MAGAJIN WILBAFOS Na A M IBRAHIM
Babi na Ashirin da ɗaya : Ayrid mai keken doki
Nan take kace-nace ya ɓarke tsakanin al'ummar wannan ƙauye, ''hmmm... wannan yaron.. Ƙardai ace shi ne Magajin Wilbafos ɗin?" Inji wani ɗan saurayi daga cikin mutanen garin.
Sai dai kuma amma wani dattijo daga gefe najin haka ya waiwayo a fusace ya dubi wannan saurayi tare da cewa, ''Ah haba dai, kai kasan matsayi da ƙarfin Izzar waɗanda suka taɓa hawa kan wannan muƙami kuwa, ku dubeshi fa.... Izzarsa fa bata fi hamsin ba, haba dai."
Nan take saurayin yai ajiyar zuciya, ''Hmmm.... hakane, to amma kuma ai wannan Miyurar dake goshinsa ita ce sak irin wadda aka nuna mana yanzu."
Dagacin wannan gari najin wannan magana da suke tattaunawa ya tari numfashinsu tare da cewa, ''To koma dai menene wannan shi ake cewa tsuntsu daga sama gashasshe.
''Wannan ƙauye namu Kanwa, lallai kyauta ce daga ALLAH, saboda haka ni ina ganin kawai mu kamashi, mu siyarwa da ɗaya daga cikin manyan ƙasashen nan na arewa. Nasan ko shi ne, koma bashi bane, lallai zamu samu kyauta mabayyaniya.
''Sannan kuma koda ya zama bashi bane ba aiba komai. Ko ba komai baza muyi dana sani ba, idan ya zama shi ne kuma muka bari ya suɓuce mana.''
Wannan sune maganganun da waɗannan mutane acikin wannan ƙauye suke tayi, idanunsu cike da buri da haɗama.
Kafin kace meye wannan tuni da dama daga cikinsu sun cimma wannan matsaya, inda kafin kace meye wannan tuni sun fara matsowa kusa dasu Núsí da Armad wanda yake tsaye cak ko motsi bayayi, idanu a rufe.
A wannan lokaci, duk abinda ke faruwa Nusi na kallo, kuma babu abinda yake juyawa acikin kanta banda lissafin yaya zata fitar dasu daga wannan hali.
Domin komai a fili yake a gareta cewa kowanne mataki ta ɗauka, to shi ne zai zama ƙaddarar wannan yaro, saboda baima san inda kansa yake ba a halin da ake ciki.
Tai tunani cewa lallai wannan yaro duk da ta gama gaya masa labarinta dalla-dalla, yadda bata taɓa gayawa wani ba, amma duk da haka bai yadda da ita ba.
Hasalima bama a rashin yadda abin ya tsaya ba, a'a sai ƙarya da ɓoye-ɓoye kawai yake mata, wata bayan wata; misali tabbas ta gamsu zuwa wannan lokaci cewa sunansa ba Djinn bane, amma yaƙi gaya mata na gaskiyar, yama share shancen.
Sannan kuma ga al'amarin tambarin goshinsa wanda shima bai gaya mata ba!!
Saboda haka tayi tunanin cewa abu mafi dacewa da zatayi shi ne ta rabu da wannan yaro tayi hanyarta.
Ta haka kaga bata janyo kanta cikin wannan husuma data shafe shi ba.
To amma duk da wannan tunani, zuciyarta taƙi amincewa da hakan. Kuma abinda take gaya mata shi ne lallai ya kamata ta taimaki wannan yaron duk da kuwa zuciyar tata tana da yaƙinin cewa babu wani alkhairi da zai fito daga wannan mataki.
To komai dai ɗan lokaci ne, domin tasan lallai tana da buƙatar ta yanke shawara cikin zafin nama kafin waɗannan mutane su cimmusu, in ba haka ba kuwa dukkansu lallai halakarsu tazo, domin babu tayadda zata iya da dukkan mutanen ƙauye guda ita kaɗai.
Bata san mai yasa ba, sannan kuma bata da wani dalili mai ma'ana acikin ranta, amma kawai cikin tsananin zafin nama ta miƙa hannu inda ta cafe wannan jan kyalle wanda tunda ya fizge daga kan Armad yai sama kuma sai a wannan lokaci yake faɗowa.
Tana fizgarsa kawai kanta tsaye taja hannu Armad da ƙarfin tsiya da niyyar su ɓace daga wajen.
Amma ina, ko motsi baiyi tamkar an kafeshi a wajan saboda haka ita ma ja birki.
A dai-dai wannan lokaci, suma waɗannan mutanen garin da suka ga tana ƙoƙarin guduwa sai suka ƙara sauri, inda suka fara gudu domin su cimmusu.
Kai hatta waɗanda da basu motsa bama, saida suka nufosu, wasu da makami wasu babu. Kafin kace meye wannan tuni baifi saura taku biyu ba a tsakaninsu ba.
Nan take wani tunani ya ƙara gilmawa ta zuciyar Nusi, cewa idan har mutun yayi niyyar yin abu, toai kwanda yayi shi da cikakkiyar niyya, ko kuma kawai a haƙura.
Wannan tunani yana gilmawa a zuciyarta, kawai ta zira hannu cikin mayafinta, inda ta zaro irin Ayrid daga ciki, wanda ya kasance yana da kala ruwan ƙasa, sannan kuma girmansa yakai kimanin rabin babban ɗan-yatsa. Kallo ɗaya kacal zaka san cewa na musamman ne.
Tana fito dashi ba tare da ɓata lokaci ba, ta sakeshi ya nufi ƙasa.
Yana taɓa ƙasa ya nutse, wanda hakan na faruwa wani ɗan ƙaramin keken doki ya bayyana a dai-dai inda Ayrid ɗin ya nutse.
Yana bayyana ya fara ƙara girma, kuma kafin ƙiftawar ido da bismilla ya kai taku ɗaya, inda ya maye gurbin ƙasar da su Nusi ke kai, wato suka zamanto tamkar acikinsa suke.
Nan take Nusi ta haɗa hannayenta guda biyu, inda ta furta wasu ɗalasimai.
A lokacinda mutanen garin nan suka ga wannan keken doki na faɗaɗa sai suka fuskanci lallai idan basuyi da gaske ba, to fa lallai tsuntsunsu daga sama gasasshe zai guje musu.
Saboda haka sai suka fara jefa makaman dake hannunsu domin raunata su, a ƙoƙarinsu na su hanasu guje musu.
A dai-dai lokacinda wasu masu suka kusa cimmusu, ita kuma Nusi take ƙoƙarin karesu, sai kawai wannan keken doki ya fara haske.
Kaɗan da kaɗan ya fara, amma kafin kace meye wannan tuni ya cika wajen, tayadda wannan mutane basa ko iya ganinsu Armad.
Wanda hakan yasa dole suka ci birki, gami da kewaye dukkan wajen da niyyar hasken na ɗaukewa suyi taron dangi, wajen cafke su Nusi.
Amma haƙarsu bata cimma ruwa ba, domin kuwa bayan daƙiƙa uku hasken ya fara raguwa, kafin daga bisani ya ɗauke baki ɗaya.
Inda sukai arba da fili kawai, babu su Armad babu dalilinsu.
***
Shi dama Armad bai san inda kansa yake ba, saboda har yanzu bai san abinda ke faruwa ba.
Amma ita kuwa Nusi tunda hankalinta nanan, kasancewar kuma wannan lokaci shi ne na farko data taɓa yin amfani da irin wannan fasaha, saboda haka tasan menene amfaninta amma bata san menene hatsarin amfani da ita ba.
Shi dai wannan Ayrid ɗin data fito dashi, malaminta tane ya bata shi saboda da ɓacin rana, kuma kamar yadda taji ana amfani da shi ne wajan yin tafiya mai nisan gaske a lokaci ɗaya, a lokacin da mutun yake fuskantar hatsari.
Saboda haka ta ajiye da niyyar yin amfani dashi wataran idan ta shiga babban hatsari a rayuwarta da baza ta iya guduwa ba.
Amma bisa mamaki gashi tayi amfani dashi a wani yanayi da ba wannan ba.
Abu ɗaya data ayyana a ranta lokacin da take lazimta wannan ɗalasimai shi ne garin Maikironomada.
Saboda haka wannan Ayrid mai sifar keken doki ya ɗaukesu zuwa can, inda ya watsar dasu a ƙarshen wani daji wanda daga nan baifi tafiyar wuni bace tsakaninsu da garin na Maikironomada ba.
To amma sai dai kamar yadda aka bata da cikakkiyar masaniya akan hatsarin amfani da wannan fasaha.
Saboda haka suna dira kanta ya fara juyawa, inda kafin kace meye wannan ta faɗi ƙasa sumammiya.
Shi kuwa Armad yana tsaye ido a rufe, har a wannan lokaci baisan meke faruwa.
Abinda kuwa yasa ta suma shi ne, shi wannan Ayrid, fasahar sa tana zuƙe Negrinkin jikin mai amfani da ita ne. A saboda hakane bayan Negrinkin jikin nata yaje ƙarshe ta yadda ana ci gaba da zuƙa, to sai dai ta kuma ta mutu.
Sai wannan fasaha ta tsaya cak, wanda kuma hakan ne ma yasa basu isa cikin garin na Maikironomada ba, hasalima a dokar daji ya watsar dasu.
***
Acan wannan ƙauye kuwa tuni mai garin, ya tara dukka ƴan majalisarsa kuma suka yanke shawarar cewa bazasu bari wannan yaro da suka samu ya tafi a banza ba.
Saboda haka suka samo ma'abota zane, waɗannan suka zana siffar Armad komai da komai, sannan kuma da bayanansa.
Cikin kwanaki uku suka tashi ƴan aike inda suka aikesu wasu garuruwa dake bawa wannan ƙauye tsaro, da wannan zanuka, da niyyar inganta dangantakarsu da kuma siyarwa da duk wani maɓuƙaci wannan hoto na Armad.
***
A kwana na biyar bayan wannan keken doki ya watsar dasu acikin dokar daji, Nusi ta farka, ta kuma tararda da kanta acikin tanti, Armad kuma a gefenta ya rufe ta kayayyaki, sannan kuma ya haɗa wasu yayi mata matashin-kai dashi.
Bayan farkawar ta ya kawo mata abinci taci tasha, sannan kuma ta samu nutsuwa.
Kallo ɗaya kacal tayiwa Armad ya gane cewa ranta a ɓace yake a game dashi, kuma dama a kwana biyar ɗin da suka wuce tun bayan sanda hankalinsa ya dawo jikinsa, ya tabbatar da cewa lallai wani babban abu ya faru wanda yasa bai gansu acikin wannan ƙauye ba, amma kuma gasu a tsakiyar daji.
Saboda abu na ƙarshe da yake iya tunowa shi ne wannan ƙauye da kuma wannan takarda dake ɗauke da sunan Tirifil-fakta.
Saboda hakan nema ya riga ya yanke shawarar cewa lokaci yayi daya kamata ya amince da wani a doron wannan ƙasa da bai san kowa ba.
Kuma yasan cewa indai har yana da buƙatar ya amince da wani to Nusi ita tafi dacewa.
Kuma babu aminta idan akwai ƙarya! Saboda haka ya yanke shawarar gaya mata sunansa na gaskiya a duk sanda ta farka.
Tana kuwa yi masa wannan kallo ya ce, ''ehmmmm... yaya, suna na er... Armad Wilbafos!''
Fuskarsa cike da murmushin ban haƙuri ya kwashe dukkanin abubuwan da suka shafi Miyurarsa da kuma sunansa da ma yadda sukayi da antinsa Jushaya ya gaya mata.
Bayan ya gama gaya mata, sai tayi shiru kawai tsahon lokaci.
Kai har saida tunane-tunane suka fara yawo acikin zuciyar Armad akan ko mai yasa tayi shiru bata ce komai ba.
Amma bayan kimanin rabin rabin sa'a, saita ɗago kai, fuskarta babu alamun fushi ko kaɗan kuma ta dubi Armad gami dayin kyaran murya sannan ta fara kawabi, ''To amma yanzu meye abinyi.
"Domin a halin yanzu, bawai neman Tirifil-fakta bane mafi muhimmanci a gabanka ba, a'a, kare kanka shi ne mafi muhimanci!
"Domin kuwa kaima yanzu kaine abin neman! Domin zan iya ce maka yadda duniya take nemansa, kaima haka za'a fara farautarka, banbancin kaɗan ne!!!"
Comments
Post a Comment