Shísu yayi shiru yana tunani. Bai taɓa gwada fasaharsa a irin wannan yanayi ba, amma kuma abu ne mai yiwuwa. Tunda yana iya amfani da tunaninsa ya motsa ƙarfe ai kuwa zai iya ƙara masa gudu ko kuma ya rage. Kamar yadda yake ture masu da kibbau idan an harbo masa. Sai dai kuma yana jin tsoro kada yace zai iya kuma sai lokaci yazo ya kasa. Hakan zai iya sanadiyar mutuwar Asifu dama sauran wanda suke tare dasu. Shin mai zai cewa Nusi-ya idan hakan ta faru? "Ban taɓa... yin hakan ba, amma ina ganin watakila..." Nusi ta ɗora hannu a kafaɗarsa lamarinda yasa ya daina kinkina. "Zaka iya," inji Nusi. "Ni nasan zaka iya." Shísu ya risuna cikin girmamawa. Tabbas tunda Nusi-ya tace zai iya to kuwa zai iya. Bazai bata kunya ba komai rintsi komai wuya. "Zan iya," inji Shísu. "Amma yaya zaku yi da ƙusar mairakana?" Inji Armad. A ganinsa babban abinda yake ƙarawa denizawa ƙarfi shi ne fasahar mairakana. Koda Asifu zai iya yanka jikin Iluru bazai s...