Armad ne da Kiru a tsaye su na fuskantar juna, kowa da tasa takobin a zare! Tun dai ƴan mintuna da suka gabata, Hasanu wanda shi ne babban wannan tawaga ya kwance Armad ya kuma bashi takobinsa. Abinda kawai ya rage shi ne Kiru ya nunawa Hasanu da wannan budurwa, wadda ta kasance ƙanwarsa, irin sabuwar fasaha, da ya koyo. Fuskar Armad bata canja ba ko kaɗan, tamkar babu abinda ke faruwa, yana riƙe da ƙotar takobinsa. A wannan lokaci ne Kiru yayo kan Armad, yana zuwa ya ɗaga takobinsa ya kawo masa wani wawan sara. Wata ƙara mai kashe kunne ta tashi sama yayinda waɗannan takubba nasu suka haɗu a sama, lamarinda yasa dukkan tsuntsaye da sauran dabbobi dake kewayen fara guje-guje. Kan kace meye wata iska ta tashi daga kewayen su, inda ta bazu ko'ina, har saida ta kaɗa bangon ruwan dake arewa, wanda bashi da nisa da inda ake fafatawar. Kiru ya kalli takobin Armad idanunsa cike da mamaki, wanda a wannan lokaci fuskarsa taɗan canja, kana gani kasan haɗa takobin da sukai yasa ya...