Skip to main content

Babi na Ashirin

MAGAJIN WILBAFOS na A M IBRAHIM

Babi na Ashirin : MAGAJIN WILBAFOS

Minti ɗaya da daƙiƙa ashirin kafin rufewar idon Armad.

Tafiya yake yana dube-dube hagu da dama,  badan komai ba sai dan irin kyawun muhalli da yaga wannan ƙauye nada shi.

Duk da cewa wannan ƙauye bashi da girma, amma duk inda ka duba akan hanyoyinsu sunyi shuka ta korayen tsirrai masu sanyaya ido.

Sannan kuma ga filawowi masu launi daban-daban ko ina ka kalla.

Armad bai san mai yasa ba, amma yana shiga wannan ƙauye yaji hankalinsa yayi matuƙar kwanciya tamkar tsumma a randa.

Wani farin ciki da baisan daga ina yake ba ya fara lulluɓeshi.

To yana cikin wannan hali ne idanunsa suka kai ga kan wata ƴar takarda mai launin ja, kuma tana da matsakaicin faɗi.

Acikin wannan takarda akwai ɓangarori guda uku; na farko yana magana kamar haka-

Tarifil-fakta mutun ne mai tsananin hatsari ga zaman lafiyar al'umma.
Saboda haka maɗaukakiyar masarauta take tabbatarwa da jama'a su kwantar da hankulansu domin zatai duk wata mai yiwuwa wajen ganin cewa an kama shi.

Ɓangare na biyu kuma yana magana ne akan kyaututtukan da aka tanada ga duk wanda ya kawoshi ko kuma ya samarda jawabi daya taimaka aka cimmasa, kamar haka-

Duk wanda ya kamoshi ko kuma ya bayarda wani bayani daya taimaka aka cimmasa, to yana da waɗannan kyatuttuka;
1-Za'a ɗaga darajarsa data ƙabilarsa zuwa doron ƙasa ta farko!
2-Za kuma a bashi mafificin muƙami a wannan ƙabila kowacce ce!
3-Za'a ƙarfafa ruhinsa dana zuriyarsa da ɗaya daga cikin huɗu na Izzan dake Maɗaukakiyar masarauta!

Ɓangare na uku kuma yana bayani ne akan alamonin yadda za'a gane shi;

Yana da tambarin Miyura a goshinsa madauwami, wanda baya taɓa ɓacewa.

A kewaye da wannan tambarin akwai hoton wata guda uku; ɗaya daren tara, na biyun daren sha takwas sai kuma na ƙarshe daren ashirin da bakwai!

Waɗannan watannin guda uku su na motsawa tamkar masu rai, inda suke kewaye wannan Miyura!

Ga hoton wannan Miyura!

Sai kuma daga ƙasa aka bayarda hoton Miyurar da ake magana akai!

Ɓangare na ƙarshe kuma yana ƙunshe da sa hannu na sarki bisa doron ƙasa ta biyu, wato Dul'Ururu.

A gabansa kuma kaɗan akwai alamun fuska, wadda ba abinda ake gani acikinta face ɓaƙaƙen idanuwa guda biyu.

Waɗanda idan ka kula sosai zaka ga wasu lokutan idan wani yazo yana karanta wannan takarda suna motsawa su kalleshi.

Sai dai kuma ba kowa ba, domin wani ko mai duban da zaiyi ba zasu taɓa nuna alamun motsi ba, tamkar ma babu wanda ke wajan.

Sai kuma wani lokaci da idanun suke motsi shi ne, idan wani yazo yai magana a gabansu cewa yana da bayani akan Tirifil-fakta, to su na motsawa su kuma kalli cikin idanun mutun.

Kuma kamar yadda kowa ya sani, a gaban waɗannan idanu baka da buƙatar ka mayarda bayaninka zuwa kalmomi, domin kallo ɗaya kacal suke da buƙatar suyi maka su zaƙulo wannan bayani daga cikin kwakwalka ba tare ma ka sani ba.

Abu na ƙarshe a jikin wannan takarda shi ne tambari mai ɗauke zanen ƙasa bakwai wanda a samansa yake da hoton fada.

Wannan ba wani tambari ba ne, illa na maɗaukakiyar masarauta.

To ko mai yasa idanun Armad suka rufe ruf, kuma duk da ya sa hannu amma ya kasa buɗe su.

Abinda ya faru shi ne, Armad na zuwa ƙarshen wannan takarda bayan ya gama karanta jawaban saman, kuma tuni ya ƙara fahimtar abinda Núsí ta gaya masa akan girman al'amarin daya ɗauko da kuma kaɗan daga cikin wane ne Tarifil-fakta. Sai idanunsa suka nufi kan ɓangare na ƙarshe a jikin wannan takarda, wanda ke ƙunshe da alamun wannan fuska da kuma waɗannan baƙaƙen idanu guda biyu.

Amma a wannan lokaci ne, ya ji kawai idanunsa da kansu sun fara rufewa da kansu, kuma kafin yayi wani abu yaji suna ƙoƙarin rufewa su kaɗai.

Nan take ya fara ƙoƙarin rufe su, amma ina.

A wannan lokaci ne yaji tamkar wata Izza mara iyaka ta taso daga jikin wannan mutun-mutumi dake cikin tambarin Miyura dake goshinsa,ta ƙarawa idanun nasa sauri, inda cikin ƙiftawar ido suka rufe ruf.

Sannan kuma wannan Izza ta kewaye su, gami da tabbatar da cewa sun zauna a rufe.

Armad bai yadda da abinda ke faruwa ba, saboda haka nan take ya fara ƙoƙarin buɗe idon nasa.

Amma ina ko motsi basuyi ba.

Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne iskar dake kewaye da wannan baƙaƙen idanu a jikin wannan takarda ta kaɗa. Wanda nan take duk da cewa idanun Armad a rufe suke ya fara jin wata irin Izza wadda tunda yake a rayuwarsa bai taɓa jin irinta ba ko da a mafarki kuwa, ta fara tashi daga wannan idanu.

Kuma inda idanunsa a buɗe suke da yaga abinda Núsí take gani baki a buɗe a wannan lokaci.

Domin kuwa wannan idanu sun fara fitarda wani baƙi hayaƙi, wanda kafin kace meye wannan ya cika wannnan waje ta yadda da kyar kake ganin waye a gabanka.

Kafin kace meye wannan kusan dukkanin mutanen wannan ƙauye sun firfito daga gidajensu cikin firgici, kasancewar sun san cewa indai wannan idanu suka fara fitar da hayaƙi to yana nuna cewa kenan akwai sanarwa ta musamman daga maɗaukakiyar masarauta.

Tuni wannan baƙaƙen idanu suka fara sheƙi, suna ƙara baƙi.

Kafin kace meye wannan tuni wannan ƙauye ya fara duhu duk kuwa da cewa rana ce tsaka.

Tamkar baƙaƙen idanuwan suna zuƙe haske gaba ɗayan ƙauyen ne!

Bayan kimanin daƙiƙa talatin, sai kawai suka ga wannan hayaƙi ya fara tattaruwa yana dunƙulewa a waje ɗaya.

Kafin kace waye wannan ya haɗe a waje ɗaya ya dunƙule, inda nan take ya fara juyawa da ƙarfin gaske, ta yadda idan ka fiya ƙura masa ido kaima sai kaji kanka ya fara juyawa.

Cikin daƙiƙa bakwai wannan hayaƙi ya rikiɗe ya koma siffar ƙararrawa.

Baƙar ƙatuwar ƙararrawa, wadda idan ka ɗaga kai, sai kaga tamkar ta rufe dukkanin sararin samaniya.

A dai-dai wannan lokaci tuni Núsí ta isa kan Armad wanda tuni abinda ke faruwa a cikin kwakwalwar sa yasa yama daina ƙoƙari buɗe idon nasa, ya tsaya kawai jikinsa yana karkarwa.

Dukkanin abubuwan dake faruwa, idanun Armad a rufe suke, saboda haka bai san da dama daga abubuwan dake faruwa ba.

Sai dai kuma shima acikin ruhinsa yana ganin abinda babu wanda yake gani saishi.

Acikin kwakwalwar tasa yana ganin wata duniya ce ta musamman, inda yake tsaye kamar matacce, wannan hayaƙi dake tashi daga wannan baƙaƙen idanu guda biyu yazo ya fara ƙoƙarin buɗe idon nasa ta ƙarfin tsiya, tamkar wanda rayuwarsa da samuwar sa ya wanzu akan wani abu dake cikin idanun na Armad.

To amma kuma a wannan lokaci ne wannan mutun-mutumi da hotonsa ya bayyana acikin kwakwalwar Armad wanda ke ƙoƙarin hanashi buɗe idon nasa ya ɗaga hannunsa inda wata doguwar takobi, wadda takai tsayinsa ta bayyana aciki.

Wanda kuma nan take yayi kan wannan hayaƙi da sara. To sai dai kuma a dai-dai lokacin ne wannan baƙin hayaƙi ya juye izuwa halitta mai kai tara.

A jikin kowanne kai akwai baƙaƙen idanu guda biyu, wanda hakan ya sa baƙaƙen idanu guda gima sha takwas suka bayyana.

Armad dai na tsaye acikin wannan duniya kamar ɗan kallo,  mahaukacin azababben yaƙi ya kaure.

Dukkaninsu daga ita wannan halittar, har shi mutun-mutumin babu wanda hotonsa ya fita sosai yadda Armad zai gane kamanni sosai, amma duk da haka yana jin irin ƙarfin tsananin tsana da azabar yaƙi ta har abada dake tsakanin sifofin guda biyu.

A waje kuma acikin duniyar mutane, Núsí tana tsaye tana ta ƙoƙarin farkar da Armad, amma ina, baya ko alamun jinta, kuma har wannan lokaci idanunsa a rufe suke.

Nusi na tsaye inda a dai-dai lokacinda wannan ƙararrawa ta gama haɗuwa ta ɗaga kai sama, kuma ta samu cewa bisa mamaki ƙararrawar tana dai-dai samanta.

A saboda haka nema dukkan mutanen wannan ƙauye da suka firfito, idan suka ɗaga kansu sama suka kalli wannan ƙararrawa sai kuma su saukar da kai kuma su dubi su Armad domin ganin mai ke faruwa.

Wanda kuma, abinka da ƙauye kowa yasan kowa, saboda haka nan take maganganu suka fara tashi ana nunosu ana cewa baƙi ne suka shigo.

Wannan abu dake faruwa bai ɗau hankalin mafi yawa daga cikin jama'ar ƙauyen ba, domin da dama har a lokacin kansu yana kan wannan ƙararrawa kuma su na jira su ji wane bayani ne zai sauka daga maɗaukakiyar masarauta a wannan lokaci.

To kowa dai yana tsaye yayi kasake, wasu kuma hankalinsu nakan Armad wanda suke tunanin mai yasa ya rufe idonsa.

Wasu ma tuni sun fara tunanin ai makaho ne, amma daga bisani daga bisani suka ƙara ƙura masa ido suka ga kwata-kwata baiyi kama da makahon ba.

Sannan kuma akwai wasu jijiyoyi a zagayen idanun nasa dake ƙara kumbura wanda ke nuna alamun cewa idanun nasa da ƙarfi aka rufesu, wato bashi ya rufe su ba.

Ana cikin wannan hali ne, ƙararrawar nan tai ƙara sau ɗaya, wanda hakan yasa duk mutanenda ke wajen suka zube akan gwiwowinsu.

Hatta Núsí sai da ta zube ba tare da ta sani ba, tamkar wadda bata da iko da jikinta.

To amma wani abu wanda yasa dukkanin mutanen wajen suka maida hankalinsu kan Armad cikin mamaki, shi ne ko kaɗan Armad bai durƙusa ba.

Hasalima hatta Nusi da taga mutane nata kallonsa, saida ta fara ƙoƙari fizgarsa dan shima ya durƙusa amma ina, tamkar wanda take jan bishiyar kuka.

Wannan ƙararrawa ta ƙara kaɗawa ta biyu, inda wata murya mai ɗauke da wata irin irin Izza wadda ke tursasawa kunne sauraro kuma ta tursasawa kwakwalwa fahimta ta fara jawabi, ''sanarwa zuwa ga dukkan ma'abota dukkan ma'abota ƙasashen ƙasa.

''Wani Magajin Wilbafos ɗin ya sake bayyana.

''Yana da tambarin Miyura mai tsarin dauwama a goshinsa.

''Mai irin wannan tsari'' Wannan murya na furta haka, sai hoton wannan Miyura da take nufi ya bayyana acikin ruhin dukkan wani mutun da yaje sauraron wannan magana.

''Wannan wata dama ce ga dukkan wani mai so ya cimma Tarifil-fakta, ku kamashi kuyi amfani da jininsa.''

Tana faɗar haka sai tayi shiru, sannan bayan ƴan daƙiƙu ta ƙara kaɗawa inda dukkanin al'ummar dake wajen hankalinsu ya dawo jikinsu.

Nan take suka mimmiƙe, idanunsu cike da mamakin abinda suka ji.

''Magajin Wilbafos........

''Magajin Wilbafos.... maike faruwa...

''Wane ne wannan...ai koma wane ne dai an kamashi an gama." Nan take mutanen wannan gari suka fara tattaunawa a tsakakninsu.

A can gefe wasu dattijai guda uku suka numfasa tare da fara  fara jawabi, ''Yanzu bayanin shi ne wane ne zai fara cimmasa...domin kuwa duk wanda ya kama wannan magajin Wilbafos ɗin, lallai ya samu wata dama musamman ta kama Tirifil-fakta.

''To amma kuke tunanin shi wannan magajin bashi da ƙarfin Izza, domin kuwa na tabbata indai tarihin da yazo a littattafai akan zuriyar Wilbafos haka ne, to fa lallai jarumin gaske ne kaɗai zai iya zama magajin wannan gida.

''A'a, ai ni ina gani cewa komai ƙarfinsa, to fa lallai kamar an kamashi ne an gama, domin ko waye shi babu tayadda za iya da dukkanin miliyoyin al'ummar jaruman dake son kama Tirifil-fakta, dan ni idan ni ne shima, kawai zan miƙa kaina ne kawai.''

To waɗannan dai sune kalamanda al'ummar wannan ƙauye suka fara tattauna hankulansu na dawowa jikinsu.

Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne wannan ƙararrawa bayanda ta baje, ta ƙara komawa wannan hayaƙi, shi kuma ya dunƙule waje ɗaya inda ya rikiɗe izuwa siffar wani hannu mai girman gaske, wanda ke a rufe da baƙin gashi.

Wannan hannu yana bayyana ya nufo Armad da saurin gaske a buɗe, tamkar wanda ke ƙoƙarin ƙwaƙule masa ido.

Kafin wani yayi wani abu tuni wannan hannu ya isa gabda idanun Armad, kuma yana gabda taɓa su.

Amma a dai-dai wannan lokaci ne wata iska ta bayyana ta daki wannan hannu, inda yayi sama izuwa goshinsa.

Kafin kace meye wannan yayi sama inda ƙarfin wucewar tasa ta cire jan kyalle da Armad yake amfani dashi wajen ɗaure goshinsa.

Nan take tambarin Miyurar dake goshin Armad ya bayyana ƙarara.

Kafin kace meye wannan jama'ar wannan ƙauye sun fara ajiyar zuciya, babu abinda kake ji illa, ''wannan Miyura dake goshiɓ wannan yaro... kai..... Ai.... Ita ce...

''wannan Miyura.....ai...ita yanzu aka nuna mana a jawabin nan....

''Kar dai ace......wannan yaro.....shi.....ne...

"shi....ne!!!"

***
To fa, shi ne wa?? Waye zai canka

Comments

Post a Comment

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...