Skip to main content

Babi na sha tara

MAGAJIN WILBAFOS Na A M Ibrahim

Babi na sha Tara : Sa hannun Sarki Dul'Ururu

Saboda saurin da Nusi ta taso dashi, duk dan ta riƙo Armad cikin ƙoƙarinta na ta hanashi sanya ƙafa acikin wannan waje,  tana ganin ya riga ya faɗa sai taci birki da ƙarfin tsiya domin kada ita ma ta faɗa ayi biyu babu.

Amma ina, dama a lokacin bai wuce sauran kamu uku ba tsakaninsu da Armad ba, saboda haka duk da cijewar da tayi saida ta ita ma ta afka.

Duk da cewar ba dukkan jikinta bane ya faɗa ba, amma ƙafarta ta dama tuni ta shiga wajen.

Nan take ta rufe ido cikin takaici, babu abunda take tambayar kanta face, ''mai yasa...mai yasa... duk akan wannan yaro da bai ma san banbancin fari da baƙi ba, nake neman halaka kaina....''

Wannan shi ne tunaninda yake ta juyawa a ranta, a lokacin da ta gano cewa ta rasa komai data daɗe tana tanadi, duk acikin ƙanƙanin lokaci, sannan kuma ga rayuwarta nan ma tana kusantar halaka.

Amma wani abun mamaki ga ita kanta shi ne, gashi dai lallai ya kamata tayi baƙin ciki gameda yadda abubuwa suka juya mata, kuma babu wanda ya kamata ta zarga face Armad, amma ko kaɗan bata jin dana sani acikin zuciyarta.

Hasalima ji take tamkar tayi wani babban abu mai matuƙar muhimmanci a gareta, tamkar sauke wajibi daga cikin wajibai.

Saboda irin wannan tunani da take, kawai saita rufe idanunta cikin ɗimuwa a wani yanayi na bankwana da duniya.

Ƙafarta tata tana shiga cikin wata iska mai tsananin ƙarfin gaske ta finciko dukkan jikinta daga inda yake izuwa cikin wannan waje.

Nan take ta buɗe ido, sanda taji  ta a sama tana lilo tana nufar ƙasa, ƙiris ta faɗo.

Abu ne sananne cewa acikin waje da suke kira da Hijabi, tsananin hawa-hawa ne, kuma yana mafi ƙarfi akan ƙasar wajen.

Saboda haka ta fara ƙoƙarin yin wata dabarar, domin kada ta taɓa ƙasa, amma ina kafin tayi wani abu tuni baifi saura kamu biyu ba a tsakaninsu da ƙasa ba.

Idanunta a rufe tana jira ta fuskanci irin wannan uƙuba data riga ta sani aduk lokacinda tayi arba da wannan guri, kwatsam kawai sai jitayi komai ya tsaya tsak aduniya babu abinda ke  motsi.

Kai a yadda taji ma, hatta zuciyarta saida ta tsaya da bugawa na taƙi ɗaya kafin ta ci gaba.

Nan take ta buɗe ido gami da duba izuwa muhallinta domin ganin mai yake faruwa.

Nan kuwa idanunta sukai arba da Armad wanda ke riƙe da ita akan iska.

Bata san lokacinda tsananin mamaki ya kamata ba, a sanda ta juya ta kuma tabbatar da cewa ƙafafun Armad ɗin a tsaye suke cak akan wannan waje babu kuma ko alamun girgiza a tattare dashi.

Kai hasalima babu wani alamun yana kan wani waje na musamman ko kuma mai sharri.

Armad yayi murmushi mai ɗan ɗauke da yarinta ta dai-dai shekarunsa, inda baice komai ba, bai kuma tsaya ba, nan take ya ci gaba da tafiyarsa a wannan waje.

Duk inda Armad ya taka saiya ƙara yin tsananin ja sosai, tayadda har sai kore-koren dake gauraye da launin jan ya ɓace ɓat, amma hakan ko kaɗan baya ko alamun cutar dashi, hasalima tamkar sauri yake ƙara masa.

Tuni mamakin daya haɗiye Núsí ya rikiɗe ya koma firgici, inda idanunta suka fara karkarwa saboda firgici.

Ba komai bane ya jawo haka ba illa abinda take tunani acikin ranta, ''mai ke faruwa, hatta sinadarin Negrinkin cikin wannan waje ma baya masa komai, maimakon su rinƙa tureshi, shi kuma yana ƙoƙari akan su karɓeshi, amma wannnan yaro tamkar nemansa suke, tamkar sune suke buƙatarsa bashi bane yake buƙatarsu ba....

"Wai haƙiƙanin wane ne wannan yaro, kuma maike faruwa...kuma dai na tabbatar ba mafarki nake ba!!!''

To abinda bata sani ba shi ne Armad yana shiga wajen, yaji wannan mutun-mutumi da suka haɗa ido dashi a baya ya ƙara motsawa, inda wani abu ya faru cikin tsananin sauri, wanda lallai da Armad ɗin ya ƙifta ido sau ɗaya kacal to da lallai bazai gani ba.

Abinda kuwa ya faru shi ne; Armad na sanya ƙafa cikin wannan guri yaji tamkar ya faɗa cikin garwashi.

Tsananin raɗaɗi ya gauraye jikinsa, tayadda kafin yayi wani abu tuni ƙafafunsa sun kasa ɗaukarsa kuma sun fara neman durƙushewa.

To amma a wannan lokaci ne wannan mutun-mutumi ya motsa cikin tsananin sauri tayadda inka ƙifta ido sai ɗaya kaɗai bazaka lura da faruwar abin ba.

Amma wannan motsawa da yayi ita ce tasa iskar dake kewaye dashi ta motsa, inda wata ƴar ƙaramar guguwa ta kaɗa inda kafin kace meye wannan tuni ta gauraye wajen.

Armad bazai taɓa iya bayanin maiya faru ba, ko kuma taya ya abinda ya faru ya faru ba, amma zai iya rantsewa cewa acikin wannan iska data giftashi wadda ta fita daga jikin wannan mutun-mutumi, akwai wani 'umarni', irin umarnin da babu wata halitta mai rai ko mara rai data isa ta saɓashi.

Armad baisan haƙiƙanin meke cikin wannan umarni ba, amma lallai zai iya rantsewa cewa an bada wannan umarni.

Wanda kuma faruwar hakan keda wuya yaji duk abinda yake ji a jikinsa ya kau, babu ko alamun ciwo ko zafi.

Kuma hakan na gama faruwa hankalinsa ya dawo jikinsa inda yaga Núsí tana ƙoƙarin faɗuwa, shi kuma yayi sauri wajan tallafo ta.

Su na tafiya tana riƙe a hannun nasa, inda shi kuma yake nufar ɗaya ɓangaren domin fita daga wajen.

Kuma koda yaga irin yanayi na mamaki da firgici data shiga, sai kawai ya fara mata bayanin dukkanin abinda ya faru, daga sanda ya taka ƙafarsa har ya zuwa wannan lokacin.

To dama dukkanin wajan da zasu wuce ɗin wanda ake kira da Hijabin, baifi taku ashirin ba, saboda haka a dai-dai kusan lokacin da suke niyyar ficewa ya hattama zayyana mata abinda ya faru.

Haka dai suka ƙarasa takunsu na ashirin da ɗaya wanda ya ƙarasa fitar dasu daga wannan waje gaba ɗaya.

Inda ya ajiye ta gami da kyara musu waje dominsu zauna.

Ƙasar dake bayan wannan waje tana da banbanci da wadda suka baro; tayadda duk inda ka duba zaka ga alamun rayuwa.

Kamarsu tsirrrai da namun daji, kuma gaba kaɗan garesu daji ne katafare.

Núsí ta ɓoye mamakin ta kuma ta haɗiye tambayoyinta game da Armad, domin a ɗan iya lokacinda suka yi dashi da kuma abubuwan daya gaya mata, ta fahimci cewa lallai akwai abubuwa na ban al'ajabi a tattare da wannan yaro.

Kuma babban abin mamakin shi ne, shi kansa ga dukkan alamu bashi da masaniya akan wannan abubuwa.

Saboda haka taji a ranta bata san ta matsa masa da tambaya.

Amma wani abu guda ɗaya wanda dole ne shi da ita su warware shi ne, a wanne matsayi suke a yanzu.

Nanfa ta buɗe baki, fuskarta cike da murmushi mai alamun godiya tace, ''nagode Armad, daka wutar dani wannan jarabawa, domin kuwa ban taɓa tsammanin wucewa da wuri haka ba.

''Amma wani hanzari ba gudu ba, naji labarinka kuma naji aniyarka ta neman Tarifil-fakta.

''Sannan kuma na gaya maka kaɗan daga cikin irin hatsarinda wannan aniya taka ke ciki. Amma daga alamun daka nuna min naga baka da niyyar canja ra'ayi.

''To amma naga lallai bakai kama da wawa ba, saboda haka nasan daga ɗan abinda na gaya maka da kuma wanda ka sani, ya isheka ka gane cewa a yadda kake ɗinnan  babu abinda zaka iya. A taƙaice dai ina ganin baka da ƘARFIN DA ZAKA IYA NEMO SHI A YANZU!''

Data zo nan a zancenta, sai ta ɗan tsaya, saboda ganin da tayi ya ɗago kai yana kallonta.

Duk da ba tayi mamaki ba sosai, kuma bata daɗe ba ta ci gaba da bayani ba, amma abinda bata sani ba shi ne, dalilin da yasa ya ɗago kai shi ne, ta taɓa dai-dai inda yake masa ƙaiƙayi.

''Kamar yadda kaji a labari na ina daga cikin manyan ɗalibai a mazhabar Maikironomada, saboda haka idan kana so zan iya zuwa dakai na samar maka wajen fara horo!''

To daya ke faɗuwa ce tazo dai-dai da zama, Armad bai tsaya ɓata lokaci ba ya amince ɗa wannan shawara.

Inda suka zauna a wannan waje tsahon kwanaki biyu suna hutawa.

Suka kafa ɗan ƙaramin tanti, inda suka zauna aciki.

Duk da cewa bata kulashi sosai, amma hakan baisa ya rage bata labarai ba wanda mafiya yawansu na doron ƙasa ta uku ne, da kuma yi mata tambayoyi akan yaya ƙasar Maikironomada take, kuma yaya irin horonsu yake.

A rana ta uku suka ɗaura siddi akan wata alfadara da suka kama a ranar farko, kuma suka nufi gabas ta cikin wannnan daji dake gabansu.

Duk da cewa sun ɗauki sama da sati ɗaya suna tafiya acikin wannan daji, amma babu wani abu muhimmi daya faru a yayin tafiyarsu.

A kwana na tara suka iso wani ɗan ƙauye mai yawan bukkoki.

Duk da akwai ƙofar gari amma babu wani caje da ake kafin shiga wannan ƙauye, kuma babu wata doka ta musamman.

Saboda haka basu sha wata wahala ba suka shiga kuma kai tsaye Núsí ta jasu wani ɗan waje da aka gina da rumbu.

Daga saman ƙofar shigar an rubuta, 'wajan shan furar matafiya'.

Har sun kusa zuwa sai ta buɗe baki ta ce, ''shekaru uku da suka wuce kafin na fara wannan jarabawa, anan nasha fura da zan wuce.

''Musha fura anan, kafin mu nemi wajan kwana a wannan gari saboda.......''

Dai-dai sanda tazo nan a zancenta tana gabda shiga ƙofar wannan waje, amma saita tsaya cak ta kuma yi sauri ta juya.

Ba komai bane ya jawo haka ba face Armad wanda ya tsaya cak, fuskarsa a kafe akan bangon wannan wuri na ɓangaren kudu.

Kana ganinsa kasan acikin firgici yake, jikinsa kaf karkarwa yake amma kuma wani babban abin mamaki shi ne idanunsa a rufe suke ruf.

Kuma ƙarara ƙoƙari yake tayi ya buɗe su harda hannayensa biyu amma ya kasa.

Bata tsaya ɓata lokaci ba ko kaɗan, ta juyo ta kuma nufoshi da sauri, sannan kuma a lokaci guda, idanunta suka bi dai-dai fuskar ta Armad take kafe a jikin bangon.

Ba komai ta gani ba, illa takardar da kusan kowa a wannan doron ƙasa ta huɗu ya sani.

Wadda kuwa ita ce takardar da Sarki Dul'Ururu ya saka hannu akai.

Wadda ita ce ke ƙunshe da Kyaututtukan da za'a bawa duk wanda ya kawo ko kuma ya bada wani bayani daya taimaka aka kama Tarifil-Fakta.

Sannan kuma da wasu hanyoyi da za'a iya ganeshi.

Sai kuma sa hannun sarki bisa doron ƙasa ta biyu, wato Dul'Ururu, wanda ke jaddada ingancin wannan takarda!

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...