idanunta sun ɗanyi ja kaɗan, daga dukkan alamu ta ɗan gimtsa kuma bata daɗe da tashi ba.
Tun kafin ta ƙaraso, suna haɗa ido tayi masa murmushi. Sannan kuma tayi kyaran murya gami da cewa, ''Armad ƙanina!''
Tana faɗar haka, a karon farko run bayan haɗuwarsu wata ƴar ƙaramar dariya ta kwace mata, kafin daga bisani taci gaba, ''hmmm... kasan ko, ko a iya nan ka tsaya ka koma gida, na tabbata mahaifiyar ka zatai matuƙar farin ciki da jarumtar daka nuna....'' Nan take lafazinta ya ƙara taushi ya kuma juya mai kama da lallashi, ''basai ka matsawa kanka ba, idan muka mu ƙarasa cikin gari,'' ta ɗaga ɗanyatsan gami da yi masa nuni da wani waje daga can nesa ɓangaren arewa inda wani haske yake tashi.
''Akwai kuɗi na da zan karɓa na cin wannan jarabawa, nasan zai isa ka hau Ecigan har zuwa doron ƙasa ta uku.
''Hmmmm....karka damu, kyauta na baka, ba kace ni yayar ka bace!'' Ta ƙarasa maganar ta da wani lafazi, kamar tana jin tsoron kada yaƙi amince da biya masa da tace zatai.
Shima Armad murmushi kawai yayi sannan barta ta ƙaraso inda ya fara nasa jawabin, ''na yanke shawara, saboda dalilai guda uku;
''Na farko, lallai haƙiƙa ina so na koma gida wajen dangina, musamman yadda na fara ji a jikina cewa lallai na daɗe bamu haɗu dasu ba.
''To amma a yadda nake ɗinnan, ko na koma bana tunanin idan ma wani rikici ne ko kuma yaƙi ya taso zan iya taɓuka wani abu.
''Sai dai ma wataƙila na kawo musu cikas kawai, saboda kamar yadda nake gaya miki har yanzu na kasa kammala koyon ko ƙarni na farko na 'Wilbafosiyan siwod dans'.
''Saboda haka lallai bana jin zan ƙara musu wani abu.
''Sannan kuma na biyu, ina ganin na fara fahimtar kaɗan daga cikin dalilin da yasa dangina suke ɓoye wannan sunan.
''Saboda ina ganin suna na yana alaƙa da neman wannan mutun mai suna Tirifil-fakta. Ina tunanin ma shi ne yasa a duk cikin manyan kwamandojin Troika suka zaɓi mahaifiya ta domin ta jagoranci nemansa a wancan lokaci.
''Saboda haka, indai akwai dama, ko yaya take, na cewa zan cika burin mahaifiya ta na nemo wannan mutun koma wanene, to bazan jada baya ba, ko kaɗan har sai ranar da na cika buri na!!!
''Kuma ina ganin haɗuwa ta dake ƙaddara ce daga ALLAH, kamar yadda kike ta taimako na baji ba gani.
''Ina ƙara gode miki yaya, kuma ina fatan nima ALLAH ya bani damar dazan rama miki wannan alkhari. Saboda haka inaga wannan ita ce shawara t........."
Kwatsan ya katse zancensa, bai san mai ya faru ba, shi dai kawai yaji an jefo masa wani abu a fuskarsa, kafin ya ɗago kai daga bisani ya kuma yi arba da Nusi tana huci akansa.
''kada ka ƙara cewa idan nayi maka abu zaka biyani!!!
''Darasi na farko; babu irin wannan godiyar tsakanin ya da ƙani!''
Nan fa bayan ya gama saurararta ya dage abin da kyar, ya ƙaƙalo wani ɗan murmushi mai kama da yaƙe, amma acikin ransa kawai cewa yake, lallai tana da zafin nama, ko motsin tahowar abin nan banji ba!
Abu na gaba daya gani shi ne Núsí ta gama haɗa musu kayansu, kuma harta fito, inda ta cilla masa jakarsa ita ma ta rataye tata, gami da cewa, ''yafi kamata mu shiga cikin garin yanzu da daddare, saboda wasu dalilai.
Nan take suka fara tafiya su na gudu-gudu sauri-sauri a ƙasa inda suka nufi wajan hasken nan data nuna ɗazu, wanda shi ne ya kasance ɓangaren garin da zasu je.
''Garin da zamu shiga sunansa khan, kuma yana ɗauke da sama da mutane dubu ɗaruruwa. Amma kuma duk da haka shi ne mafi ƙanƙanta acikin garuruwa huɗu dake wannan ɓangare.
''Kuma sama da kaso casa'in na mutanen garin baƙi ne, wato dai ba ƴan ƙabilar Maikironomada bane.
''Amma kuma dukkanin wanda ya shiga garin amintacce ne a ma'aunin Maikironomada. Idan mun ƙarasa bakin ƙofar garin zaka fuskanci abinda nake nufi da hakan.
''Kasaka a ranka cewa amfanin shigarka garin nan shi ne, ka reni irin Izzarka, ta yadda kaima a hankali zaka zama ma'aboci Izza.
''Kaga a wannan lokaci, koda tsautsayi yasa wani ya gano kasancewarka magaji, zaka iya ɗaukar matakin daya dace, sannan kuma zai zamo ba kowa bane zaiyi mafarki gabato kaba da sharri.
''Ba kamar yanzu ba da ba wanda zaiji tsoronka ba.'' Ta kalleshi sama da ƙasa tamkar wacca take mamakin ya akai har yanzu yake raye.
Amma Armad ko a jikinsa, kawai kallonta yayi kuma yai dariya, domin ya riga ya gane cewa ƙoƙari kawai take, nata saka shi ya ƙara himma, da kuma kada ya sa ran mataki Izzarsa ta ishe shi a haka.
''Zanyi duk wata mai yiwuwa domin ganin ka samu duk wata dama data dace domin ƙarfafa maka gwiwa, ragowar kuma ya rage ya naka.
''A sanda kake bacci, tuni na tura saƙo ta Ayrid zuwa ga mutane na, kuma tuni sun kama maka layi na shiga Non-toch-teka! Saboda haka ka zama cikin shiri.''
To duk da yake wannan bashi bane karo na farko ba, daya ji kalmar Nin-toch-teka ba, amma jin cewa koma mene ne , wannan lokaci ya shafe kai tsaye, yasa yayi hanzarin yin tambayar, ''wai yaya, menene wannan abinne, waishi Non-toch-teka?''
Ta kalleshi kawai fuska cike da mamaki, sannan tace, ''hmmm.. bani da masaniyar meke wakana a doron ƙasa ta uku, amma a iya sani na duk wani mai Miyura yana da buƙatar Non-toch-teka.
''Amma karka damu, yanzu dai ka gane cewa wata hanyace da zata taimaka maka wajen sarrafa Negrinkin ka da kuma Fotenshiyal-sifes ɗinka, ragowar kuma saika gani da idonka.''
A dai-dai lokacin da tazo nan a zancenta suka fara hango katangar gari ta tashi sama, sannan kuma ga ƙatun ƙatun ɗin ƙofofin gari nan guda biyu suna kallonsu daga nesa.
Ɗaya baƙa ɗaya kuma yaluwa!
Tun daga nesa mutun zai iya hango ƙatun-ƙatun ɗin mutun mutumi nan guda shida manya-manya a bakin yaluwar ƙofar, sannan kuma guda ɗaya a bakin baƙar ƙofar.
Suna ƙara kusanta wannan ƙofofi suna ƙara girma da waɗannan mutun mutumi. Sannan kuma suka ga mutane a kan layi a bakin wannan baƙar ƙofar.
Sai dai kuma babu mai gadi, amma duk da haka waɗannan mutane dake bin layi a nutse suke babu ko ɗaya mai nuna alamun son yin rige ko kuma turereniya ko kuma hayaniya.
Kai duk da tsakiyar dare ne saika nutsu sosai zaka iya tsuntar magana ɗaya biyu.
Kafin ma su ƙarasa waɗansu mutane sanye da fararen kaya suka bayyana a gabansu.
Ɗaya fari mara jiki, mai kama da ɗan fulani, ɗaya kuma wankan tarwaɗa sannan kuma murɗaɗɗe.
Duk da fuskokinsu a sunkuye suke, amma zaka iya fahimtar cewa wankan tarwaɗar bazai yi barkwaci ba ko kaɗan ba kamar mai kamar ƴan fulanin ba, sannan bazaiyi magana sosai ba.
Mai kamar ƴan fulanin ya fara magana cikin ladabi, ''barka da zuwa yaya Núsí, da fatan kin iso lafiya.''
Fuskarta cike da murmushi ta amsa da cewa, ''Basharu, Kamálu, ba sai kun sunkuyar da kawunanku ba.'' Amma duk da haka bai sa sun ɗago kawunan nasu ba.
A saboda haka kawai ta girgiza kai tayi murmushi, gami da ajiyar zuciya, ''toh, da fatan na sameku lafiya.''
A wannan lokaci ne wani abu ya fara gayawa Armad cewa lallai Nusi babbar mutun ce acikin wannan gari. Nan fa ya fara tunanin wacece harda ake mata irin wannan ladabi??
Nan take su biyun suka juya gami da cewa, ''mun gama shirya komai, mu ƙarasa zuwa ciki.''
Nan take suka juya suka nufi wannan ƙofofi.
Tunda suka bayyana ƴan tsirarun mutanen dake tsaye a bakin baƙar ƙofar nan, suka waiwayo suke kallonsu.
Amma a ciki babu wanda ya gane su, da dama ma ɗauke kai sukai.
Amma can bayan wani lokaci sun ƙara kusantar katangar, sai kuwa ɗaya daga cikin waɗannan mutun-mutumi guda shida suka ya buɗe idonsa inda wani haske ya feso daga ciki ya nufo su.
Kafin kace meye wannan tuni, wajen da da yake shiru tsit, ya hargitse da hayaniya, ana nunosu da hannu.
Wannan haske bai tsaya ko ina ba, sai akan fuskar Nusi.
Yana taɓa fuskarta ya shuge ciki kuma ya ɓace ɓat.
Tamkar babu abinda ya faru, sai dai kuma a wannan lokaci idanun ta a rufe suke ruf.
Nan take suka nufi wannan yaluwar ƙofa gadan-gadan, inda suna isa Armad ya fara ƙoƙarin tsayawa domin a iya kallonsa babu hanyar wucewa, saboda waɗannan mutun-mutumi, amma bisa mamaki sai yaga sun wuce ta cikinsu tamkar ma babu su a wajan.
Saboda haka shima kawai yabi bayansu da niyyar wucewa.
Amma abu na gaba daya gani shi ne jini yana tsiyaya ta goshinsa, sannan kuma yana zaune a ƙasa zaman dirshen.
Ba komai ya jawo haka ba kuwa illa karo da yayi, da ɗaya daga cikin mutun-mutumin nan guda shida. Inda ya daki kansa, kuma kafin kace meye wannan ya fasa kai jini ya fara zuba, gami da faɗuwa ƙasa dirshen.
Ɗaya daga cikin abubuwan mamakai na wannan ƙabila ta Maikironomada shi ne, a tsahon shekaru da dama da suka gabata a bakin ƙofar kowanne gari, abu ne sananne cewa akwai manya-manyan mutun-mutumi, waɗanda yawansu ya banbanta tsakanin kowacce ƙofa daga cikin ƙofofin shiga garuruwan nan guda huɗu.
Misali a garin Khan, yaluwar ƙofa nada shida sannan baƙa kuma nada ɗaya.
Kuma duk da matuƙar kama da na gaske da waɗannan mutun-mutumi sukai musamman idan ka hangesu daga nesa, amma kowa yasan cewa ba na gaske bane, kamar hoto suke na magiji, tayadda zaka iya wucewa ta cikinsu kai tsaye ba tare kaji komai ba.
Waɗannan mutun-mutumi bawai dasu aka ƙirƙiri ƙofofin nan ba, a'a a hankali a hankali shekaru su na wucewa aka samesu.
Ta wata hanya wadda kusan duk wani ɗan ƙabilar Maikironomada ya sani, kuma yake burin shima ya isa wannan mataki.
Kai har amintattun baƙi ma daga cikin garin Khan suma su na burin kaiwa wannan mataki, duk da kuwa sanin cewa, kusan abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba, amma bazasu iya daina burin hakan ba har sai sun jisu a kabari!!
Alƙaluman da kowa ya sani su ne na mutumin ƙarshe daya saka mutun-mutumi ɗaya ya ƙaru daga na garin khan, wanda hakan yai matuƙar ɗaga darajar gabaki ɗaya garin har ya zuwa wannan lokaci.
Wannan ba kowa bane illa wani da ake kira da Bihanzin!
Kuma wanda ya ƙaru shi ne wannan guda ɗayan dake baƙin baƙar ƙofar, kasancewar a lokacin da zai fara shiga garin, ta wannan ƙofa ya shiga.
Abinda aka sani shi ne duk wanda ya samu damar fito da ɗaya daga cikin waɗannan mutun-mutumi alamu ne na cewa tauraruwar sa zata haskaka a duniya, saboda haka aka saka musu sunan Al'yaya.
Kalmar da a Aldurish( yaren Alderiya) take nufin maɗaukakin jarumi.
A dai-dai lokacin da Armad yaje ƙasa wani haske mai tsananin kashe ido, ya tashi sama gami da haskaka sararin samaniya.
Sannan kuma tamkar wanda yake son ya tabbatar kowa acikin garin ya tabbatar da meke faruwa, ya nausa bayan gatangar ya kuma shiga cikin garin, inda kafin kace meye wannan tuni ya haskaka kowannna loko da saƙo na cikin garin.
Kafin kace meye wannan tuni hayaniya da ruɗani ta fara tasowa daga cikin wannan gari.
A dai-dai wannan lokacin su Nusi suka ƙarasa juyowa wajen Armad wanda ke zaune a ƙas, jini na ɗisa ta cikin jan ƙyallen daya ɗaure goshinsa.
Nan take ba tare da wani jawabi suka fara ƙoƙarin rufewa Armad fuska, kasancewar tuni ƴan tsirarun mutanen da ke tsaye a bakin baƙar ƙofar nan suka fara azama wajan isowa wajan domin su ganewa idonsu wanene ya zama ƙara zama Al'yaya.
Acikin garin kuwa a wata fada wasu mutun uku ne suka bayyana, dukkaninsu daga ka kallesu zaka ga cewa fuskokinsu a ɓace suke.
Suna sanye da alkyabba iri ɗaya mai ruwan baƙi da yalo, tamkar ƙofofin wannan gari.
Kai idan kallesu sosai ma zaka iya hasashen cewa muƙaminsu ɗaya ma.
Nan take ɗaya daga cikinsu ya ce, ''wannan ƙabila.....''ya ƙara cije haƙora sannan ya kwalla, ''Djinn!!
''Kamar bai isheta ba dawowar da tayi ba, amma saita taho wani, kuma waninma irin wancan wancan mutumin.... Bihanzin!''
Ɗayan ya ce, ''yanzu dai meye abinyi, domin idan bamuyi da gaske ba, to abinda ya faru da Bihanzin Djinn shekaru ashirin da biyar da suka wuce, zai ƙara faruwa da wannan yarinyar, Núsí Djinn''
Comments
Post a Comment