Skip to main content

Babi na sha takwas : Mutumin da yafi kowa Yawan Makiya

MAGAJIN WILBAFOS na A M Ibrahim

Babi na sha Takwas : Mutumin daya fi kowa Yawan maƙiya (Tarifil Fakta)

Núsí ta kalleshi kallo mai zurfi, wanda acikinsa akwai alamun tausayi, tsahon daƙiƙa goma, kafin daga bisani ta fara wata dariya mai matsakaicin sauti, kai daka ji kasan akwai tsananin ciwon rai acikin wannan dariya.

Kana daga bisani ta numfasa tace, ''Mangwaron Negrinki!

''Zaka sha wahala matuƙa, kuma abu nema mai kama da samun jaki mai ƙaho, kafin ka sami wani abu guda ɗaya dake da muhimmancin Mangwaron-Negrinki wajen ƙarfafa ruhi da inganta Izza, kai hasali ma akwai hikayoyi da dama da suka rawaito cewa idan ka samu adadi mai kyau ka kuma yi amfani dasu ta yadda ya dace, to zaka iya tashin matacce daga kabari da ƙarfin sihirin wannan mangwaro.

''Hakan nema yasa mallakar wannan mangwaro abu ne mai tsananin wahalar.

''A misali; a sama da shekaru goma da nayi a birnin Maikironomada nayi ayyuka na kwadago da dama kuma na samu dukiya dai-dai gwargwado.

''Amma a lokacin da zan fito wannan jarrabawa wadda nasan bazata taɓa yiwuwa ba idan mutun bashi da wannan Mangwaro ba.

''A saboda haka na tattare dukkan tari na, na tsahon rayuwa ta dan na sayi wannan mangwaro, amma a ƙarshe ban iya mallakar sama da guda biyu ba.

''Bayan zuwa na nan wurin acikin shekaru uku da nayi anan, na ƙarar da guda ɗaya aciki.

''Saura guda ɗaya, wanda kuma shima yanzu babu.

''A duk lokacinda kake fafatawa wajen ƙoƙarin wuce wannan hijabi idan ka samu rauni, to fa baka da wata hanya mafi sauƙi face kayi amfani wannan mangwaro, wajen warkar da ciwon naka.

''Babban sharrin sinadarin Negrinkin dake wajen nan, shi ne ciwon da yake yiwa jiki baya warkewa da wuri, ɗan ƙarami ma yakan ɗauki shekaru da dama.

''Amma da taimakon wannan mangwaro zaka iya rageshi zuwa kwanaki.

''Dukkan waɗannan dalilai ne suka sa babu ta yadda wani mahaluƙi, zai iya wuce waɗannan wannan mataki ba tare da wannan mangwaro ba.''

Tana zuwa nan a zancanta ta girgiza kai gami da cize haƙora tana cewa, ''naso na fita daga wannan waje.

Armad ya ƙura mata ido yana sauraren ta cikin mamaki.

Tun kafin tazo nan a zancenta Armad ya gama haɗa lissafin duk abinda ke faruwa, kuma ya gane inda ta dosa; wato wannan abu daya ji a bakinsa ba komai bane illa mangwaron-negrinkin nata guda ɗaya daya rage.

Kuma wannan yanayi na ɗebe haso daya bayyana a fuskarta ba komai ya jawoshi ba, illa rasa wannan mangwaron sihiri da tayi.

Bayan ya gama fahimtar komai, sai nan da nan yaji kyautayi da ƙaunar wannan budurwa ta shiga ransa. Irin ƙaunar dake zuwa rai ga wanda ya taimake ka a lokacin da kafi buƙatar taimako.

Armad yana wannan tunani ne hankalinsa a kwance, babu ko alamun ayar tashin hankali a tattare dashi.

Duk da kuwa duba da cewa babban abinda yafi ɗagawa ita Núsín hankali shi ne rashin hanyar da zasu fita daga wajen.

Hakan nema yasa ta dago kai ta dubeshi idanu cike da mamaki, tayadda duk da bata ce komai ba ya bayyana ƙarara a idonta cewa mamaki take da hankalin Armad bai tashi ba duk da cewa kuwa ta gaya masa a fili cewa basu da hanyar fita daga wannan waje.

Armad yai murmushi gami da cewa, ''kamata yayi a mayarda alkhairi da alkhairi, wato ina nufin baki sanni ba amma kin yarda dani kuma harkin sanar dani labarinki.

''Nima ina ganin ya kamata na gaya miki dukkan labari na a zahiri, kuma ina baki haƙuri dana ɓoye miki a baya.''

Nan fa Armad ya kwashe dukkan labarinsa tun daga dalilin fitowarsa daga doron ƙasa ta uku har ya zuwa sanda suka haɗu dasu Zahra da kuma yadda ya ƙare a wannan waje.

Sai dai kuma abu ɗaya; duk da haka bai gaya mata tsakaninsu da Masanin-ƙasa ba dangane da sunansa na gaskiya ba.

Ya kula sosai wajen labarinsa, tayadda shidai bai ƙara yi ƙaryar sunansa ba, amma kuma bai gaya mata sunansa Wilbafos ba! Kawai yai shiru yabar wajen a haka.

Ita ma kuma, tunda ta fuskanci baya son maganar, sai kawai ta share.

Wani abu da Armad ya kula dashi shi ne, tunda farko daya ambaci sunan Tirifil-fakta fuskarta ta canja sosai, sai dai tunda batai magana ba shima bai ce mata komai ba, kawai ya ci gaba da zayyana labarinsa.

Bayanda ya gama sai yai shiru inda ya kalli gabansa dai-dai wajen wannan hijabi.

Ya dubi Núsí da niyyar ya tambaye ta me ake buƙata mutun yayi kafin ace ya wuce wannan waje, amma kafin yayi magana yaji muryarta tana cewa, ''Tirifil-fakta......!!!

''Lallai kana da ƙarfin aniya.... amma shin kasan meka ɗaukowa kanka kuwa!'' Tayi shiru gami da ajiyar zuciya tana kallon Armad cikin mamaki.

Can bayan daƙiƙu ta ƙara numfasawa tace ''Bazan kashe maka gwiwa ba, amma abu ɗaya daya kamata ka fara sani akan wannan alamari shi ne; babu wani mahaluƙi, rayayye ko matacce, tun daga kan doron ƙasa ta farko harya zuwa doron ƙasa ta bakwai daya kai mai wannan suna yawan masu so su cimmasa.

''Wasu maƙiya wasu masoya. Babu wanda yasan daɗewar wannan suna a doron ƙasa babu kuma wanda yasan wanene ko kuma ya yake. Kai hikayoyi da dama ma sun rawaito cewa daɗewar sunan tamkar daɗewar ƙasashe bakwai ne.

''An rawaito a mas'alolin farkon lokaci, cewa shi shi kaɗai ne mutumin da Ma'abota Ururu suka taɓa saka kyauta ga duk wanda ya kamo ko kuma ya bayarda wani bayani daya kai aka kamashi.

''Kimanin shekaru ashrin da suka wuce Dul'ururu ya saka hannu kan dokar kyauta akansa.

''Kayi sani cewa a halin yanzu zaka iya cewa duk duniya babu wani mahaluƙi kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba, yana sane ko kuma baya sane, da baya neman mai wannan suna.

''Da dama su na nemansa ne saboda kyautar da za'a Bawa duk wanda ya kawo shi, ko kuma kawai ya bada wani bayani daya taimaka aka iya cimmasa.

''To, zata iya yiwuwa wasu su na da tsohuwar ƙiyayya, wasu kuma akasin haka, amma dai a zahirin gaskiya zaka iya cewa mutanen da suka san Tirifil-fakta ko kuma wani abu muhimmi akansa ƙalilan ne, domin har sunfi adadin jaki mai ƙaho yawa.''

''Shin yanzu ka fahimci wa kake nema?'' Ta rufe jawabinta da tambaya.

To a wannan lokaci bayan ta gama duk wannan jawabi Armad na tsaye yana kallonta, wanda a sannan ne ya bata amsar da bata taɓa tsammani ba.

Inda yayi murmushi gami da cewa, ''ba matsala, kawai yana nuna ina da buƙatar na fi ƙarfin duk ragowar masu neman nasa ko?''

Fuskarsa cike da murmushi ya ci gaba da cewa, ''ta yaya ake wuce matakin wannan jarabawa?'' Ya tambaya ya na nufat gurin wannan hijabi cikin sauri da kwanciyar hankali tamkar wanda zai shiga cikin ɗakinsa.

Sai dai kuma a wannan lokaci ne Núsí wadda tun amsar daya bata bakinta ke buɗe cike da mamaki, ta taso da sauri inda ba tare da cewa komai ba ta riƙo hannunsa da sauri a dai-dai lokacinda yake ƙoƙarin miƙa hannu cikin wannan waje.

Ta janyoshi da ƙarfin tsiya inda har saida yayi taga-taga gami da yowa baya kamar zai faɗi.

Tun kafin Armad ya gama nutsuwa ya fara magana cikin mamaki, ''aargh.. Yaya?''

Nan take ta rufeshi da masifa, ''kasha giya ne! hannuka yana taɓa wancan waje zaka ƙara shiga yanayin daka shiga ɗazu.

''Dama gashi bawai gama farfaɗowa kai ba.

''Kuma nidai bani da wani abu daya rage dazan iya ceto ka idan haka ta faru.

''Saboda haka ya kamata ka nutsu, mu zauna muyi tunani akan mai ya kamata muyi.''

Har a lokacin da take magana Armad idonsa na kafe akan wannan waje.

Shi dai waje ne wanda babu wani abu ban tsoro a tattare dashi ko kaɗan.

Kai hasali ma babu komai face dai kawai tamkar wani layi ne aka sa aka raba tsandaurin ƙasar zuwa gida biyu; ɗaya, inda su Armad ke tsaye, ƙasar nada launin ruwa ƙasa kamar a ko'ina, sai kuma ɗan rairayi daya rufe ta, ɗaya kuma wanda ke gabansu shi ma fili ne kawai kamar na farkon, sai dai kawai ƙasar wajen launinta na musamman ne, imda take da launin ja mai gauraye da shuɗi.

Wannan kala ta ja-da-shuɗi ta ɗau haske sosai, inda har kyalli take tana zubarda haske inda ya maida iskar dake yawo a saman ƙasar irin kalar.

Aƙa'ida duk wani tsarar Armad daya kalli wannan waje ya kamata yaji nauyi yana tashi acikin zuciyarsa, kamar yadda ita ma Núsí take ji.

Amma abinda bata sani ba shi ne Armad baya jin komai ko kaɗan daga kallon wannan waje, kuma hasalima ji harga ALLAH shi ji yake acikin ran nasa tamkar ɗakin nasa zai shiga.

Bayan Armad ya gama kallon wannan waje, bai bata amsar duk maganganun da tai masa ba, sai kawai ya dubeta, gami yi mata murmushi, wanda ke ƙunshe da godiya na kula da take nuna masa.

Amma gama murmushi keda wuya, shi kansa bai san mai yasa ba, kawai yaji tsananin soyayyar ya tashi ya shiga wannan wuri, tamkar wanda wani abu acikin wajen yake kiransa.

Armad ya ƙara juyawa ya kalleta gami da cewa, ''bari na gwada, sau ɗaya kurum, idam baiba, saimu canja wata shawarar!''

Tayi niyya, kuma harta buɗe baki domin gaya masa wani abun, duk don ta gaya masa cewa bazai yiwuba, amma ina kafin ma tayi wani abu tunu Arnad ya kwace ya nufi wannan guri gadan-gadan, tamkar wanda ake jansa.

Nan take ta miƙe ta kuma bishi, amma kafin ta cimmasa tuni ya afka da ƙafafunsa biyu cikin wannan waje!

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...