Ganin haka, Binani da matar mai kama da Rabi suka bisu da gudu. Idan ka lura zaka ga filin yaƙin ya sauya salo. A ɓangare guda Nusi tana ɗauke da Armad da Fatima tana gudu. A ɗaya ɓangaren kuma Nazára ya ɗakko Rabi, Binani da Rabi-mutun-mutumi suna binsa. A wani wajen kuma Zaikid yana ƙoƙarin tare Dul'Ururu, jan doki da Najunanu suna ƙoƙarin tare Diwani. Maruta kuma yana can gefe yana kula da rundunar Ururu da kuma faɗan Ƙaraiƙisu da Maikiro'Abbas. "Armad," inji Nusi. "Ka amsa min mana. Kana ji na? Armad?" Shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Kawai jini ne yake zuba daga bakinsa. "Ya suma," inji Fatima, cikin alhinin. "Bazan iya amfani da izza ba saboda da wannan ƙarfen." Ta nuna ankwar dake jikinta. "Amma farfesa Zaikid zai iya bashi izza ya farfaɗo dashi." Nusi najin haka ta waiwaya ta hangi Zaikid tsaye a gaban Dul'Ururu. Ko kokwanto bata yi Dul'Ururu yafi ƙarfinsa. "Giwa, Cokali, Sarkin Bai, Barilu, Inyaya,...