Skip to main content

Posts

Featured post

Gidan Sharhi

Sharhin mu na satin farko  
Recent posts

461

Rai a ɓace, Dul'Ururu ya saka hannu biyu akan sandarsa ya ture takobin Zaikid data jan doki gefe. Sannan da sauri ya juyo ya take zakunan dake riƙe da ƙafarsa ya kuma kawowa Cokali sura. Abin mamaki kafin hannunsa ya ƙaraso sai Cokali ya ɓace ɓat. Sarkin ya juyo kan sarkin Bai da Inyaya, amma kafin ya ƙaraso duk sun ɓace. Ya ƙara juyawa kan Barilu, amma kafin yayi wani abu shima ya ɓace. "Hmm.. wannan sihirin da kuka zo dashi bazai yi aiki ba," Inji Dul'Ururu. To a yayinda Dul'Ururu yake fama dasu Zaikid, acan gefe kuma Maikiro'Abbas ne suke kai-komo da Ƙaraiƙisu. "Haha... Maikiro'Abbas, Maikiro'Abbas," Inji Ƙaraiƙisu. "Kada ka bani kunya mana. Na saka rai zan samu jarumi barde wanda zan kara dashi amma har yanzu banga komai ba." Ya ƙara kawowa Maikiro'Abbas duka da ƙafa. Maikiro'Abbas bai motsa ba har ƙafar basamuden tazo ta same shi. Zaka yi tunanin saboda girman ƙafar zata yi cilli da Maikiro'Abbas, amma sarkin

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B

459

 Ganin haka, Binani da matar mai kama da Rabi suka bisu da gudu.  Idan ka lura zaka ga filin yaƙin ya sauya salo. A ɓangare guda Nusi tana ɗauke da Armad da Fatima tana gudu. A ɗaya ɓangaren kuma Nazára ya ɗakko Rabi, Binani da Rabi-mutun-mutumi suna binsa.  A wani wajen kuma Zaikid yana ƙoƙarin tare Dul'Ururu, jan doki da Najunanu suna ƙoƙarin tare Diwani. Maruta kuma yana can gefe yana kula da rundunar Ururu da kuma faɗan Ƙaraiƙisu da Maikiro'Abbas. "Armad," inji Nusi. "Ka amsa min mana. Kana ji na? Armad?" Shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Kawai jini ne yake zuba daga bakinsa.  "Ya suma," inji Fatima, cikin alhinin. "Bazan iya amfani da izza ba saboda da wannan ƙarfen." Ta nuna ankwar dake jikinta. "Amma farfesa Zaikid zai iya bashi izza ya farfaɗo dashi." Nusi najin haka ta waiwaya ta hangi Zaikid tsaye a gaban Dul'Ururu. Ko kokwanto bata yi Dul'Ururu yafi ƙarfinsa.  "Giwa, Cokali, Sarkin Bai, Barilu, Inyaya,

458

  "Mayaƙan Ururu!" Maruta ya daka musu tsawa ganin suna jada baya. "Mai kuke yi haka? Ku kashe shi? Mutum ɗaya ne fa, tsoho tukuf? Tsoron mai kuke ji?" Jin haka mayaƙan suka ƙara azama suka danno kan Maikiro'Abbas. Ganin haka Maikiro'Abbas yayi dariya. Yana tsaye ya jira suka ƙaraso sannan ya kaɗa sandarsa yayi kansu. Da farko mayaƙan sunyi baya, amma da suka ga babu alamun hari a tare dashi sai suka zagaye shi, su kuwa mayaƙan Maikironomada juya sukai da gudu baya. Sun riga sun san halin uban gidansu.  Wani daga cikin mayaƙan Ururu ya samu ya ƙarasa kusa ya sari Maikiro'Abbas a idon sahu, jini yayi sama.  "Dama yana zubda jini?" "Aka ce jininsa na ƙanƙara ne?" "Haha... Indai yana jini kuwa ai za'a iya kashe shi." Inji mayaƙan. Ganin haka suka ƙara azama wajen kai masa sara, harbi, da suka. Sai da yaje tsakiyarsu sannan ya tsaya. A hankali ya ɗaga ƙafa ya daki ƙasa ya kira ɗalasimi. "Jinin ƙanƙara!" Da farko ba

456

Aiban'zhisu Babban karni!  ************* Tunda Armad ya riga yazo nan to fa bazai koma ba sai ya ɗauki mahaifiyarsa.  "Aiban'Zhisu, babban ƙarni!" Ɗalasimin yana barin bakinsa, jikinsa ya ɗau hasken walkiya. Tun daga kai har ƙafa babu inda baya tartsatsin walkiya. A lokaci guda walkiyar ta fara juyawa tana zagaya jikinsa tana yin sama. A ɗan ƙanƙanin lokaci ta dunkule tayi sama ta fasa ta cikin gajimare ta fice ta ƙara lulukawa sama. Ta wuce Hajarul Ururu ta shiga doron ƙasa na farko tayi sama ta haɗe da gajimare. A lokaci guda da walkiyar take yin sama, wata walkiyar ce ta fita daga jikin Armad tayi ƙasa ta fasa doron ƙasa ta uku data huɗu data biyar data shida data bakwai ta shige ƙarƙashin ƙasa. Sannan kafin wani yayi wani abu sai walkiyar ta fashe zuwa ƙawanyar walkiya dubu a sama doron ƙasa ta farko, sannan wata ƙawanyar dubu a ƙasa doron ƙasa ta bakwai. Kowacce ƙawanya acikin dubun ta rabe zuwa ƙawanya ba adadi suka fantsama suka shiga duniya. Cikin rabin dakika

451-455

 Can bayan wani lokaci Rabi ta ƙara ji ya kira sunanta. Ta buɗe baki zatai magana amma tayi shiru ganin cewa babu wanda yaji sai ita.  "Tar...ko... ne..." Inji Anbalu. Har yanzu Rabi ita kadai take jin mai yake cewa. Ya ƙara maimaitawa. "Tarko ne." Rabi ta tsaya cak ta kalli Fulafunu. "Wai kana nufin duk baka jin abinda yake cewa?"  Fulafunu yayi jim yana kallonta cikin mamaki.  "Ni banji komai ba," ya ce.  Rabi ta ɓata rai. Tabbas akwai wani abu dake faruwa a wajen. Mai ya kamata tayi? "Zarru? Kai ma baka ji ba?" Hadimin ya girgiza kai.  "Banji ba."  To ko mafarki take yi? Amma kuma tabbas taji murya a kunnenta. Anbalu yace mata 'tarko ne', to amma wane irin tarko? Mai yake nufi? Wa aka sawa tarkon acikinsu? "Mu koma," inji Rabi. "Mu koma wajen su Shema'u." Fulafunu ya ɓata rai. Tabbas akwai abinda yake damun Rabi. A ɗazu ta dage sai an kai Anbalu gida amma kuma ace har ta canja shawara, mai ya

446-450

 Can sai kaga kunne a ƙanƙare, can kaga yatsa, can kaga ido, gaba ɗayan Iluru yayi daga-daga ya zama babu. Ko binne shi iyalinsa baza su samu damar yi ba.  "I...I....Iluru ya mutu," wani sadauki ya faɗa cikin kinkina. Kana gani kasan sun kasa fahimtar abinda ke faruwa. Musamman duba ga cewa Iluru fa sarkin jinzidal ne guda. Ace duka ɗaya an gama dashi. Kuma fa muƙamin su ɗaya da Maikiro'Abbas.  "Maikiro!" "Maikiro!!" "Maikiro!!!" Mayaƙa suka hau murna da ihu.  A nasa ɓangaren Maikiro'Abbas bai koma wajen daya baro ba. Tsayawa yayi anan yana kallon Dul'Ururu da mayaƙan Ururu kamar yana ce musu idan sun isa su taho. Ga dukkan alamu sarkin ya fara gajiya da jira. A dai-dai lokacin da Iluru ya zama ƙanƙara ya tarwatse a lokacin faɗa ya ƙara tsamari a ɓangaren Ururu. Ganin abinda Maikiro'Abbas yayi wa Iluru yasa Dul'Ururu ya taka a fusace wajen da Armad yake kwance da niyar ɗaukar fansa.  Armad yaji tahowar sa. Jikinsa ya ɗan fara