Sharhin mu na satin farko
Rai a ɓace, Dul'Ururu ya saka hannu biyu akan sandarsa ya ture takobin Zaikid data jan doki gefe. Sannan da sauri ya juyo ya take zakunan dake riƙe da ƙafarsa ya kuma kawowa Cokali sura. Abin mamaki kafin hannunsa ya ƙaraso sai Cokali ya ɓace ɓat. Sarkin ya juyo kan sarkin Bai da Inyaya, amma kafin ya ƙaraso duk sun ɓace. Ya ƙara juyawa kan Barilu, amma kafin yayi wani abu shima ya ɓace. "Hmm.. wannan sihirin da kuka zo dashi bazai yi aiki ba," Inji Dul'Ururu. To a yayinda Dul'Ururu yake fama dasu Zaikid, acan gefe kuma Maikiro'Abbas ne suke kai-komo da Ƙaraiƙisu. "Haha... Maikiro'Abbas, Maikiro'Abbas," Inji Ƙaraiƙisu. "Kada ka bani kunya mana. Na saka rai zan samu jarumi barde wanda zan kara dashi amma har yanzu banga komai ba." Ya ƙara kawowa Maikiro'Abbas duka da ƙafa. Maikiro'Abbas bai motsa ba har ƙafar basamuden tazo ta same shi. Zaka yi tunanin saboda girman ƙafar zata yi cilli da Maikiro'Abbas, amma sarkin