Amma ina, bashi da izza ko ɗigo a jikinsa, ko walkiya ɗaya bai gani ba. "Armad!" Fatima ta kwala masa kira tana ƙoƙarin ture shi gefe. Kafin ya fahimci mai take ƙoƙarin gaya masa yaji izzar Dul'Ururu a bayansa. Da sauri ya dawo da mahaifiyarsa ƙasa ya rufe ta da jikinsa. Sandar Dul'Ururu ta sauka a bayansa. Wata wuta mai haɗe da narkakken dutse tayi sama tana tartsatsi. "Armad!" Nusi ta kwalla ƙara tare da tafiya da gudu wajen Armad. Zaikid wanda ke kusa da ita yayi maza ya riƙe ta. "Idan kika shiga faɗan can mutuwa zaki yi," inji Zaikid. A banza, duk da abinda Zaikid ya faɗa Nusi bata ji ba, kawai ƙoƙarin ƙwacewa take yi domin ta tafi wajen Armad ta ceto shi. A ɗaya ɓangaren ita ma Fatima hawaye kawai take yi tana ƙoƙarin ture Armad gefe domin harin ya sauka a kanta. Amma Armad ya dake yaƙi matsawa ko'ina. Dul'Ururu ya ƙara loda masa sandar tsafinsa. Jini ya fara malala daga hanci da bakin Armad yana zuba akan Fatima. Gashi babu izz...

Pls aduba mu kwana biyu ba post. Bayan haka ina mika aakon gaisuwa ta ga Dr yya ibada
ReplyDeleteDr mai wilbafos Allah ya ƙara nisan kwana
ReplyDelete